Connect with us

Labarai

Matasan da su ka farwa sha’iri da sara sun shiga hannu

Published

on

Matasan da su ka farwa wani shari’i saboda daukar fansa a unguwar Bachirawa Madugu tuni suna hannun jami’an ‘yan sanda domin gudanar da bincike.

Sakataren kungiyar hadin kai al’ummar Bachirawa, Kwamared Mukhtar Ya’u Bachirawa ne ya bayyana hakan a zantawarsa da gidan rediyon Dala.

Tun abaya ne dai fusatattun matasan su ka farma shari’in da sara saboda zargin dan uwan sa ya halaka abokin sa, wanda tuni dan uwan na sa ya na gidan yari.

Ya ce, “An samu ci gaba sosai, tun abubuwan da su ka faru akwai kwamiti da a ka kafa karkashin jagorancin mai garin Bachirawa, domin magance abubuwan da ke faruwa kuma an samu hadin kai a tsakanin ‘yan sintiri da kuma ‘yan sanda, an je an yi bincike an kamo mutane 12 da su ke hannu a na tuhumar su, domin gano gaskiyar wadanda su ka aikata wannan al’amari”.

Ya kuma ce,“Mutane su na zuwa wannan unguwa bata gari, saboda haka mu na da tsarin da duk wanda zai zauna sai an san waye shi, kuma daga ina ya taso, domin dakile harkar shaye-shaye da kuma laifuka a unguwar”. Inji Kwamared Mukhtar Bachirawa

Wakilin mu Yusuf Nadabo Isma’il ya rawaito cewar, Kwamared ya kara cewa, yanzu haka suna kokarin ganin an yi adalci a kan matasan duk mai laifi an hukunta shi.

Labarai

Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Laraba a matsayin ranar hutu

Published

on

Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Laraba, 1 ga watan Mayun 2024, a matsayin ranar hutu, domin bikin ranar ma’aikata na wannan shekara.

Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayyana hakan, a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Talata.

Olubunmi, ya kuma sake nanata buƙatar ganin ma’aikata sun jajirce da yin aiki yadda ya kamata a dukkanib matakai daban-daban.

Continue Reading

Labarai

Wahalar Fetur ta haifar mana da koma baya a sana’ar mu – Mai Motar Haya

Published

on

Wani mai sana’ar tuƙin motar Haya, da kuma lodin fasinjoji mai suna Kabiru Muhammad, mazaunin ƙaramar hukumar Munjibir, ya ce ƙarancin motocin Haya da ake samu a yanzu, yana da alaƙa da wahalar man Fetur da ake fuskanta a sassan Najeriya.

A zantawar mutumin da wakilinmu Yusuf Nadabo Isma’il, ta cikin shirin rahotanni daga ƴan Zazu na yau Talata, ya ce a baya har motoci hamsin suke yiwa lodin fasinjoji su tashi, amma a yanzu Mota ɗaya suke iya cikawa sakamakon ƙarancin Fetur da ake fama da shi.

Ya kuma ce ƙaranci tare da tsadar man fetur ɗin da ake fama da shi, sun haddasa musu koma baya a sana’ar su, baya ga batun kuma matsalar da suke fuskanta da fasinjoji wajen biyan kuɗin Mota.

Wakiliyarmu da ta bibiyi shirin na ƴan Zazu Ummi Bala Ahmad ta rawaito cewa, matuƙin motar Kabiru Muhammad, ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jahohi, da su yi abinda ya kamata dan ganin farashin man Fetur ɗin ya sauka, domin al’umma su samun sauƙi.

Continue Reading

Labarai

Dilolin Wiwi sun yanki mai unguwa da Wuƙa, tare da cizon shi a hannu, kan ya shana su sha da siyar da wiwi a Kano

Published

on

Wasu matasa da ake zargin ƴan Daba ne, kuma dilolin Wiwi, sun kai wa mai unguwar yankin Bachirawar Tukwane ƙarshen kwalta hari da muggan makamai.

Tun farko dai mai unguwar yankin Malam Mustapha ya shawarci matasan ne, da su dai na ɗaurin tabar Wiwi, da siyar wa a kofar gidajen mutane lamarin da ya tunzura matasan.

Matasan dai sun rutsa mai unguwar Bachirawar ne inda suka yi yunƙurin hallaka shi, bayan da suka yanke shi da Wuƙa, tare da cizon sa a Hannu, sai dai ‘yan ƙungiyar bijilante na yankin sun kawo masa ɗauki inda suka kama wani matashi mai laƙabin Kokuwa.

A lokacin ne kuma mutanen yankin suka yi yunƙurin ɗaukar doka a hannu, sai dai mai unguwar Bachirawa Malam Mustapha dan Bachirawa Gabas Malam Abdulkadir Dandiyo, sun kuɓutar da matashin inda aka mika shi ofishin ƴan sanda, ragowar matasan suka tsere.

Shugaban kungiyar ci gaban al’ummar yankin Dakta Jibrin Sagir, ya ce a shirye suke su tinkari duk wani ɓata gari a yankin da yake addabar su.

Continue Reading

Trending