Connect with us

Labarai

Sha’iri ya auri mata ba tare da sanin mahaifin ta ba

Published

on

Wani fitaccen sha’iri mai gudanar da majalisi a jihar Kano a na zargin ya angwance da amaryar sa ba tare da sanin iyayen ta ba.

Sha’irin ya gurfana ne a gaban kotun shari’ar musulunci dake zaman ta a unguwar Goran Dutse, inda a ke zargin sha’irin ya hada kai da mahaifiyar Amaryar sa a ka daura ma su aure ba tare da sanin waliyin ta ba, wanda ta kai har ta tare a gidan sa, yayin da kuma saura kwanaki kadan a yi bikin ta da wani mutum daban.

Sai dai Ango da Amaryar su na zaman auren ne mahaifin ta da ya ke baya gari, ya dawo ya ji labarin auren su, nan kuma take ya garzaya tare da waliyin Amarya gidan, domin tabbatar da al’amarin, daga bisani su ka shigar da kara a kotun shar’ar musulunci.

Tuni dai kotun ta zauna ta saurari karar, kuma lauyan wanda a ke zargi ya gabatar da da’awar cewar, mahaifin ta ba shi da hurumin da zai yi mata walicci, saboda tsawon lokaci ba shi yake ciyar da ita ba, hasali ma kuma kula da ita ba shi ne ba, domin haka hakkin walicci ya tashi a kan sa.

A nasa bangaren, shima lauyan masu kara ya ce,” Sai dai kotun ta sanya Amaryar a igiyar wakafi tun da akwai shakku a kan auren a na cikin shari’a”.

Kazalika, kotun ta sanya Amaryar a hannun wakafi, inda a ka damka ta a hannun yayan ta, kuma babu batun ci gaba da zama a gidan sha’irin, har sai an gama kammala zaman kotu.

Kotun kuma ta umarci Angon ya dauko Amaryar ta sa da hannun sa ya kawo ta wajen yayan ta, domin ta ci gaba da zama a hannun sa.

Labarai

Ƴan kasuwa ku tsaftace magudanan ruwa bisa gabatowar Damuna – Ƙungiyar Amata ta kasuwar Singa

Published

on

An buƙaci ƴan kasuwa da su rinƙa tsaftace tare da gyara magudanan ruwa a cikin kasuwannin su, bisa yadda damuna ke ƙara gabatowa.

Shugaban ƙungiyar Amata reshen kasuwar Singa Alhaji Musa Ibrahim Ɗan gaske, ne ya bukacin hakan a zantawar sa da manema labarai, yayin kaddamar da tsaftace kasuwar da kuma gyara mugudanun ruwan kasuwar.

Alhaji Musa, ya kuma ce ta hanyar tsaftace magudanan ruwan ne za a gujewa kowacce irin ambaliyar ruwa a cikin kasuwanni.

Continue Reading

Hangen Dala

Yau za’a fara Shari’ar Ganduje da gwamnatin Kano

Published

on

A yau ne babbar kotun jaha mai lamba 4 zata fara sauraron wata sharia wadda gwamnatin kano ta ahigar.

 

Gwamnatin jahar kano dai ta shigar da karar tsohon gwamnan jahar kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da mai dakinsa Hafsat Umar Ganduje da kuma dansu Umar Abdullahi Ganduje da kuma wani kamfani mai suna Lamash da kuma Dr Jibrilla Muhammad.

 

Gwamnatin jahar kano dai tana zargin Ganduje da wadanna mutane da laifin hada baki da barnatar da dukiyoyin gwamnati.

 

 

Cikin zarge-zargen da ake yiwa su Ganduje akwai batun sun sayar da wasu filotai ba bisa ka’ida ba.

 

 

Da kuma batun zargin da akewa Ganduje na badakalar karbar dala tun a shekarar 2019.

 

 

Yanzu haka an girke jami,an tsaro a harabar sakateriyar Audu Bako inda kuma daga yanzu zuwa kowane lokaci kotun zata fara sauraron korafin kamar yadda wakilinmu Yusuf Nadabo Ismail ya rawaito

Continue Reading

Labarai

Ku tallafawa mazauna gidajen gyaran halin dan rage musu raɗaɗin rayuwa – Mallam Ibrahim Bunkure

Published

on

Limamin masallacin Salafussaleh dake unguwar Ɗorayi ƙarama a jihar Kano, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya shawarci al’umma da su ƙara dagewa wajen tallafawa mazauna gidajen ajiya da gyaran hali, da masu buƙata ta musamman, domin rage musu wani raɗaɗin rayuwa na yau da kullum.

Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya bayyana hakan ne yayin da suka tallafawa mazauna gidan gyaran hali na Goron Dutse, da kayayyakin Abinci, da kuma na gidan yara, a wani ɓangare na taya su bikin ƙaramar Sallah, wajen ganin sun samu farin ciki a bukukuwan ƙaramar sallar da aka gudanar.

Ya ce matuƙar masu hali za su rinƙa tallafawa mazauna gidan gyaran halin da abubuwan da suka sawwaƙa, babu makawa za’a rage musu wata damuwa ta yau da kullum.

Wakilinmu Yakubu Ibrahim Dogarai ya rawaito cewa, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya ce daga cikin kayan abincin da suka kai wa mazauna gidajen akwai Tuwon Sallah, da garin Kwakwaki, da kuma sinadarin Ɗanɗano, da Sukari, domin ragewa mazaunan gidajen wani raɗaɗin rayuwa.

Continue Reading

Trending