Connect with us

Labarai

Ana zargin wani magidanci da yunkurin haikewa ‘yar shekaru biyar

Published

on

Ana zargin wani magidanci da yunkurin haikewa wata karamar yarinya ‘yar shekaru 5, a unguwar Gaida da ke karamar hukumar Kumbotso.

Ana zargin magidancin yaja yarinyar zuwa gidan sa ya na kokarin haike mata inda wasu matasan unguwar su ka dauki doka a hannu su ka fara dukan sa, sai dai kuma jami’an Bijilante sun shiga tsakani sun mika shi ga mahukanta.

Shugaban kungiyar Bijilante da ke yankin Shekarau Ali ya ce, “Mutumin dama muna samun sa da laifukan shan giya yana daukar kayan mutane, yau kuma ya sha giya ya dauki yarinyar ya shiga gidansa har daki zai haike mata, amma jami’an mu sun je sun kama shi da kaya a tube”.

Ya kuma ce, “Mutanen unguwa har sun fara dukan sa, suna yi masa ihu mu ka zo mu ka karbe shi mu ka tafi da shi zuwa shelkwatar hukumar Hisba”.

Ya kara da cewa, “Duk wanda mu ka kama da laifi irin wannan mu na kai shi wajen Dakaci da kuma Hakimi sannan ya tashi ya bar mana unguwa”. A cewar Shekarau Ali

A nasa bangaren, mahaifin yarinyar ya ce, “Muna cikin aiki a ka zo a ka ce min ga wani mutum can yaje ya kai ‘yata cikin gidansa muna zuwa muka tarar ya kwantar da ita a daki ya na kokarin haike mata, mutumin ba shi da mata, don haka muna zargin sa da yunkurin aikata fyade”. Inji mahaifin yarinyar

Wakilin mu Abba Isah Muhammad ya rawaito cewa, bai samu damar zantawa da mutumin da a ke zargi ba kasancewar ya na hannun hukuma.

Labarai

Ku tallafawa mazauna gidajen gyaran halin dan rage musu raɗaɗin rayuwa – Mallam Ibrahim Bunkure

Published

on

Limamin masallacin Salafussaleh dake unguwar Ɗorayi ƙarama a jihar Kano, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya shawarci al’umma da su ƙara dagewa wajen tallafawa mazauna gidajen ajiya da gyaran hali, da masu buƙata ta musamman, domin rage musu wani raɗaɗin rayuwa na yau da kullum.

Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya bayyana hakan ne yayin da suka tallafawa mazauna gidan gyaran hali na Goron Dutse, da kayayyakin Abinci, da kuma na gidan yara, a wani ɓangare na taya su bikin ƙaramar Sallah, wajen ganin sun samu farin ciki a bukukuwan ƙaramar sallar da aka gudanar.

Ya ce matuƙar masu hali za su rinƙa tallafawa mazauna gidan gyaran halin da abubuwan da suka sawwaƙa, babu makawa za’a rage musu wata damuwa ta yau da kullum.

Wakilinmu Yakubu Ibrahim Dogarai ya rawaito cewa, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya ce daga cikin kayan abincin da suka kai wa mazauna gidajen akwai Tuwon Sallah, da garin Kwakwaki, da kuma sinadarin Ɗanɗano, da Sukari, domin ragewa mazaunan gidajen wani raɗaɗin rayuwa.

Continue Reading

Labarai

Iyaye ku dai ma marawa ƴaƴan ku baya akan abinda suke yi da ya saɓawa doka – Mai unguwar Ja’en Jigawa

Published

on

Mai unguwar Ja’en Jigawa da ke ƙaramar hukumar Gwale a jihar Kano Sani Muhammad, ya ce bai kamata a rinƙa samun wasu iyaye da ɗabi’ar nan ta marawa ƴaƴan su baya akan abinda yaran suke aikatawa na saɓawa Doka, domin gujewa abinda ka je ya dawo.

Mai unguwar ya bayyana hakan ne yayin zantwarsa da gidan rediyon Dala FM, a lokacin da yake tsokaci kan yadda ake samun wasu daga cikin iyayen yankin sa na marawa ƴaƴan su baya kan abinda suke yi na ba dai dai ba, lamarin da yake ƙara ƙara kangarar da tarbiyyar ƴaƴan tare da tayar da hankalin al’umma.

Mai unguwa Sani Muhammad, ya kuma ce matuƙar yaran ba za su zauna lafiya a cikin unguwa da al’umma ba, to kuwa za su rinƙa ɗaukar matakin miƙa yaran hannun jami’an tsaro mafi kusa, domin ɗaukar matakin da ya dace a kan su, wajen ganin sun sauke nauyin da aka ɗora musu.

Sani Muhammad, ya ƙara da cewa ko a baya bayan nan wasu matasa sai da suka yi yunƙurin yin abinda bai kamata ba, lamarin da yasa aka ɗauki mataki a kansu amma aka samu wasu daga cikin iyaye suka marawa yaran nasu baya, wanda hakan kan haifar da barazanar tsaro.

Continue Reading

Labarai

Matasa ku ƙara dagewa da neman Ilmin addini da na zamani – Dr. Abdallah Gadan Kaya

Published

on

Fitaccen malamin addinin Musluncin nan Dakta Abdallah Usman Umar, ya shawarci matasa da su ƙara mayar da hankali wajen neman ilmin addinin da na zamani, domin zama ababen koyi a tsakanin al’umma.

Dakta Abdallah Gadan Ƙaya, ya bayyana hakan ne ta cikin Tafsirin Al-ƙur’ani mai girma, da yake gabatarwa cikin wannan watan azumin Ramadana a jihar Gombe.

A cewar sa, “Akwai buƙatar matasa ku yi riƙo da ƙananan sana’o’in dogaro da kai, da za ku rinƙa biyawa kan ku kuɗin makaranta wajen neman ilimi domin kaucewa zama a cikin jahilci, “in ji shi”.

Dakta Abdallah, ya kuma yi kira ga shugabanni da su dukkan abinda ya dace wajen inganta makarantu a sassan ƙasar nan, domin ganin ɗalibai sun samu ingantaccen Ilmi.

Continue Reading

Trending