Labarai
Kungiyar Hausawan Afrika ta karrama Freedom Radio da Dala FM

Sarkin al’ummar Hausawa na Afrika Alhaji Abdulkadir Labaran Koguna wanda ya ce, sun karrama Freedom Radiyo da Dala FM saboda gudunmawar da tashoshin su ka bayar a ranar bikin Hausan ta duniya.
Alhaji Abdulkadir Labaran Koguna ya bayyana hakan ne lokacin da Kungiyar al’ummar Hausawan ke karrama tashoshin Freedom Radiyo da Dala bisa yadda suke bayar da gudunmawa wajen ci gaban al’ummar Hausa dama sauran yarika.
A nasa bangaren, Manajan tashar Freedom Malam Ado Sa’idu Warawa ya bayyana jin dadin sa a kan karramawar.
Ya na mai cewa, “Tashar Freedom Radiyo za ta ci gaba da yada shirye shiryen da za su kara kawo ci gaban harshen Hausa da al’ummar Hausawa Koda, kuma koda a cikin shirye shiryen tashar muna kokarin ganin mun yi amfani da ingantatciyar Hausa kuma za mu ci gaba da tafiya a kan haka”. Inji Malam Ado Sa’idu Warawa
Haka zalika, itama Manajan shire-shirye ta tashar Dala Hajiya Asma’u Sadik Baby Nice ta mika godiya bisa karramawar da a ka yiwa tashoshin tare da tabbatar da cewar, suna maraba da gyara da zarar sun yi wani abu ba dai-dai ba.
Dakta Abdulkadir Labaran Koguna ya kuma kara mika godiya bisa yadda tasoshin Freedom Radiyo da Dala ke gudanar da yawancin shirye shiryen su da Hausa.

Labarai
Ba mu san Hamisu Breaker ya saki waƙar Amanata ba – Hukumar tace fina-finai

Hukumar tace Fina-finai da Ɗab’i ta jihar Kano ta ce yanzu haka tana kan bincike don gano yadda akai mawakin nan Hamisu Breaker, ya saki sabuwar wakarsa mai suna “Amanata” ba tare da an tantance ta ba.
Mai magana da yawun hukumar Abdullahi Sani Sulaiman, shi ne ya bayyana hakan a wani sakon murya da ya aikowa Dala FM Kano, a ranar Alhamis 24 ga watan Afrilun 2025.
Ya kuma ce aikin dakatar da wakar ba na hukumar Hisbah ba ne na hukumar tace fina-finai ne, amma ba laifi ba ne kasancewar duk hukumomi ne na Gwamnati, a don haka idan hukumar ta Hisbah ta magantu akai babu laifi, domin dama suna aiki kafaɗa da kafaɗa.
A game da wakar ta Hamisu Beraker, mai suna “Amanata”, Abdullahi Sani, ya ce su har yanzu ba su san ta ina wakar ta fita ba tare da an tantance ta ba, amma tuni shugaban hukumar Abba Al-mustapha ya bada umarnin gudanar da bincike akan ta.
Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ce dai ta hannun mataimakiyar babban kwamandan ta a ɓangaren mata Dakta Khadijah Sagir Sulaiman, ta yi Allah wa-dai da wakar Hausar mai taken “Amana ta” da mawaki Hamisu Breaker ya rera, inda ta shawarci matasa da su guji sauraren wakar, bisa yadda take ɗauke da abubuwan da ke ƙarfafa aikata alfasha, da kuma amfani da kalmomin batsa a cikin bidiyon ta.

Hangen Dala
Rashin wuta: Muna cikin mawuyacin hali – al’ummar Kano, Katsina da Jigawa

Al’ummar jihohin Kano, katsina da Jigawa na fuskantar yanayi mara dadi, Sakamakon karancin samun wutar lantarki daga hukumar KEDCO.
Al’ummar jihohin sun ce iya sa’o’i uku kacal suke samun wutar, wanda hakan ke haifar musu da nakasu a harkokin kasuwancin su.
Wani bincike da jaridar Daily Trust tayi ta ambato yadda masu kananan masana’antu irin su Walda, Cajin Waya, Kankara da masu sana’ar dinki da dai sauran kananan sana’o’i dake amfani da wutar lantarki sun shiga mawuyacin hali.
Kazalika rashin wutar ya shafi hatta bangaren ruwan sha, dama masu sana’ar sayar da Ruwa a irin yankunan Hotoro da sauran irin wuraren dake sayen ruwa, Inda yanzu haka ruwan yayi tashin gwauron zabi a kowace jarka.
Koda dai ana ta bangaren hukumar rarraba hasken wutar lantarkin me kula da shiyyar Kano, Katsina da Jigawa KEDCO sun nemi afuwar al’umma.
Idan za’a tuna dai a makon jiya ne Ministan Wutar lantarki yace ‘yan Nigeria Miliyan 150 na samun wadatacciyar wutar lantarki.
Sai dai kuma a jihohi irin su Kano, Katsina da Jigawa na bayyana damuwa kan karancin Wutar, Inda suka ce bata wuce ta sa’o’i uku suke samu a kowa ce rana.

Hangen Dala
Rashin wuta:- Muna cikin mawuyacin hali – al’ummar Kano, Katsina da Jigawa

-
Nishadi5 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Labarai5 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi6 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Manyan Labarai5 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai5 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya3 years ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Manyan Labarai5 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano
-
Nishadi6 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su