Connect with us

Wasanni

Na kagu a fara sabuwar kakar Firimiya – Klopp

Published

on

Mai horas da Liverpool, Jurgen Klopp, ya ce ya na sa ran kungiyar za ta yi sauri wajen ganin wasannin sada zumuncin da za ta yi ya bi jikin su, domin tunkarar sabuwar kakar gasar Firimiya.

Liverpool za ta yi wasan sada zumunci har guda biyu a nan gaba ciki akwai fafatawar ta da kungiyar Stuttgart ta kasar Jamus kuma tsohuwar kungiyar sa tun ya na karami, sai kuma kungiyar Salzburg ta kasar Austria wadda ta lashe gasar a bana.

Wasan dai za a yi shi ne a Austria ranar Asabar, sannan kuma a ranar 29 ga wannan watan na Agusta, Liverpool za ta barje gumi da Arsenal a kofin Community Shield.

Ya ce“Yan a da matukar amfani wannan dan hutun da mu ka samu, domin mu kara fuskantar junan mu, atisayaen da mu ke yi mu na jin dadi sosai, domin abun da mu ke bukata Kenan, saboda ‘yan wasana ba su gajiya ba kuma ba su sare ba, yanzu haka mu na tsakiyar shirye-shiryen mu, kuma ko yanzu a k ace mun shirya”. A cewar Klopp.

A daren gobe Alhamis ne a ke sa ran fitar da sabuwar jaddawalin kakar ta bana wanda za a fara ta a ranar 12 ga watan Satumba.

Wasanni

Bayer Leverkusen ta zama zakarar gasar Bundesliga ta 2023/2024.

Published

on

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Bayer Leverkusen ta zama zakarar gasar Bundesliga ta shekarar 2023/2024, bayan da suka samu nasara a kan Weder Bremen da ci 5-0.

Hakan ne kuma ya kawo ƙarshen shekaru 11 da Bayern Munich, da ta yi tana lashe gasar.

Wannan dai shi ne karo na farko da Bayer Leverkusen suka taɓa lashe gasar a tarihi, ida suka gaza ɗaukar kofin a shekarar 2002 a ranar ƙarshe ta gasar.

Har ila yau, a dai wannan shekarar ne su kayi rashin nasara hannun Shalke 04, a wasan ƙarshe na German Cup Da ci 4-2.

Haka kuma, Real Madrid suka doke su a wasan ƙarshe na zakarun nahiyar turai.

Rahotanni sun bayyana cewa ƙungiyar bata taɓa ɗaukar wata gasa ba a ƙarni na 21, sai bayan da Xavi Alonso ya karɓe su.

Continue Reading

Wasanni

Hukumar NPFL, ta amince da buƙatar Kano Pillars na ɗage wasan ta na mako na 28 da Enyimba

Published

on

Yanzu haka an samu dai-daito da hukumar NPFL, wanda ta amince da bukatar Kano Pillars na dage wasanta na mako na 28, da Enyimba zuwa ranar Alhamis, mai zuwa.

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars, ce ta wallafa hakan a shafin ta na Facebook da yammacin Litinin ɗin nan, ta ce ƴan wasan ta za su tashi a gobe Talata, da safe zuwa Aba domin fafata wasannin su.

Idan dai ba’a manta ba ƙungiyar ta wallafa kaɗan daga irin ƙalubalen da take fuskanta a harkokin gudanarwar ta.

Pillars, ta wallafa ƙalubalen ne kamar haka, “A yanzu haka zancan da muke muku Kano Pillars ta rasa kudin da za taje garin Aba, domin buga wasan hamayya na Nigeria Premier league wato Zobia Classic”.

Wasan dai shine wasa mafi ɗaukar hankali a league din Nigeria baki ɗaya, ku taya mu yadawa dan Allah.

Continue Reading

Wasanni

Glesner ya zama sabon mai horas da Palace.

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Crystal Palace ta sanar da nadin Oliver Glesner a matsayin sabon mai horaswar ta.

Glesner wanda tsohon mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Eintracht Frankfurt ne mai shekaru 49 dan asalin kasar Austrian, ya maye gurbin tsohon mai horaswa Roy Hodson, wanda ake ganin ya gaza kai kungiyar ga tudun mun tsira.

A wasanni 16 da Crystal Palace ta buga a bayan nan ta yi rashin nasara a wasanni 10 duk karkashin jagorancin Roy Hodson wanda hakan yasa take mataki na 16 a teburin gasar firimiyar kasar Ingila.

Glesner dai ya rattaba kwantaragi da Palace har na tsawon shekaru biyu, zai kuma jagoranci kungiyar a wasan sa na farko da kungiyar kwallon kafa ta Burnley a ranar Asabar mai kamawa.

Continue Reading

Trending