Connect with us

Labarai

Noman dabino zai iya samar da ayyukan yi ga matasa a Kano – Sarkin Pindiga

Published

on

Sarkin Pindiga, mai martaba Alhaji Muhammad Seyoji Ahmad,  da ke jihar Gome ya bukaci Gwamnatin tarayya da na jihohi da su samar da tsari mai ɗorewa a kan Noman Dabino da Sarrafa shi tare da kasuwancin sa a faɗin Nijeriya.

Sarkin ya bayyana haka ne a ranar Laraba lokacin da ya kai ziyara, ta musamman ma’aikatar ayyukan Gona ta jihar Kano, a cikin tsare -tsare gabatar da shirin ga gwamnatin jihar Kano, a bangaren daya kuma da kaddamar da Jagorancin Manoman Dabino na jiha.

Ya ce, “Akwai riba mai yawa a Noman na Dabino  ciki har da samar da aiyyukan yi ga matasan da basu da ayyuka a Karkara , ba wai laruwa zuwa ga Mai na Fetur da sauran Ma’adinai  a matsayin hanyoyin samar wa da kasar nan kudaden shiga”. A cewar Alhaji Muhammad Seyoji Ahmad

A nasa jawabin, mataimakin gwamnan jihar Kano Nasiru Yusuf Gawuna, wanda mai baiwa gwamna shawara na musamman a kan harkokin Noma Hafiz Muhammad , ya wakilta ya ce, “Shirin a na sa ran Noma Dabino Kadada (Hectre ) dubu Talatin a fadin jiha , da zarar an fara shirin karkashin tallafin banki kasa CBN da Bankin Duniya”. Inji Hafiz Muhammad

Wakilin mu Aminu Halilu Tudunwada, ya rawaito cewar, Sarkin na Pindiga tun da fari ya kai ziyara ga Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero, tare da gabatar masa da shirin wanda a ke sa ran mutum dubu dari da Ashirin ne za su samu ayyukan yi da an kaddamar da shi a jihar Kano.

 

Labarai

Ƴan kasuwa ku tsaftace magudanan ruwa bisa gabatowar Damuna – Ƙungiyar Amata ta kasuwar Singa

Published

on

An buƙaci ƴan kasuwa da su rinƙa tsaftace tare da gyara magudanan ruwa a cikin kasuwannin su, bisa yadda damuna ke ƙara gabatowa.

Shugaban ƙungiyar Amata reshen kasuwar Singa Alhaji Musa Ibrahim Ɗan gaske, ne ya bukacin hakan a zantawar sa da manema labarai, yayin kaddamar da tsaftace kasuwar da kuma gyara mugudanun ruwan kasuwar.

Alhaji Musa, ya kuma ce ta hanyar tsaftace magudanan ruwan ne za a gujewa kowacce irin ambaliyar ruwa a cikin kasuwanni.

Continue Reading

Hangen Dala

Yau za’a fara Shari’ar Ganduje da gwamnatin Kano

Published

on

A yau ne babbar kotun jaha mai lamba 4 zata fara sauraron wata sharia wadda gwamnatin kano ta ahigar.

 

Gwamnatin jahar kano dai ta shigar da karar tsohon gwamnan jahar kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da mai dakinsa Hafsat Umar Ganduje da kuma dansu Umar Abdullahi Ganduje da kuma wani kamfani mai suna Lamash da kuma Dr Jibrilla Muhammad.

 

Gwamnatin jahar kano dai tana zargin Ganduje da wadanna mutane da laifin hada baki da barnatar da dukiyoyin gwamnati.

 

 

Cikin zarge-zargen da ake yiwa su Ganduje akwai batun sun sayar da wasu filotai ba bisa ka’ida ba.

 

 

Da kuma batun zargin da akewa Ganduje na badakalar karbar dala tun a shekarar 2019.

 

 

Yanzu haka an girke jami,an tsaro a harabar sakateriyar Audu Bako inda kuma daga yanzu zuwa kowane lokaci kotun zata fara sauraron korafin kamar yadda wakilinmu Yusuf Nadabo Ismail ya rawaito

Continue Reading

Labarai

Ku tallafawa mazauna gidajen gyaran halin dan rage musu raɗaɗin rayuwa – Mallam Ibrahim Bunkure

Published

on

Limamin masallacin Salafussaleh dake unguwar Ɗorayi ƙarama a jihar Kano, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya shawarci al’umma da su ƙara dagewa wajen tallafawa mazauna gidajen ajiya da gyaran hali, da masu buƙata ta musamman, domin rage musu wani raɗaɗin rayuwa na yau da kullum.

Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya bayyana hakan ne yayin da suka tallafawa mazauna gidan gyaran hali na Goron Dutse, da kayayyakin Abinci, da kuma na gidan yara, a wani ɓangare na taya su bikin ƙaramar Sallah, wajen ganin sun samu farin ciki a bukukuwan ƙaramar sallar da aka gudanar.

Ya ce matuƙar masu hali za su rinƙa tallafawa mazauna gidan gyaran halin da abubuwan da suka sawwaƙa, babu makawa za’a rage musu wata damuwa ta yau da kullum.

Wakilinmu Yakubu Ibrahim Dogarai ya rawaito cewa, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya ce daga cikin kayan abincin da suka kai wa mazauna gidajen akwai Tuwon Sallah, da garin Kwakwaki, da kuma sinadarin Ɗanɗano, da Sukari, domin ragewa mazaunan gidajen wani raɗaɗin rayuwa.

Continue Reading

Trending