Connect with us

Wasanni

Cinikin ‘yan wasa: Liverpool ba za ta kashe kudi kamar na Chelsea ba – Klopp

Published

on

Mai horas da Liverpool Jurgen Klopp, ya ce kungiyar sa ta banbanta da sauran kungiyoyi wajen yadda sauran abokan hamayyar ta ke kashe makudan kudade wajen siyan ‘yan wasa.

Wannan batun na Kocin na zuwa ne yayin ganawar sa da wkiliyar BBC, dangane da yadda kungiyar Chelsea ke kashe makudan kudade wajen daukar ‘yan wasa a sabuwar kakar da za a fara.

Mai rike da kamun gasar Firimiya Liverpool ta dai kashe Fam miliyan 11.7 a bana wadda ta dauki dan wasa Tsimikas, a yayin da Chelsea ta kashe Fam miliyan 200 a hada-hadar kasuwancin ‘yan wasa a bana.

Mai horaswar ya ce“Abu ne mara tabbas yadda cutar Covid-19 ta haifar, zai zama mara amfani ga wasu, amma duk da mun kasance kungiya, ba za mu sauya lokaci guda ba, mu zama ko mu nuna dabi’ar irin yadda Chelsea ta yi a yanzu ba, mun banbanta da sauran kungiyoyin, saboda sau biyu mun je wasan karshe na cin kofin zakarun kungiyoyin nahiyar Turai, a zagaye na biyu ne mu ka lashe gasar, sannan mu ka lashe Firimiya duk da yadda mu ke a yanzu”. Inji Klopp.

Ko a shekarar bara, Liverpool ta kashe iya Fam miliyan 1.3 kawai, wanda ta dauki matashin dan wasan bayan kasar Holland, Sepp van den Berg daga kungiyar PEC Zwolle, inda ta daukimai tsaron raga Adrian da kuma Andy Lonergan a matsayin kyauta, sai kuma dan wasan gaban kungiyar, Red Bull Salzburg da ta dauka kuma dan kasar Japan, Takumi Minamino a wannan watan Janairu a kan kudi Fam miliyan 7.25.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Wasanni

Serie A: Dan wasa mara lasisi ya janyo an kwacewa Roma maki

Published

on

Hukumar shirya gasar Serie A a kasar Italiya ta kwacewa AS Roma maki Uku a gasar sakamakon saka wani dan wasa mara lasisi a cikin jerin mutane 25 da su ke fafatawa a gasar.

Dan wasan mai suna Amadou Diawara mai shekaru 22, kungiyar ba ta yi masa rijista ba a cikin gasar Serie A, wadda kuma ta saka dan wasan a karawar su da Hellas Verona a wasan farko na gasar da ta yi canjaras da kungiyar.

Yanzu haka Hellas Verona ita a ka baiwa maki da ci 3-0 a wasan bayan an gano dan wasan ba shi da rijista.

Continue Reading

Wasanni

Arturo Vidal: Dan wasan ya koma Inter Milan

Published

on

Dan wasan tsakiyar Barcelona, Arturo Vidal ya koma kungiyar Inter Milan a kan kudi Fam dubu 900 kwatantacin Yuro miliyan 1.

Dan wasan mai shekaru 33 dan kasar Chile yanzu haka ya koma karkashin tsohon abokin sa kuma wanda ya ke a matssyin mai horaswa wanda su ka lashe gasar Serie A uku a kungiyar Juventus.

Vidal ya koma Barcelona daga Bayern Munich a shekarar 2018, yanzu haka zai fafata wasa a karawar su da Fiorentina a ranar Asabar.

Continue Reading

Wasanni

Tottenham: Gareth Bale zai ci gaba da zama a kungiyar – Dilalin sa

Published

on

Dilalin dan wasan gaban kungiyar Tottenham, Jonathan Barnett, ya ce dan wasa Gareth Bale, zai ci gaba da zama a kungiyar a matsayin aro.

Bale mai shekaru 31 dan kasar Wales, a makon da ya gabata ne dai Tottenham ta karbi dan wasan daga Real Madrid a matsayin aro.

A shekarar 2013 ne dan wasan ya bar kungiyar sa ta Tottenham a kan kudi Fam miliyan 85 zuwa Real Madrid.

“Na tabbata babu wata matsala a tsakanin mu, saboda akwai fahimta a tsakanin juna, kuma wannan ita ce kungiyar da da ya zaba ya bugawa wasa, ina ganin babu wata matsala har idan ya bukaci ya kara wata shekarar a Tottenham a matsayin aro”. Inji Jonathan Barnett.

Har yanzu dai dan wasa Bale,ya na da kwantiragi a kungiyar sa ta Real Madrid har zuwa shekarar 2022.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!