Connect with us

Labarai

Zan yi aiki tare da kungiyar tallafawa al’ummar Bichi – Dandarman Bichi

Published

on

Hakimin Bichi kuma Dandarman Bichi, Alhaji Abdulhamid Ado Bayero, ya ce zai yi aiki kafada da kafada da kungiyar Fitilar jama’ar Bichi, domin ganin an samarwa da al’umma mafita na samun ci gaban su.

Alhaji Abdulhamid Ado Bayero, wanda ya tabbatar da hakan a yayin da ya karbi tawagar kungiyar ci gaban al’ummar Bichi wato Fitilar jama’ar Bichi a gidan sa da ke Bichi.

Cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar, Alhaji Lirwanu Idris Malikawa Garu kuma dagacin Malikawa Garu ya sanyawa hannu, ta ce Dandarman Bichi, ya kuma ce,”Ina yaba mu ku, kuma wannan kungiyar ta ku ta yi ma’ana sakamakon irin ayyukan da ta ke yin a hidimtawa al’umma, na yi alkawarin yin aiki da ku kafada da kafada, sannan ku yi amfani da manufofin ku domin cimma burin da ku ka saka a gaba”. Inji Alhaji Abdulhamid Ado Bayero.

Da ya ke na sa jawabin shugaban kungiyar ya ce,“Mun ziyar ce ka ne saboda mu saka ka a cikin ayyukan da mu ka kuduri niyar cimma”. A cewar Lirwanu Idris Malikawa Garu.

Shugaban kungiyar ci gaban al’ummar Bichi, Alhaji Rilwanu Idris Malikawa Garu, ya kuma ce kungiyar su za ta yi amfani da mutanen da su ke da karfi, domin ganin sun tallafawa al’ummar yankin 122, da su ke fama da matsalar Idanu wajen ganin an yi mu su aikin Idanu a asibiti. Sannan kuma kungiyar ta su za ta wayar da Limamai da ma su unguwanni a kan illar shaye-shaye da matsalolin auratayya da ke damun al’umma.

 

Labarai

Gwamnatin Kano za ta inganta filaye da bunƙasa duk ɓangarorin wasannin matasa – Kwamishinan Matasa da Wasanni

Published

on

Sabon kwamishinan ma’aikatar wasanni da ci gaban matasa na Jihar Kano Mustapha Rabi’u Musa kwankwaso, ya bada tabbacin cewar Gwamnatin Jihar za ta ɗauki matakin inganta filayen tare da bunƙasa duk wasu ɓangarorin wasanni da matasa ke yi.

Mustapha Rabi’u Musa Kwankwaso, ya bayyana hakan ne yayin da ya kama aiki yau Asabar, tare da kai ziyara a wasu filayen wasannin dake ihar Kano.

Daga cikin filayen wasannin da ya ziyarta akwai filin wasa na Sani Abacha da ke ƙofar Mata, da filin wasa na Kano Pillars da ke sabon Gari, da kuma filin wasa na Ado Bayero Square dake unguwar Sabon Gari, sai kuma filin wasa na Mahaha da ke ƙofar Na’isa.

Da yake jawabi bayan kammala ziyarar kwamishinan wasannin da ci gaban Matasa na jihar Kano, Mustapha Rabi’u Musa kwankwaso, ya ce ya gudanar da ziyarar ce domin sanin halin da filayen wasannin ke ciki.

A lokacin ziyarar kwamishinan na tare da mai bai wa Gwamnan Kano shawara a kan harkokin wasanni Ambasada Yusuf Imam Ogan Ɓoye, da shugaban magoya bayan ƙungiyar ƙwallon Ƙafa ta Kano Pillars Alhaji Rabi’u Abdullahi Kawo, da kuma mai riƙon Shugabancin hukumar wasanni ta jiha Malam Bala Sani Shehu.

Continue Reading

Labarai

Muna sane da ƙarancin Ruwa a wasu sassan Kano – Hukumar rarraba ruwan Sha

Published

on

Hukumar rarraba ruwan sha ta jihar Kano ta ce matsalar rashin samun ruwa da ake fuskanta a wasu sassan jihar Kano, yana da alaƙa ne da lalacewar wani abun kan Famfo a madatsar ruwan da ke Tamburawa.

Shugaban hukumar Injiniya Garba Ahmad Bichi, ne ya bayyana haka yayin zantawar sa da manema labarai, ya ce cikin guraren da za’a yiwa gyaran har da madatsar ruwa ta Challawa da Watari, da amincewar gwamnatin jihar Kano.

Injiniya Garba, ya kuma ce suna sane da ƙarancin ruwan da ake fuskan ta a wasu sassan jihar Kano, amma nan gaba kaɗan za kammala gyaran kan famfon, domin ganin an wadata sassan jihar Kano, da ruwan domin ganin sun samu wani sauƙi.

 “Mu ma a ɓangaren mu Bama jin daɗin yadda al’umma suke rasa ruwa a sassan jihar Kano, kuma nan da ranar Litinin mutane za su fita daga cikin wannan matsala ta rashin Ruwa, a yanku nan su, “in ji shi”

Garba Ahmad, ya kuma ƙara da cewa matsalar fashewar Fayif da aka samu a ci gaba da aikin gadar mahaɗar Ɗan Agundi, yanzu haka suna kan ɗaukar mataki tsakanin su da kamfanin da suka taka har ya fashe, dan ganin an gyara al’ummar da ake baiwa ruwa su ci gaba da damu.

Continue Reading

Labarai

Ƴan kasuwa ku tsaftace magudanan ruwa bisa gabatowar Damuna – Ƙungiyar Amata ta kasuwar Singa

Published

on

An buƙaci ƴan kasuwa da su rinƙa tsaftace tare da gyara magudanan ruwa a cikin kasuwannin su, bisa yadda damuna ke ƙara gabatowa.

Shugaban ƙungiyar Amata reshen kasuwar Singa Alhaji Musa Ibrahim Ɗan gaske, ne ya bukacin hakan a zantawar sa da manema labarai, yayin kaddamar da tsaftace kasuwar da kuma gyara mugudanun ruwan kasuwar.

Alhaji Musa, ya kuma ce ta hanyar tsaftace magudanan ruwan ne za a gujewa kowacce irin ambaliyar ruwa a cikin kasuwanni.

Continue Reading

Trending