Connect with us

Labarai

Tun bayan ɓullar Corona jarin mu ya karye – Ƙananan ‘yan kasuwa

Published

on

Bayan ɓullar cutar Corona a Najeriya kawo wannan lokaci masu ƙananan sana’o na ci gaba da kokawa a kan ciniki da kuma durƙusar da tattalin arzikin su.

Sani Ibrahim mai laƙabin mai ‘yar sana’ar yara da ke sayar da soyayyar Doya a Garin Tiga da ke karamar hukumar Bebeji wanda ya kashe sama da shekaru goma sha shida ya na sana’ar.

Ya ce, “Annobar cutar Corona Virus ta yi mana matuƙar illa a harkar kasuwancin a yanzu wanda hakan yasa ba ni da jari sosai kamar yadda na ke da shi a baya ga kuma matsalar da a ke fama da ita”. Inji Sani Ibrahim

Haka zalika, Daya daga cikin masu gudanarda sana’ar sayar da kifi a kwanar Bagauda wato ‘yan Kifi.

Ya ce, “Yanzu ina rashin ciniki sosai, akwai bukatar gwamnati ta kawo mana ɗauki kasan cewar Cutar Corona ta yi mana illa”. Inji mai sana’ar sayar da kifi

Shima wani dattijo mai suna Alhaji Uba Tiga da ke gudanar da sana’ar kayan kanti wanda ya kwshe sama da shekaru arba’in ya na gudanarda da ita.

“Cinikin da mu ke yi a baya ko rabin sa ba ma yi a yanzu wanda hakan yasa jarina ya sami matsala sosai musamman a yanzu kasan cewar abaya jarina ya ɗara sama da naira dubu ɗari da takwas amma yanzu jarin nasa bai gaza dubu ɗari biyar ba domin duk ya yi amfani da ƙudin wajen ciyar da iyali a lokacin zaman kulle na Lockdown” A cewar Alhaji Uba Tiga

Wakilin mu Abdulkarim Muhammad Tukuntawa ya rawaito cewa, ‘Yan kasuwar a jihar Kano dai na cigaba da kira ga jama’a musamman gwamnati da a kawo musu ɗauki musamman waɗanda su ka gamu da iftila’in karyewar jarin su sakamakon ɓullar annobar cutar Corona a Kano da aka sha fama da ita wanda ta jefa rayuwar su da ta iyalansu cikin matsala a yanzu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Labarai

Rahoto: Saurayi ya kai iyayen budurwar sa kotu kan zargin cinye masa kudade

Published

on

Wani matashi ya yi zargin iyayen budurwar sa sun karbi kudaden aure har da sadaki a hannun sa, bayan ya rage kwanaki uku a daura aure, iyayen budurwar su ka kawar da maganar auren kuma tsawon watanni ba zancen aure ko kuma dawo masa da kudaden da ya bayar.

Sai dai iyayen budurwar sun yi da’awar cewar, an je gwaji ne kafin aure saurayin ya gudu, inda shi kuma ya mayar da martanin cewar, a ranar da a ka je gwajin bai je da isassun kudi ba, shi yasa ya tafi, kuma washe gari ko da yaje gidan budurwar bijiro da zancen ta fasa auren, yanzu tsohon saurayin ta za ta aura, hakan ta sanya ya garzaya kotun shari’ar musulunci domin a bi masa hakkin sa.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Mai sayen filaye ya kai karar abokin cinikin sa kotu bayan shekaru 3

Published

on

Kotun shari’ar musulunci da ke zamanta a unguwar Goran dutse, karkashin mai shari’a Isma’il Garba Kofar Na’isa, wani mutum mai suna Ibrahim Ishaq, ya yi karar wani mai suna Ibrahim Abba, kan cinikin wani filaye da su ka yi shekaru uku da su ka gabata.

Ibrahim Abba ya bai wa Ibrahim Ishaq motoci guda biyu shi kuma ya bashi filaye guda tara, daga bisani takaddama ta barke a tsakanin su, Ibrahiim Ishaq ya na zargin an cuce shi a cinikin, hakan ya sanya shi garzaya wa kotu.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

 

 

Continue Reading

Labarai

Rahoto: NAFDAC ta kama magungunan dabbobi na jabu a Kano

Published

on

Hukumar lura da ingancin abincin da magunguna ta kasa reshen jihar Kano NAFDAC, ta kai sumame wani gida a karamar hukumar Bichi, ta ka kama  wani mutum Muhammad Jamilu Sani, wanda aka samu yana hada magungunan dabbobi da allurai da ta ke zargin na jabu ne.

Shugaban hukumar Malam Shaba Muhammad ne ya bayyana hakan a ranar Laraba yayin zantawar sa da gidan rediyon Dala.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!