Rundunar yan sanda na neman tallafin dusa

Biyo bayan wani kame data aiwatar akan barayin shanu, rundunar yan sandan jihar kano tace ya zuwa yanzu ta samu nasarar kwato sama da dubu guda.

Kakakin hukumar anan kano DSP. Abdullahi Haruna Kiyawa ya shaidawa wakilan Baba Suda cewar sun samu nasarar kwato shanun daga wadanda ake zargin barayin shanu.

Abdullahi Kiyawa yace idan da akwai mtsaalr da suke fuskanta a wanna lokaci bata wuce na karancin abincin dabbobi ba, a saboda haka suka sanya kokon bara daga al’ummar gari.

Lawan Mihd da Suleman Abdullahi dai matasa ne da ake zargi, wanda an kama su da bindigogi kirar AK47 biyu.

Yanzu haka dai rundunar tace ta mika koken ta ga gwamnatin kano, tunda ciyar da dabbobi masu yawa haka yafi karfin ta.

Leave a Reply

en_USEnglish
en_USEnglish