Connect with us

Labarai

Wasu motoci 3 sun yi hadari a Kofar Kabuga

Published

on

Wani hadarin motoci guda a kofar Kabuga kan hanyar zuwa Jami’ar Yusuf Maitama Sule, ya janyo jikkatar al’umma.

Al’amarin ya faru a ranar Litinin, inda wata karamar mota kirar Toyota Corolla tare da wani kan DAF da baya dauke da bodi, suka doki juna har takai da ita Toyotar kifa saka makamakon dukan da kan DAF din.

Wasu da abun ya faru a kan idon su sun yi wa Wakilin mu Hassan Auwalu Muhammad karin haske.

“Na ga abun da ya faru, mot ace ta kwace ta daki wacce ta ke tafiya, inda wani mai motar yayi masa overtaking, burki ya kwace masa”. A cewar shaidar gani da ido

Shima mai karamar motar ta Corrolla, mai suna Malam Naziru Uba Muhammad, wanda da kyar a ka zaro shi daga cikin motar, sakamakon kifawar da ta yi, ya bayyana mana yadda abun ya faru.

“Ina tafiya a kan titi, sai mai babbar motar ya zo ya yi min dukan gefe, yazo zai yi min overtaking, ya na duka na motar ta kifa, daya motar tana gefe itama ya je ya dake ta.” Inji Malam Naziru

Nayi kokarin jin ta bakin direbobin DAF din, amman sunki yarda na dauki muryar su, to amman wani da yake cikin daya daga motocin DAF din mai suna Anas Ali ya ce, “Mu na cikin tafiya sai ji mu ka yi an dake mu, kuma ba kowa a gaban mu”. A cewar Anas Ali

Labarai

Zaman lafiya: Majalisar dinkin duniya ta taka rawa – Farfesa Kamilu Fagge

Published

on

Masanin kimiyar siyasa a jami’ar Bayero da ke jihar Kano Farfesa Kamilu Sani Fagge, ya ce majalisar dinkin duniya, ta taka rawa wajen samar da zaman lafiya a duniya.

Farfesa Kamilu Sani Fagge ya bayyana hakan yayin zantawa da wakiliyar mu Aisha Aminu Kundila a wani bangare na bikin ranar tunawa da majalisar dinkin duniya a wannan shekarar.

Ya ce, “Nijeriya ta zama mamba ce a majalisar ta dinkin duniya a 1960 a matsayin mamba ta 99”. Inji Farfesa Kamilu Sani Fagge.

Continue Reading

Labarai

Polio: Za mu dakile bullar cutar shan inna a Kano – Gwamnatin Kano

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta ce za ta ci gaba da sanya idanu, domin ganin ba a sake samun bullar cutar shan inna ba ta Polio a fadin jihar Kano.

Kwamishinan lafiya na jihar, Dakta Aminu Ibrahim Tsanyawa ne ya bayyana hakan a yayin zantawar sa da manema labarai a wani bangaren na bikin ranar yaki da cutar shan inna ta duniya da ake gudanarwa a yau.

Ya ce, “Za mu ci gaba da gudanar da rigakafin cutar Polio a fadin jihar Kano, duk da cewa babu cutar a jihar wanda hakan zai bai wa yara kariya daga kamuwa da cutar a nan gaba”. A cewar Dakta Aminu Ibrahim Tsanyawa.

Sai dai ya bukaci iyaye da su ci gaba da kai yaran su, domin karbar rigakafin wanda hakan ne kadai zai taimaka wajen yaki da cutar ko da a nan gaba.

 

Continue Reading

Labarai

‘Yan sandan SARS 16 za su fuskanci hukunci sakamon zargin kisan kai

Published

on

Kwamitin shugaban kasa da ke bincike kan ayyukan ‘yan sanda ya ba da shawarar hukunta ‘yan sandan SARS 16 sakamakon zarginsu da kisan kai a jihohin kasar nan 12 har da birnin tarayya Abuja.

Rahotanni sun ce tun a watan Yunin shekarar da ta gabata ne kwamitin ya yi bincike kan mutanen, inda sai akwanan ne ya mikawa shugaban kasa rahoton.

Sauran wadanda aka mikawa rahoton sun hada da sufeto Janar na ‘yan sandan Muhammed Adamu da hukumar kula da ayyukan ‘yan sanda ta kasa da kuma attorney Janar na tarayya.

Jihohin da ‘yan sandan na SARS suka gudanar da ta’asar sun hada da: Akwa Ibom, Benue, Delta, Enugu, Lagos da Ogun, Rivers, Gombe, Kaduna da Kogi da kuma Kwara.

 

 

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!