Connect with us

Labarai

Mawadata su rinka tallafawa mabukata da naman layya – Mansur Gabari

Published

on

Gidauniyar tausayawa da tallafawa mabukata wato Empathy Foundation ta ja hankalin al’ummar da suka sami damar gudanar da ibadar layya da su rika tallafawa yaran da ke tsare a gidajen masu lalurar kwakwalwa dana gidajen kangararru da naman layyar da suka yi domin sanya farin ciki a zukatan su.

Shugaban gidauniyar Mansur Musa Gabari ne ya bayyana hakan a yayin ziyarar da gidauniyar ta kai gidan gajiyayyu na Yakasai dana Bichi da Danbatta domin basu tallafin nama da Biredi da Biskit da kuma Suturu.

Ya ce, “Mawadata su rinka taimakawa marasa karfi musamman wadanda ba su sami damar yin layya ba da naman domin samun ladan da ke cikin hakan”.

Ya kuma ce, “Ya na da kyau al’umma su rinka ziyartar gidajen masu lalurar kwakwalwa da ke kauyuka domin duba irin halin da su ke ciki wajen kai musu dauki”. Mansur Musa Gabari

Mansur Musa Gabari ya kuma yi kira ga gwamnatin data kara yawan ma’aikatan dake kula da gidajen masu matsalar ta kwakwalwa da sauran gidajen da ake tsare al’umma don kara inganta tsaro a gidajen.

Labarai

NAHCON ta sanya ranar fara jigilar maniyyata aikin hajjin bana zuwa Saudiyya

Published

on

Yanzu haka hukumar Aikin Hajji ta ƙasa NAHCON, ta 15 ga watan nan na Mayun 2024, a matsayin ranar da za’a fara jigilar maniyyata aikin hajjin bana, zuwa ƙasa mai tsarki.

Bayanin hakan ya fito ne ta bakin shugaban hukumar ta NAHCON, Jalal Ahmad Arabi, a wajen taron masu ruwa da tsaki kan aikin Hajji da Umrah, da ya gudana yau Alhamis birnin tarayya Abuja.

“Maniyyata kimanin 65,500 ne za su sauke Farali daga ƙasar nan a ƙasa mai tsarki; za su shafe aƙalla kwanaki huɗu domin yin ziyara a Madina kafin fara aikin Hajji, “in ji Arabi”.

Daga bisani shugaban hukumar aikin hajjin Jalal Ahmad Arabi, ya kuma bayyana cewa za ayi jigilar maniyyata aikin hajjin ne daga cibiyoyi 10 a faɗi ƙasar nan.

Continue Reading

Labarai

Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Laraba a matsayin ranar hutu

Published

on

Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Laraba, 1 ga watan Mayun 2024, a matsayin ranar hutu, domin bikin ranar ma’aikata na wannan shekara.

Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayyana hakan, a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Talata.

Olubunmi, ya kuma sake nanata buƙatar ganin ma’aikata sun jajirce da yin aiki yadda ya kamata a dukkanib matakai daban-daban.

Continue Reading

Labarai

Wahalar Fetur ta haifar mana da koma baya a sana’ar mu – Mai Motar Haya

Published

on

Wani mai sana’ar tuƙin motar Haya, da kuma lodin fasinjoji mai suna Kabiru Muhammad, mazaunin ƙaramar hukumar Munjibir, ya ce ƙarancin motocin Haya da ake samu a yanzu, yana da alaƙa da wahalar man Fetur da ake fuskanta a sassan Najeriya.

A zantawar mutumin da wakilinmu Yusuf Nadabo Isma’il, ta cikin shirin rahotanni daga ƴan Zazu na yau Talata, ya ce a baya har motoci hamsin suke yiwa lodin fasinjoji su tashi, amma a yanzu Mota ɗaya suke iya cikawa sakamakon ƙarancin Fetur da ake fama da shi.

Ya kuma ce ƙaranci tare da tsadar man fetur ɗin da ake fama da shi, sun haddasa musu koma baya a sana’ar su, baya ga batun kuma matsalar da suke fuskanta da fasinjoji wajen biyan kuɗin Mota.

Wakiliyarmu da ta bibiyi shirin na ƴan Zazu Ummi Bala Ahmad ta rawaito cewa, matuƙin motar Kabiru Muhammad, ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jahohi, da su yi abinda ya kamata dan ganin farashin man Fetur ɗin ya sauka, domin al’umma su samun sauƙi.

Continue Reading

Trending