Connect with us

Labarai

Rahoto: Hukumar bayar da agaji ta kai ziyara gidan da ya rushe a Kano

Published

on

Hukumar bayar da agajin gaggawa da tsugunar da gajiyyu ta jihar Kano ta kai ziyara gidan da gini ya danne wasu ‘yan mata biyu har su ka rasa ran su domin jajanta masu, a yankin Muskwani da ke karamar hukumar birnin Kano.

Shugaban Hukumar Dakta Sale Aliyu Jili ya jagoranci kai ziyarar a madadin gwamnan jihar Kano Dr. Abullahi Ganduje.

Domin jin cikakken shirin saurari wannan.

 

Labarai

Kano da Indiya Danjuma ne da Danjummai – Ganduje

Published

on

Gwamantin Kano ta ce za ta ci gaba da kyautata alakar ta da kasar Indiya.

Gwamnan Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje ne ya bayyana hakan a lokacin da ya ke karbar bakwancin karamin jakadan kasar Indiya a Nijerya.

Ya ce”Dama dai akwai kyakyawar alaka tsakanin kasar ta Indiya da Nijeriya, sannan gwamnati za ta ci gaba da amfani da kayayyakin aikin noma na kasar Indiyar, musamman ma yadda manoma ke jin dadin aiki da su”. Inji Ganduje.

Wakiliyar mu Zahrau Nasir ta rawaito cewa karamin jakadan kasar Indiya a Nijeriya, Abay Takur ya kuma ce ya kawo ziyarar ne da tawagar sa, domin kara inganta alaka da jihar Kano.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Babu zanga-zanga a musulunci domin neman wata bukata – Liman

Published

on

Limamin masallacin juma’a na Shelkwatar rundunar ‘yan sanda da ke Bompai SP Abdulkadir Haruna ya ce, rayuwar al’umma ba za ta inganta ba matukar babu zaman lafiya.

SP Abdulkadir Haruna, ya bayyana hakan a zantawar sa da wakilin mu Abba Isah Muhammad jim kadan bayan idar da sallar juma’a.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Mu guji yada karya a kafafen sada zumunta – Liman

Published

on

Babban limamin masallacin juma’a na Masjidul Kuba da ke unguwar Tukuntawa, Malam Ibrahim Abubakar Tofa ya ce, al’umma su guji yada karya a kafafen sadarwa na Internet wanda hakan kan janyo fitina a cikin al’umma.

Malam Ibrahim Abubakar Tofa, ya bayyana hakan a hudubar sa da ya gudanar a masallacin na Juma’a.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!