Connect with us

Labarai

Kisan wuta: Magidanci ya kai karar tsohon mijin matar sa kotu

Published

on

A na zargin wani mutum mai suna Usman Ali dake unguwar Dabai a jihar Kano da bibiyar tsohuwar matar sa da ya sake ta, bayan ta tare a gidan sabon mijin ta, har ma kuma ake zargin ya saya mata waya yana kiran ta suna haduwa a wani wajen daban.

Tun da fari dai an gabatar da Usman Ali a kotun shari’ar musulunci dake Post Office, daga bisani alkalin ya bukaci a mayar da shi wajen ‘yan sanda domin su fadada bincike, bayan kuma sun yi binciken aka mika takardar tuhumar harabar rukunin kotuna dake Sakatariyar Audu Bako domin sanin kotun da za’a fara sauararen karar.

A zantawar gidan rediyon Dala da sabon mijin matar mai suna, Malam Musbahu Nasir a ranar Talata ya bayyana yadda al’amarin ya faru.

“Duk bibiyar da ake yiwa mata ta tsawon shekaru biyu da rabi, Allah ne da ikon sa yake kare ta, shekarar da ta gabata har fitar da ita ya yi daga gida na ya bata kudin mota ta tafi garin ‘yan uwan mahaifiyar ta domin su zo a raba aure na da ita, daga baya iyayenta da na aure ta a hannunsu su ka gane gaskiyar al’amarin su ka dawo da ita su ka ga ma ba’a hayyacinta take ba”.

Ya kuma ce, “So yake yi in sake ta ya sake aure ta, saboda shi ya cutar da ita a lokacin da su ka yi aure, ni kuma na gane haka, amma bai daina ba ya ci gaba da bibiyar ta, har ‘ya’yan ta ya aiko da magani ta rinka sha shafawa, sai daga baya ta gane, a shekarar nan ma sai da ya kuma fitar da ita daga gidan ta bar jihar ta tafi wajen wan mahaifiyar ta, ya dawo da ita gida, amma a karshe bayan an yi addu’a da kanta ta bukaci ganina ta kuma ce za ta bayyana min duk abubuwan da su ka faru, ta nuna min waya ta ce tafi wata uku da ita muke waya da shi”.

Ya kara da cewa, “To ina gayawa duniya yanzu na fara son mata ta, kuma da ta zo gidana ta samu kulawa, ba zagi ba wulakanci, bata shekara ba ta canja, ai bai iya zama da mace ba, mace ‘yar rarrashi ce… Ni bukata ta na yarda shari’a za ta yi adalci a kan abun da yayi min, domin ina da shaidu”. A cewar Malam Musbahu Nasir

Wakilin mu Ibrahim Abdullahi Soron dinki ya rawaito cewar, ya tuntubi Usman Ali wanda ake zargi, amma ya ce baya tare da lauyan sa, saboda haka  ba zai iya cewa komai ba.

Labarai

Ƴan kasuwa ku tsaftace magudanan ruwa bisa gabatowar Damuna – Ƙungiyar Amata ta kasuwar Singa

Published

on

An buƙaci ƴan kasuwa da su rinƙa tsaftace tare da gyara magudanan ruwa a cikin kasuwannin su, bisa yadda damuna ke ƙara gabatowa.

Shugaban ƙungiyar Amata reshen kasuwar Singa Alhaji Musa Ibrahim Ɗan gaske, ne ya bukacin hakan a zantawar sa da manema labarai, yayin kaddamar da tsaftace kasuwar da kuma gyara mugudanun ruwan kasuwar.

Alhaji Musa, ya kuma ce ta hanyar tsaftace magudanan ruwan ne za a gujewa kowacce irin ambaliyar ruwa a cikin kasuwanni.

Continue Reading

Hangen Dala

Yau za’a fara Shari’ar Ganduje da gwamnatin Kano

Published

on

A yau ne babbar kotun jaha mai lamba 4 zata fara sauraron wata sharia wadda gwamnatin kano ta ahigar.

 

Gwamnatin jahar kano dai ta shigar da karar tsohon gwamnan jahar kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da mai dakinsa Hafsat Umar Ganduje da kuma dansu Umar Abdullahi Ganduje da kuma wani kamfani mai suna Lamash da kuma Dr Jibrilla Muhammad.

 

Gwamnatin jahar kano dai tana zargin Ganduje da wadanna mutane da laifin hada baki da barnatar da dukiyoyin gwamnati.

 

 

Cikin zarge-zargen da ake yiwa su Ganduje akwai batun sun sayar da wasu filotai ba bisa ka’ida ba.

 

 

Da kuma batun zargin da akewa Ganduje na badakalar karbar dala tun a shekarar 2019.

 

 

Yanzu haka an girke jami,an tsaro a harabar sakateriyar Audu Bako inda kuma daga yanzu zuwa kowane lokaci kotun zata fara sauraron korafin kamar yadda wakilinmu Yusuf Nadabo Ismail ya rawaito

Continue Reading

Labarai

Ku tallafawa mazauna gidajen gyaran halin dan rage musu raɗaɗin rayuwa – Mallam Ibrahim Bunkure

Published

on

Limamin masallacin Salafussaleh dake unguwar Ɗorayi ƙarama a jihar Kano, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya shawarci al’umma da su ƙara dagewa wajen tallafawa mazauna gidajen ajiya da gyaran hali, da masu buƙata ta musamman, domin rage musu wani raɗaɗin rayuwa na yau da kullum.

Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya bayyana hakan ne yayin da suka tallafawa mazauna gidan gyaran hali na Goron Dutse, da kayayyakin Abinci, da kuma na gidan yara, a wani ɓangare na taya su bikin ƙaramar Sallah, wajen ganin sun samu farin ciki a bukukuwan ƙaramar sallar da aka gudanar.

Ya ce matuƙar masu hali za su rinƙa tallafawa mazauna gidan gyaran halin da abubuwan da suka sawwaƙa, babu makawa za’a rage musu wata damuwa ta yau da kullum.

Wakilinmu Yakubu Ibrahim Dogarai ya rawaito cewa, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya ce daga cikin kayan abincin da suka kai wa mazauna gidajen akwai Tuwon Sallah, da garin Kwakwaki, da kuma sinadarin Ɗanɗano, da Sukari, domin ragewa mazaunan gidajen wani raɗaɗin rayuwa.

Continue Reading

Trending