Connect with us

Wasanni

Foden da Greenwood: ‘Yan wasan biyu sun bar sansanin Ingila

Published

on

Mai horas da kasar Ingila, Gareth Southgate, ya tabbatar da cewa ‘yan wasan Ingila biyu da a ka tabbatar da su sun kamu da cutar Covid-19, sun bar sansanin kasar ta Ingila.

‘Yan wasan Phil Foden da kuma Mason Greenwood, a ka tabbatar sun a dauke da cutar.

‘yan wasan wanda su ka karya ka’idar dokokin da a ka shimfida a kwallon kafa a kan cutar duka an same su da laifi, domin kuwa sun ma buga wasan da Ingila ta samu nasara a hannun Iceland da ci 1-0 a wasan cancantar shiga gasar cin kofin nahiyar Turai na kasa da kasa.

Foden dan wasan tsakiyar Manchester City mai shekaru 20, da kuma dan wasan gaban Manchester United Greenwood mai shekaru 18, wannan shi ne karo na farko da su ka fara bugawa kasar Ingila wasa.

Mai horas da kasar Ingila South Gate ya ce“Dukan ‘yan wasan biyu sun bayar da hakuri, amma kuma sun karya dokar Covid-19 da a ka shimfida, amma yanzu haka dolle su killace kan su, domin ba za su ci gaba da zama da mu ba, dole su koma gida, kuma mu inda mu ke baa bun da ya same mu”.

Ingila za ta fuskanci kasar Denmark a ci gaba da wasan cancantar shiga gasar cin kofin nahiyar Turai na kasa da kasa a daren ranar Talata.

Wasanni

Bayer Leverkusen ta zama zakarar gasar Bundesliga ta 2023/2024.

Published

on

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Bayer Leverkusen ta zama zakarar gasar Bundesliga ta shekarar 2023/2024, bayan da suka samu nasara a kan Weder Bremen da ci 5-0.

Hakan ne kuma ya kawo ƙarshen shekaru 11 da Bayern Munich, da ta yi tana lashe gasar.

Wannan dai shi ne karo na farko da Bayer Leverkusen suka taɓa lashe gasar a tarihi, ida suka gaza ɗaukar kofin a shekarar 2002 a ranar ƙarshe ta gasar.

Har ila yau, a dai wannan shekarar ne su kayi rashin nasara hannun Shalke 04, a wasan ƙarshe na German Cup Da ci 4-2.

Haka kuma, Real Madrid suka doke su a wasan ƙarshe na zakarun nahiyar turai.

Rahotanni sun bayyana cewa ƙungiyar bata taɓa ɗaukar wata gasa ba a ƙarni na 21, sai bayan da Xavi Alonso ya karɓe su.

Continue Reading

Wasanni

Hukumar NPFL, ta amince da buƙatar Kano Pillars na ɗage wasan ta na mako na 28 da Enyimba

Published

on

Yanzu haka an samu dai-daito da hukumar NPFL, wanda ta amince da bukatar Kano Pillars na dage wasanta na mako na 28, da Enyimba zuwa ranar Alhamis, mai zuwa.

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars, ce ta wallafa hakan a shafin ta na Facebook da yammacin Litinin ɗin nan, ta ce ƴan wasan ta za su tashi a gobe Talata, da safe zuwa Aba domin fafata wasannin su.

Idan dai ba’a manta ba ƙungiyar ta wallafa kaɗan daga irin ƙalubalen da take fuskanta a harkokin gudanarwar ta.

Pillars, ta wallafa ƙalubalen ne kamar haka, “A yanzu haka zancan da muke muku Kano Pillars ta rasa kudin da za taje garin Aba, domin buga wasan hamayya na Nigeria Premier league wato Zobia Classic”.

Wasan dai shine wasa mafi ɗaukar hankali a league din Nigeria baki ɗaya, ku taya mu yadawa dan Allah.

Continue Reading

Wasanni

Glesner ya zama sabon mai horas da Palace.

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Crystal Palace ta sanar da nadin Oliver Glesner a matsayin sabon mai horaswar ta.

Glesner wanda tsohon mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Eintracht Frankfurt ne mai shekaru 49 dan asalin kasar Austrian, ya maye gurbin tsohon mai horaswa Roy Hodson, wanda ake ganin ya gaza kai kungiyar ga tudun mun tsira.

A wasanni 16 da Crystal Palace ta buga a bayan nan ta yi rashin nasara a wasanni 10 duk karkashin jagorancin Roy Hodson wanda hakan yasa take mataki na 16 a teburin gasar firimiyar kasar Ingila.

Glesner dai ya rattaba kwantaragi da Palace har na tsawon shekaru biyu, zai kuma jagoranci kungiyar a wasan sa na farko da kungiyar kwallon kafa ta Burnley a ranar Asabar mai kamawa.

Continue Reading

Trending