Connect with us

Labarai

Binne gawa: Matashi ya dauke wa mutum waya a makabarta

Published

on

A na zargin wani matashi mai suna Abdullahi Idris Sudawa mai shekaru 40, da satar waya a na tsaka da binne gawa a makabartar Abbatuwa da ke Kofar Mazugal.

Matashin dai al’ummar da su ka zo binne gawar sun yi nasarar kama shi ne bayan ya yanka aljihun wani mutum ya na yunkurin satar wayar lokacin da a ke binne gawa.

Gidan radiyon Dala ya zantawa da Abdullahi Idris inda ya bayyana yadda al’amarin ya faru.

Ya ce, “Waya ce na dauka kuma na bai wa mai ita kayar sa, a cikin makabarta ne abun ya faru, ban san mai ita ba, amma kuma na ba shi kayan shi, ba ‘yan unguwar mu ba ne, tsayawa na yi addu’a… Gaskiya na fada na dauka na kuma bayar, ban san kudin wayar ba, kuma da yardar Allah na yi na farko na yi na karshe, idan na sata a kwai wanda na ke kai wa a Wapa ya siya… Kauyuka na ke zuwa yin sata, idan mutum ya na tafiya in saka masa hannu a aljihun gefe”. A cewar Abdullahi Idris

Suma dai wasu daga cikin wadanda su ka halarci binne gawar kuma abun ya faru a kan idanunsu sun yi mana karin bayani.

“Sunana Zahradden Shu’aibu Haruna. Mun je makabartar Abbatuwa mun ajiye baburan mu mun shiga ciki sai a ka kama wasu sun yanka aljihun mutane su na kokarin daukar mu su wayoyi, sai mu ka fito fito waje, na zo zan dauki babur di na na gan shi a bude, abun ya razana ni, wannan abun ya zama ruwan dare, a dauke wa mutane abun hawa”.

“Sunana Isah Rabi’u Ahmad Goran dutse. Daya daga cikin wadanda su ka kama gawa za’a saka a kabari wayar sa ta fada cikin kabari ya zaro wayar ya miko a rike masa, a wajen ba’a san wanda ya karbi wayar ba saboda rashin imani na al’umma, sannan a ka samu mutane an yanka masu aljihu, mu ka fito mu ka ga an bude kan baburan mu”. A cewar ganau

Shugaban ‘yan bijilante na yankin Kofar Mazugal, Danlami Kwamanda ya ce, “Abun ya ba ni mamaki, rashin tsoron Allah irin na mutane, a cikin makabarta an zo sa gawa, amma barayi su zo suna sata a makabarta, ka duba yadda kan babura su ke a bude, barawon nan ba shi kadai ba ne”. Inji Danlami Kwamanda

Wakilin mu Abubakar Sabo ya rawaito cewar, Danlami Kwamanda ya kuma ce, yanzu matakin da za su dauka sai sun ga karshen wannan abun, domin za su kai shi ga hukuma a dauki matakin.

Labarai

Gwamnatin Kano za ta inganta filaye da bunƙasa duk ɓangarorin wasannin matasa – Kwamishinan Matasa da Wasanni

Published

on

Sabon kwamishinan ma’aikatar wasanni da ci gaban matasa na Jihar Kano Mustapha Rabi’u Musa kwankwaso, ya bada tabbacin cewar Gwamnatin Jihar za ta ɗauki matakin inganta filayen tare da bunƙasa duk wasu ɓangarorin wasanni da matasa ke yi.

Mustapha Rabi’u Musa Kwankwaso, ya bayyana hakan ne yayin da ya kama aiki yau Asabar, tare da kai ziyara a wasu filayen wasannin dake ihar Kano.

Daga cikin filayen wasannin da ya ziyarta akwai filin wasa na Sani Abacha da ke ƙofar Mata, da filin wasa na Kano Pillars da ke sabon Gari, da kuma filin wasa na Ado Bayero Square dake unguwar Sabon Gari, sai kuma filin wasa na Mahaha da ke ƙofar Na’isa.

Da yake jawabi bayan kammala ziyarar kwamishinan wasannin da ci gaban Matasa na jihar Kano, Mustapha Rabi’u Musa kwankwaso, ya ce ya gudanar da ziyarar ce domin sanin halin da filayen wasannin ke ciki.

A lokacin ziyarar kwamishinan na tare da mai bai wa Gwamnan Kano shawara a kan harkokin wasanni Ambasada Yusuf Imam Ogan Ɓoye, da shugaban magoya bayan ƙungiyar ƙwallon Ƙafa ta Kano Pillars Alhaji Rabi’u Abdullahi Kawo, da kuma mai riƙon Shugabancin hukumar wasanni ta jiha Malam Bala Sani Shehu.

Continue Reading

Labarai

Muna sane da ƙarancin Ruwa a wasu sassan Kano – Hukumar rarraba ruwan Sha

Published

on

Hukumar rarraba ruwan sha ta jihar Kano ta ce matsalar rashin samun ruwa da ake fuskanta a wasu sassan jihar Kano, yana da alaƙa ne da lalacewar wani abun kan Famfo a madatsar ruwan da ke Tamburawa.

Shugaban hukumar Injiniya Garba Ahmad Bichi, ne ya bayyana haka yayin zantawar sa da manema labarai, ya ce cikin guraren da za’a yiwa gyaran har da madatsar ruwa ta Challawa da Watari, da amincewar gwamnatin jihar Kano.

Injiniya Garba, ya kuma ce suna sane da ƙarancin ruwan da ake fuskan ta a wasu sassan jihar Kano, amma nan gaba kaɗan za kammala gyaran kan famfon, domin ganin an wadata sassan jihar Kano, da ruwan domin ganin sun samu wani sauƙi.

 “Mu ma a ɓangaren mu Bama jin daɗin yadda al’umma suke rasa ruwa a sassan jihar Kano, kuma nan da ranar Litinin mutane za su fita daga cikin wannan matsala ta rashin Ruwa, a yanku nan su, “in ji shi”

Garba Ahmad, ya kuma ƙara da cewa matsalar fashewar Fayif da aka samu a ci gaba da aikin gadar mahaɗar Ɗan Agundi, yanzu haka suna kan ɗaukar mataki tsakanin su da kamfanin da suka taka har ya fashe, dan ganin an gyara al’ummar da ake baiwa ruwa su ci gaba da damu.

Continue Reading

Labarai

Ƴan kasuwa ku tsaftace magudanan ruwa bisa gabatowar Damuna – Ƙungiyar Amata ta kasuwar Singa

Published

on

An buƙaci ƴan kasuwa da su rinƙa tsaftace tare da gyara magudanan ruwa a cikin kasuwannin su, bisa yadda damuna ke ƙara gabatowa.

Shugaban ƙungiyar Amata reshen kasuwar Singa Alhaji Musa Ibrahim Ɗan gaske, ne ya bukacin hakan a zantawar sa da manema labarai, yayin kaddamar da tsaftace kasuwar da kuma gyara mugudanun ruwan kasuwar.

Alhaji Musa, ya kuma ce ta hanyar tsaftace magudanan ruwan ne za a gujewa kowacce irin ambaliyar ruwa a cikin kasuwanni.

Continue Reading

Trending