Connect with us

Labarai

Dalilan da suka sanya ShopRite ke son ficewa daga Najeriya

Published

on

Shararren kamfanin nan na Shoprite mallakin kasar Afirka ta kudu ya dakatar da ayyukansa a Najeriya

Kamfanin ya sanar da cewa ya fara gudanar da wani tsari da zai bashi damar dakatar da dukkanin ayyukansa a kasar.

Kamfanin Shoprite Holdings Limited ya ba da sanarwar a ranar Litinin a cikin rahoton hadar-hadarsa na shekara wanda ya kare a ranar 28 ga Yunin, 2020.

Kamfanin, wadanda ya sanar da samun karin kashi 6.4 cikin dari na ribar da ya samu duk da kalubalen da annobar Covid-19 ta haifar, ya ce ya dauki matakan dakatar da ayyukansa a Najeriya. “Sakamakon bukatar hakan daga masu zuba jari daban-daban, hakan ta sanya muka bullo da wannan matakin a Najeriya.”

“Hukumar gudanarwar kamfanin ta yanke shawarar fara sayar da dukkanin hannayen jari, ko kuma mafi yawa daga cikinsa, ga ‘yan kasuwa.

Duk da cewa kamfanin na iya samun karin wani kaso na musamman na hada-hadarsa, sai dai abun ba haka yake ba  a kasar Afirka ta Kudu.

A cewar rahoton, hadar-hadar tsagin kamfanin da ke wajen kasar Afirka ta Kudu amma ciki banda Najeriya sun samar da kashi 11.6 cikin dari na ribarsa, ko da yake an samu faduwar riba da kaso 1.4.

Shoprite ya danganta wannan koma baya da dokar kullen da aka samu a wasu kasashen Afirka da dama sakamakon barkewar annobar Coronavirus.

 

Labarai

NAHCON ta sanya ranar fara jigilar maniyyata aikin hajjin bana zuwa Saudiyya

Published

on

Yanzu haka hukumar Aikin Hajji ta ƙasa NAHCON, ta 15 ga watan nan na Mayun 2024, a matsayin ranar da za’a fara jigilar maniyyata aikin hajjin bana, zuwa ƙasa mai tsarki.

Bayanin hakan ya fito ne ta bakin shugaban hukumar ta NAHCON, Jalal Ahmad Arabi, a wajen taron masu ruwa da tsaki kan aikin Hajji da Umrah, da ya gudana yau Alhamis birnin tarayya Abuja.

“Maniyyata kimanin 65,500 ne za su sauke Farali daga ƙasar nan a ƙasa mai tsarki; za su shafe aƙalla kwanaki huɗu domin yin ziyara a Madina kafin fara aikin Hajji, “in ji Arabi”.

Daga bisani shugaban hukumar aikin hajjin Jalal Ahmad Arabi, ya kuma bayyana cewa za ayi jigilar maniyyata aikin hajjin ne daga cibiyoyi 10 a faɗi ƙasar nan.

Continue Reading

Labarai

Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Laraba a matsayin ranar hutu

Published

on

Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Laraba, 1 ga watan Mayun 2024, a matsayin ranar hutu, domin bikin ranar ma’aikata na wannan shekara.

Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayyana hakan, a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Talata.

Olubunmi, ya kuma sake nanata buƙatar ganin ma’aikata sun jajirce da yin aiki yadda ya kamata a dukkanib matakai daban-daban.

Continue Reading

Labarai

Wahalar Fetur ta haifar mana da koma baya a sana’ar mu – Mai Motar Haya

Published

on

Wani mai sana’ar tuƙin motar Haya, da kuma lodin fasinjoji mai suna Kabiru Muhammad, mazaunin ƙaramar hukumar Munjibir, ya ce ƙarancin motocin Haya da ake samu a yanzu, yana da alaƙa da wahalar man Fetur da ake fuskanta a sassan Najeriya.

A zantawar mutumin da wakilinmu Yusuf Nadabo Isma’il, ta cikin shirin rahotanni daga ƴan Zazu na yau Talata, ya ce a baya har motoci hamsin suke yiwa lodin fasinjoji su tashi, amma a yanzu Mota ɗaya suke iya cikawa sakamakon ƙarancin Fetur da ake fama da shi.

Ya kuma ce ƙaranci tare da tsadar man fetur ɗin da ake fama da shi, sun haddasa musu koma baya a sana’ar su, baya ga batun kuma matsalar da suke fuskanta da fasinjoji wajen biyan kuɗin Mota.

Wakiliyarmu da ta bibiyi shirin na ƴan Zazu Ummi Bala Ahmad ta rawaito cewa, matuƙin motar Kabiru Muhammad, ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jahohi, da su yi abinda ya kamata dan ganin farashin man Fetur ɗin ya sauka, domin al’umma su samun sauƙi.

Continue Reading

Trending