Connect with us

Labarai

Kudin addu’a: Muhyi ya sake magantuwa

Published

on

Hukumar karbar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano karkashin jagorancin Barista Muhyi Magaji Rimin Gado ya gabatar da wani zama da ‘yan jaridu domin karin bayani a kan fitaccen dan siyasa a jihar Kano Ali Baba da a ke zargi da hannu wajen zabtarewa malamai kudin addu’a.

Tun a makon da ya gabata ne dai a ka yi zargin Ali Baba da dan sa sun zabtarewa malama dari uku da hamsin da gwamna ya dauka domin gudanar da addu’a.

Barista Muhyi Magaji ya gudanar da zaman ne a ofishin hukumar a ranar Alhamis.

Ya ce, “Wannan abun ya dauki sabon salon a siyasa, amma mu dai a matsayin mu na hukumar da bata da alaka da siyasa, mun yi kokarin jan layi, mu na yin abun tsakani da Allah, dai-dai gwargwadon ikon mu, kuma abisa tanadin doka, a yadda a ka kawo mana korafi mun bincika mun ga ba kamar yadda duk malamai su ka zo suna cewa an kwashe kudaden su ba. Abunda ya faru akwai form guda goma da aka baiwa Ali Baba, ya rabawa mutane goma, cikin su mutum hudu sun zo sun ce ba su bayar ba, amma mutum shida an tirsasu sun bayar”.

Ya kuma ce, “Mun karbi kudaden, domin mutanen su na da bukatar kudin, akwai wanda na bashi kudin har kakkarwa ya ke yi, kuma mun dauki matakin ne domin zai taimaka mana, wanda ya ji idan yana jin tsoro ya fito ya gaya mana wani ya daukar masa kudi. Mun fadada bincike sauran wurarae na bangaren addini da suma a ka ce an basu kudade”.

Ya kara da cewa, “Wadanda su ka zo dukkanin su ‘yan Fagge ne wasu bada kan su su ka zo ba, amma tunda dokar nan ta gwamnati ce, mun yi buncike mun gano masu laifi an kuma mayar masu da kudaden su. Na dauka kudin mutane dari uku da hamsin ne a ka tafi da su, amma ba duka a ka taba kudin ba”. Inji Muhyi Magaji

Wakilin mu Abba Isah Muhammad ya rawaito cewar, Barista Muhyi Magaji ya kuma ce, kotu ce mai iya cewa Ali Baba ya yi laifi ko dan sa ya yi laifi ba, babu zancen su bi son ran wasu al’ummar.

 

Labarai

Ƴan kasuwa ku tsaftace magudanan ruwa bisa gabatowar Damuna – Ƙungiyar Amata ta kasuwar Singa

Published

on

An buƙaci ƴan kasuwa da su rinƙa tsaftace tare da gyara magudanan ruwa a cikin kasuwannin su, bisa yadda damuna ke ƙara gabatowa.

Shugaban ƙungiyar Amata reshen kasuwar Singa Alhaji Musa Ibrahim Ɗan gaske, ne ya bukacin hakan a zantawar sa da manema labarai, yayin kaddamar da tsaftace kasuwar da kuma gyara mugudanun ruwan kasuwar.

Alhaji Musa, ya kuma ce ta hanyar tsaftace magudanan ruwan ne za a gujewa kowacce irin ambaliyar ruwa a cikin kasuwanni.

Continue Reading

Hangen Dala

Yau za’a fara Shari’ar Ganduje da gwamnatin Kano

Published

on

A yau ne babbar kotun jaha mai lamba 4 zata fara sauraron wata sharia wadda gwamnatin kano ta ahigar.

 

Gwamnatin jahar kano dai ta shigar da karar tsohon gwamnan jahar kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da mai dakinsa Hafsat Umar Ganduje da kuma dansu Umar Abdullahi Ganduje da kuma wani kamfani mai suna Lamash da kuma Dr Jibrilla Muhammad.

 

Gwamnatin jahar kano dai tana zargin Ganduje da wadanna mutane da laifin hada baki da barnatar da dukiyoyin gwamnati.

 

 

Cikin zarge-zargen da ake yiwa su Ganduje akwai batun sun sayar da wasu filotai ba bisa ka’ida ba.

 

 

Da kuma batun zargin da akewa Ganduje na badakalar karbar dala tun a shekarar 2019.

 

 

Yanzu haka an girke jami,an tsaro a harabar sakateriyar Audu Bako inda kuma daga yanzu zuwa kowane lokaci kotun zata fara sauraron korafin kamar yadda wakilinmu Yusuf Nadabo Ismail ya rawaito

Continue Reading

Labarai

Ku tallafawa mazauna gidajen gyaran halin dan rage musu raɗaɗin rayuwa – Mallam Ibrahim Bunkure

Published

on

Limamin masallacin Salafussaleh dake unguwar Ɗorayi ƙarama a jihar Kano, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya shawarci al’umma da su ƙara dagewa wajen tallafawa mazauna gidajen ajiya da gyaran hali, da masu buƙata ta musamman, domin rage musu wani raɗaɗin rayuwa na yau da kullum.

Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya bayyana hakan ne yayin da suka tallafawa mazauna gidan gyaran hali na Goron Dutse, da kayayyakin Abinci, da kuma na gidan yara, a wani ɓangare na taya su bikin ƙaramar Sallah, wajen ganin sun samu farin ciki a bukukuwan ƙaramar sallar da aka gudanar.

Ya ce matuƙar masu hali za su rinƙa tallafawa mazauna gidan gyaran halin da abubuwan da suka sawwaƙa, babu makawa za’a rage musu wata damuwa ta yau da kullum.

Wakilinmu Yakubu Ibrahim Dogarai ya rawaito cewa, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya ce daga cikin kayan abincin da suka kai wa mazauna gidajen akwai Tuwon Sallah, da garin Kwakwaki, da kuma sinadarin Ɗanɗano, da Sukari, domin ragewa mazaunan gidajen wani raɗaɗin rayuwa.

Continue Reading

Trending