Connect with us

Labarai

Iyaye na taimakawa wajen lalacewar tarbiyar matasa – Kwamaret Adamu

Published

on

Wani wani matashi dan gwagwarmaya, Kwamaret Adamu Dayi ya ce, iyaye na taka rawar gani wajen lalacewar tarbiyar matasa a wannan zamanin.

Kwamaret Adamu ya bayyana hakan ne a zantawar sa da gidan rediyon Dala ranar Alhamis.

Ya ce, “Matsalolin da su ke damun matasa a yau, ni a nawa tunanin abubuwa ne guda uku, idan kayi aure ka haifi yaro, nauyin kula da shi yana wuyan ka, kafin ya fito waje a samu malamai, da sauran al’umma su bashi wata tarbiyar, to da zarar iyayen sun sakaci ya fito babu kulawa a nan tarbiyar sa take lalacewa”.

Ya kuma ce, “Abun da yake damun iyaye a yanzu shi ne mu na shagwaba ‘ya’yan mu, mu na nuna masu soyayya fiye da tarbiya, shi yasa makwabci baka isa ka tsawatarwa dan makawabci ba, haka ma abun yake a cikin family… Kalubale ga gwamnati, ya kamata a ce gwamnati ta koma ga tsari irin na da, iyaye su hada kai da malamai, malamai su hada kai da gwamnati, gwamnati kuma ta hada kai da Dagatai, to za’a samu sauki”.

Ya kara da cewa, “Idan iyaye su ka saki ‘ya’yan su a hanya dole su nemi abun da za su ci da kan su, wasu ‘yan siyasar kuma masu neman mukami a ofisoshi su kwashe su sun zama ‘yan kwaya da ‘yan daba domin biyan bukatun su, ta hanyar ba su kudi da kuma odar makamai”. A cewar Kwamaret Adamu Dayi

Wakilin mu Yusuf Nadabo Isma’il ya rawaito cewar, Kwamaret Adamu Dayi ya kuma yi kira ga matasa a kan su san mahimmancin rayuwar su, ta hanyar yin karatu da sana’a domin yin rayuwa mai inganci.

 

 

 

 

 

Labarai

Ƴan kasuwa ku tsaftace magudanan ruwa bisa gabatowar Damuna – Ƙungiyar Amata ta kasuwar Singa

Published

on

An buƙaci ƴan kasuwa da su rinƙa tsaftace tare da gyara magudanan ruwa a cikin kasuwannin su, bisa yadda damuna ke ƙara gabatowa.

Shugaban ƙungiyar Amata reshen kasuwar Singa Alhaji Musa Ibrahim Ɗan gaske, ne ya bukacin hakan a zantawar sa da manema labarai, yayin kaddamar da tsaftace kasuwar da kuma gyara mugudanun ruwan kasuwar.

Alhaji Musa, ya kuma ce ta hanyar tsaftace magudanan ruwan ne za a gujewa kowacce irin ambaliyar ruwa a cikin kasuwanni.

Continue Reading

Hangen Dala

Yau za’a fara Shari’ar Ganduje da gwamnatin Kano

Published

on

A yau ne babbar kotun jaha mai lamba 4 zata fara sauraron wata sharia wadda gwamnatin kano ta ahigar.

 

Gwamnatin jahar kano dai ta shigar da karar tsohon gwamnan jahar kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da mai dakinsa Hafsat Umar Ganduje da kuma dansu Umar Abdullahi Ganduje da kuma wani kamfani mai suna Lamash da kuma Dr Jibrilla Muhammad.

 

Gwamnatin jahar kano dai tana zargin Ganduje da wadanna mutane da laifin hada baki da barnatar da dukiyoyin gwamnati.

 

 

Cikin zarge-zargen da ake yiwa su Ganduje akwai batun sun sayar da wasu filotai ba bisa ka’ida ba.

 

 

Da kuma batun zargin da akewa Ganduje na badakalar karbar dala tun a shekarar 2019.

 

 

Yanzu haka an girke jami,an tsaro a harabar sakateriyar Audu Bako inda kuma daga yanzu zuwa kowane lokaci kotun zata fara sauraron korafin kamar yadda wakilinmu Yusuf Nadabo Ismail ya rawaito

Continue Reading

Labarai

Ku tallafawa mazauna gidajen gyaran halin dan rage musu raɗaɗin rayuwa – Mallam Ibrahim Bunkure

Published

on

Limamin masallacin Salafussaleh dake unguwar Ɗorayi ƙarama a jihar Kano, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya shawarci al’umma da su ƙara dagewa wajen tallafawa mazauna gidajen ajiya da gyaran hali, da masu buƙata ta musamman, domin rage musu wani raɗaɗin rayuwa na yau da kullum.

Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya bayyana hakan ne yayin da suka tallafawa mazauna gidan gyaran hali na Goron Dutse, da kayayyakin Abinci, da kuma na gidan yara, a wani ɓangare na taya su bikin ƙaramar Sallah, wajen ganin sun samu farin ciki a bukukuwan ƙaramar sallar da aka gudanar.

Ya ce matuƙar masu hali za su rinƙa tallafawa mazauna gidan gyaran halin da abubuwan da suka sawwaƙa, babu makawa za’a rage musu wata damuwa ta yau da kullum.

Wakilinmu Yakubu Ibrahim Dogarai ya rawaito cewa, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya ce daga cikin kayan abincin da suka kai wa mazauna gidajen akwai Tuwon Sallah, da garin Kwakwaki, da kuma sinadarin Ɗanɗano, da Sukari, domin ragewa mazaunan gidajen wani raɗaɗin rayuwa.

Continue Reading

Trending