Connect with us

Labarai

Anti-Corruption: Mu na so ta bibiyi hakkokin mu – Ma’aikatan kamfani

Published

on

Wasu ma’aikan wani kamfani a garin Panshekara da ke karamar hukumar Kumbotso, sun gabatar da korafi a hukumar karbar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano, karkashin jagorancin Barista Muhyi Magaji Rimin Gado a kan bibiyar hakkokin su da su ke zargin kamfanin ya danne masu.

A zantawar gidan rediyon Dala da wasu daga cikin ma’aikatan kamfanin sun bayyana korafin da su ke yi a kan kamfanin.

“Sunana Sulaiman D. Sani, mun kawo koke a wannan hukuma, a kan kamfanin da mu ke aiki, shekarar mu goma sha daya mu na aiki su ka sallame mu, su ka bamu kudin da bai taka kara ya karya ba, kuma ba wani dalili daya sa a ka sallame mu, da farko an sallami mutane 18, daga baya kuma a ka sallami mutane 14, kuma a kaso uku, kaso daya su ke bayarwa, an yakar mana kudin Fansho, wata ashirin da daya, akwai kuma ‘yan uwan mu da su ka samu raunuka ba’a biya su kudin diyya ba”.

“Sunana Bashir Yahuza, mu na so wannan hukuma ta kwato mana hakkokin mu dama sauran al’ummar da ke aiki a yanzu suna can an kulle su ba’a biyan su albashi yadda ya kamata”. A cewar wasu daga cikin ma’aikatan kamfanin

Wakilin mu Abba Isah Muhammad ya rawaito cewar, daga cikin masu korafin har da wani matashi mai suna Rabi’u Idris, wanda ya ji rauni, mashin ya kama hannun sa, tsawon shekaru uku ba’a ba shi diyya ba.

Labarai

Ƴan kasuwa ku tsaftace magudanan ruwa bisa gabatowar Damuna – Ƙungiyar Amata ta kasuwar Singa

Published

on

An buƙaci ƴan kasuwa da su rinƙa tsaftace tare da gyara magudanan ruwa a cikin kasuwannin su, bisa yadda damuna ke ƙara gabatowa.

Shugaban ƙungiyar Amata reshen kasuwar Singa Alhaji Musa Ibrahim Ɗan gaske, ne ya bukacin hakan a zantawar sa da manema labarai, yayin kaddamar da tsaftace kasuwar da kuma gyara mugudanun ruwan kasuwar.

Alhaji Musa, ya kuma ce ta hanyar tsaftace magudanan ruwan ne za a gujewa kowacce irin ambaliyar ruwa a cikin kasuwanni.

Continue Reading

Hangen Dala

Yau za’a fara Shari’ar Ganduje da gwamnatin Kano

Published

on

A yau ne babbar kotun jaha mai lamba 4 zata fara sauraron wata sharia wadda gwamnatin kano ta ahigar.

 

Gwamnatin jahar kano dai ta shigar da karar tsohon gwamnan jahar kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da mai dakinsa Hafsat Umar Ganduje da kuma dansu Umar Abdullahi Ganduje da kuma wani kamfani mai suna Lamash da kuma Dr Jibrilla Muhammad.

 

Gwamnatin jahar kano dai tana zargin Ganduje da wadanna mutane da laifin hada baki da barnatar da dukiyoyin gwamnati.

 

 

Cikin zarge-zargen da ake yiwa su Ganduje akwai batun sun sayar da wasu filotai ba bisa ka’ida ba.

 

 

Da kuma batun zargin da akewa Ganduje na badakalar karbar dala tun a shekarar 2019.

 

 

Yanzu haka an girke jami,an tsaro a harabar sakateriyar Audu Bako inda kuma daga yanzu zuwa kowane lokaci kotun zata fara sauraron korafin kamar yadda wakilinmu Yusuf Nadabo Ismail ya rawaito

Continue Reading

Labarai

Ku tallafawa mazauna gidajen gyaran halin dan rage musu raɗaɗin rayuwa – Mallam Ibrahim Bunkure

Published

on

Limamin masallacin Salafussaleh dake unguwar Ɗorayi ƙarama a jihar Kano, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya shawarci al’umma da su ƙara dagewa wajen tallafawa mazauna gidajen ajiya da gyaran hali, da masu buƙata ta musamman, domin rage musu wani raɗaɗin rayuwa na yau da kullum.

Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya bayyana hakan ne yayin da suka tallafawa mazauna gidan gyaran hali na Goron Dutse, da kayayyakin Abinci, da kuma na gidan yara, a wani ɓangare na taya su bikin ƙaramar Sallah, wajen ganin sun samu farin ciki a bukukuwan ƙaramar sallar da aka gudanar.

Ya ce matuƙar masu hali za su rinƙa tallafawa mazauna gidan gyaran halin da abubuwan da suka sawwaƙa, babu makawa za’a rage musu wata damuwa ta yau da kullum.

Wakilinmu Yakubu Ibrahim Dogarai ya rawaito cewa, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya ce daga cikin kayan abincin da suka kai wa mazauna gidajen akwai Tuwon Sallah, da garin Kwakwaki, da kuma sinadarin Ɗanɗano, da Sukari, domin ragewa mazaunan gidajen wani raɗaɗin rayuwa.

Continue Reading

Trending