KAROTA ta jinjinawa kanawa.

Jama’ar gari fiye da dari biyu (200) ne suka taimaka wa jami’an hukumar KAROTA cafke wani direba.

Jamian hukumar da ke aiki akan zuwa Zaria daf da gadar Lado sun fuskanci cin zarafin aiki ne daga wani direban babbar motar daukar Fasinja wadda aka fi sani da Luxurious, bayan ya karya dokar hukumar ya yi wa jami’an ta barazana.

Shaidun gani da ido sun labartawa Abba Isa Mohd cewar wannan al’amari aya fusata al’ummar gari, inda suka yi wa direban kofar rago har aka kama shi.

Wadansu da wakilin namu a tattauna dasu sun roki a hukunta wannan direba saboda rashin da’ar da ya nuna, wanda ba safai ake ganin hakan a sauran sassan kasa ba.

Daga bisani ne shugaban hukumar KAROTA Dakta Baffa Babba Dan’agundi yace lallai au’ummar gari sun nuna cewar zasu goyi bayan ayyukan da hukumar keyi na tsaftace sufuri.

Baffa Babba ya nuna jin dadinsa dangane da rawar da al ummmar ta taka waje kin goyon bayan aikita laifuka, a sabo da hak zasu jajirce akkan aikin su, daga nan ya ja hankalinsu matuka inji da su kasance masu bin doka da oda.

Ayyukan hukumar dai a kwanakin nan na daukar sabon yanayi, inda hatta masu sanye da kayan sarki ke fuskantar turjiya daga jami’an matukar basu girmama dokar tuki ba.

Leave a Reply

en_USEnglish
en_USEnglish