Connect with us

Labarai

Rundunar ‘Yan sanda ta yi holin mutane 259 a Kano

Published

on

Rundunar Yansandan Jihar Kano ta yi holin mutane 259 da ta ke zargi da aikata laifuka daban-daban a ciki da wajen Jihar.

Kwamishinan ‘Yan sandan Kano Habu Ahmad Sani, ya bayyana hakan lokacin da yake ganawa da manema labarai a Shelkwatar rundunar dake Bomfai a ranar Laraba.

Habu Ahmad Sani, ya kuma kara da cewar, nasarorin da rundunar take samu nada alaka da hadin kai da jama’a su ke basu.

Wasu a cikin wadanda ake zargin sun bayyana yadda su ka shiga hannu dama irin laifukan da a ke zargin sun aikata da suka hadar da fashi da makami, safarar miyagun kwayoyi da Kuma damfara.

Wakilin mu Abba Isah Muhammad, ya ruwaito cewar, kwamishinan ‘Yan sandan na Kano Habu Ahmad Sani, ya nanata kudirin sa na tabbatar da tsaron rayuka da dukiyar Al’umma kamar yadda tsaron aikin su ya ke.

Labarai

Rahoto: Saurayi ya kai iyayen budurwar sa kotu kan zargin cinye masa kudade

Published

on

Wani matashi ya yi zargin iyayen budurwar sa sun karbi kudaden aure har da sadaki a hannun sa, bayan ya rage kwanaki uku a daura aure, iyayen budurwar su ka kawar da maganar auren kuma tsawon watanni ba zancen aure ko kuma dawo masa da kudaden da ya bayar.

Sai dai iyayen budurwar sun yi da’awar cewar, an je gwaji ne kafin aure saurayin ya gudu, inda shi kuma ya mayar da martanin cewar, a ranar da a ka je gwajin bai je da isassun kudi ba, shi yasa ya tafi, kuma washe gari ko da yaje gidan budurwar bijiro da zancen ta fasa auren, yanzu tsohon saurayin ta za ta aura, hakan ta sanya ya garzaya kotun shari’ar musulunci domin a bi masa hakkin sa.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Mai sayen filaye ya kai karar abokin cinikin sa kotu bayan shekaru 3

Published

on

Kotun shari’ar musulunci da ke zamanta a unguwar Goran dutse, karkashin mai shari’a Isma’il Garba Kofar Na’isa, wani mutum mai suna Ibrahim Ishaq, ya yi karar wani mai suna Ibrahim Abba, kan cinikin wani filaye da su ka yi shekaru uku da su ka gabata.

Ibrahim Abba ya bai wa Ibrahim Ishaq motoci guda biyu shi kuma ya bashi filaye guda tara, daga bisani takaddama ta barke a tsakanin su, Ibrahiim Ishaq ya na zargin an cuce shi a cinikin, hakan ya sanya shi garzaya wa kotu.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

 

 

Continue Reading

Labarai

Rahoto: NAFDAC ta kama magungunan dabbobi na jabu a Kano

Published

on

Hukumar lura da ingancin abincin da magunguna ta kasa reshen jihar Kano NAFDAC, ta kai sumame wani gida a karamar hukumar Bichi, ta ka kama  wani mutum Muhammad Jamilu Sani, wanda aka samu yana hada magungunan dabbobi da allurai da ta ke zargin na jabu ne.

Shugaban hukumar Malam Shaba Muhammad ne ya bayyana hakan a ranar Laraba yayin zantawar sa da gidan rediyon Dala.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!