Connect with us

Wasanni

Barcelona: Mako mai kamawa kowa zai san matsayin sa – Shugaban Kungiyar

Published

on

shugaban kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, Josep Maria Bartomeu ya ce a mako mai kamawa ne kowa zai san makomar sa a kungiyar kwallon kafa Barcelona.

Wannan batun cikin bacin rai na shugaban kungiyar na zuwa ne lokacin da Bayern Munich ta kasar Jamus ta yi wa kungiyar tonan silili a tarihin kungiyar da kuma nahiyar turai da ci 8-2 a wasan daf da na kusa da na karshe a birnin Lisbon na kasar Portugal a daren Juma’a.

Ys ce”Mako mai kamawa kowa zai san makomar sa, tun daga kan masu horaswa da manyan ma’aikatan kungiyar da kuma ‘yan wasan mu”. Shugaban kungiyar Josep.

A daren jiya bayan kammala wasan kyaftin din kungiyar Gerard Pique ya bayyana cewa”Babu wanda zai tsira a cikin mu, domin kuwa wannan bas hi ne na farko ba, bas hi ne na biyu ba, kuma bas hi ne na uku ba, mu na tsaka mai wuya na san za a yi wani abu a kai, saboda duk mun gaji mu na bukatar ‘yan wasa masu jinni a jika”. Inji Pique.

Bayern Munich ta zama kungiya ta farko a gasar Champions League da ta zura kwallaye a wasan daf da na kusa da na karshe a nahiyar turai, tun bayan da Real Madrid ta lallasa FC Wacker Innsbruck da ci 9-1 a shekarar 1990-91.

Bacerlona ba ta taba dibar kwallaye 8 a raga ba a gasar, tun bayan da Sevilla ta lallasa ta da ci 8-0 a gasar Spanish Cup a shekarar 1946.

Haka zalika, Bayern Munich ta lashe wasanni 19 ba tare da ta yi rashin nasara ba, sannan ta kuma kafa tarihi a kungiyoyin kasar Jamus.

Yanzu haka Bayern Munich na jiran Manchester City ko kuma Lyon a wasan kusa da na karshe na gasar, wanda za a fafata a ranar Laraba mai zuwa.

 

Wasanni

Bayer Leverkusen ta zama zakarar gasar Bundesliga ta 2023/2024.

Published

on

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Bayer Leverkusen ta zama zakarar gasar Bundesliga ta shekarar 2023/2024, bayan da suka samu nasara a kan Weder Bremen da ci 5-0.

Hakan ne kuma ya kawo ƙarshen shekaru 11 da Bayern Munich, da ta yi tana lashe gasar.

Wannan dai shi ne karo na farko da Bayer Leverkusen suka taɓa lashe gasar a tarihi, ida suka gaza ɗaukar kofin a shekarar 2002 a ranar ƙarshe ta gasar.

Har ila yau, a dai wannan shekarar ne su kayi rashin nasara hannun Shalke 04, a wasan ƙarshe na German Cup Da ci 4-2.

Haka kuma, Real Madrid suka doke su a wasan ƙarshe na zakarun nahiyar turai.

Rahotanni sun bayyana cewa ƙungiyar bata taɓa ɗaukar wata gasa ba a ƙarni na 21, sai bayan da Xavi Alonso ya karɓe su.

Continue Reading

Wasanni

Hukumar NPFL, ta amince da buƙatar Kano Pillars na ɗage wasan ta na mako na 28 da Enyimba

Published

on

Yanzu haka an samu dai-daito da hukumar NPFL, wanda ta amince da bukatar Kano Pillars na dage wasanta na mako na 28, da Enyimba zuwa ranar Alhamis, mai zuwa.

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars, ce ta wallafa hakan a shafin ta na Facebook da yammacin Litinin ɗin nan, ta ce ƴan wasan ta za su tashi a gobe Talata, da safe zuwa Aba domin fafata wasannin su.

Idan dai ba’a manta ba ƙungiyar ta wallafa kaɗan daga irin ƙalubalen da take fuskanta a harkokin gudanarwar ta.

Pillars, ta wallafa ƙalubalen ne kamar haka, “A yanzu haka zancan da muke muku Kano Pillars ta rasa kudin da za taje garin Aba, domin buga wasan hamayya na Nigeria Premier league wato Zobia Classic”.

Wasan dai shine wasa mafi ɗaukar hankali a league din Nigeria baki ɗaya, ku taya mu yadawa dan Allah.

Continue Reading

Wasanni

Glesner ya zama sabon mai horas da Palace.

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Crystal Palace ta sanar da nadin Oliver Glesner a matsayin sabon mai horaswar ta.

Glesner wanda tsohon mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Eintracht Frankfurt ne mai shekaru 49 dan asalin kasar Austrian, ya maye gurbin tsohon mai horaswa Roy Hodson, wanda ake ganin ya gaza kai kungiyar ga tudun mun tsira.

A wasanni 16 da Crystal Palace ta buga a bayan nan ta yi rashin nasara a wasanni 10 duk karkashin jagorancin Roy Hodson wanda hakan yasa take mataki na 16 a teburin gasar firimiyar kasar Ingila.

Glesner dai ya rattaba kwantaragi da Palace har na tsawon shekaru biyu, zai kuma jagoranci kungiyar a wasan sa na farko da kungiyar kwallon kafa ta Burnley a ranar Asabar mai kamawa.

Continue Reading

Trending