Nawa kuke ganin Katsina utd. ta sayi Gambo Muhd?

Labarin komawar dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars, Gambo Muhammad zuwa kungiyar kwallon kafa ta Katsina United ya rigaya ya zama abin tattaunawa a wajen matasa dake da shaawar tattauna batutuwa da suka shafi kwallon baka, koda yake ba’a bayyana ko akan nawa kungiyar ta sayi Gambo ba.

Gambo, Wanda ya lashe gasar cin kofin firimiya ta Nigeria sau hudu da Pillars ya koma kungiyar ne daga Buffalo F/C a shekara ta 2006.

A shekara ta 2013 Dan wasan yayi kokarin komawa kungiyar kwallon kafa ta Club African dake kasar Tunisia sai dai daga baya cinikin ya rushe saboda wasu dalilai.

Shekaru biyu da suka gabata ma dai Gambo yaso barin Kano Pillars, Wanda ake kira sai masu gida zuwa kungiyar Plateau United nan ma cinikin ya rushe.

Gambo ya zura kwallaye sama da 70 a Kano Pillars kuma ya buga wasansa na karshe a kungiyar a wasan da Pillars ta doke kungiyar Ashate Kotoko anan Kano a gasar cin kofin zakarun nahiyar Africa wasan daya zura kwallo daya acikin kwallaye ukun da kungiyar ta jefa a raga.

Leave a Reply

en_USEnglish
en_USEnglish