An ceto rayuwar jamiin kwana kwana da yayi arba da Maikilago

Hukumar kashe gobara ta jihar kano ta ce jami’in nan nata da ake zargin yayi arba da aljanin cikin ruwa yana samun sauki

Da yammacin Alhamis din data gabata ne jami’an hukumar suka garzaya wani kauye mai suna Kayi a yankin karamar hukumar Kumbotson jihar Kano, domin ceto rayuwar wani matashi da ruwa ya tafi dashi lokacin daya je domin wanka.

Sai dai daga bisani kallo ya koma sama, lokacin da jami’in hukumar ta kwana kwana ya rafka ihun neman ceto daga abokan aiki.

Nan take kuwa sauran abokan aikin sa dake jiran karbar gawar matashin idan an dauko suka fara tsinduma cikin ruwan domin kwato abokan aikin su, matashi da ya sanya mutanen gari ihun “yayi arba da mai kilago”

Kakakin hukumar ta kashe gobara a jihr kano ya shaidawa wakilin mu Ibrahim Abdullahi soron Dinki cewar tuni abon nasu ya fara samun sauki a wqni asibiti dake yankin birni, wanda ana sa ran sallamar sa da zarar ya watstsake

Shi dai aljani mai Kilago yayi kaurin suna a shekaru sama da 30 da suka shude musamman a kasar Kano, inda da zarar ruwa yaci mutum akan dorawa mai kilago laifi.

Leave a Reply

en_USEnglish
en_USEnglish