Connect with us

Wasanni

Cinikin ‘yan wasa: Liverpool ba za ta kashe kudi kamar na Chelsea ba – Klopp

Published

on

Mai horas da Liverpool Jurgen Klopp, ya ce kungiyar sa ta banbanta da sauran kungiyoyi wajen yadda sauran abokan hamayyar ta ke kashe makudan kudade wajen siyan ‘yan wasa.

Wannan batun na Kocin na zuwa ne yayin ganawar sa da wkiliyar BBC, dangane da yadda kungiyar Chelsea ke kashe makudan kudade wajen daukar ‘yan wasa a sabuwar kakar da za a fara.

Mai rike da kamun gasar Firimiya Liverpool ta dai kashe Fam miliyan 11.7 a bana wadda ta dauki dan wasa Tsimikas, a yayin da Chelsea ta kashe Fam miliyan 200 a hada-hadar kasuwancin ‘yan wasa a bana.

Mai horaswar ya ce“Abu ne mara tabbas yadda cutar Covid-19 ta haifar, zai zama mara amfani ga wasu, amma duk da mun kasance kungiya, ba za mu sauya lokaci guda ba, mu zama ko mu nuna dabi’ar irin yadda Chelsea ta yi a yanzu ba, mun banbanta da sauran kungiyoyin, saboda sau biyu mun je wasan karshe na cin kofin zakarun kungiyoyin nahiyar Turai, a zagaye na biyu ne mu ka lashe gasar, sannan mu ka lashe Firimiya duk da yadda mu ke a yanzu”. Inji Klopp.

Ko a shekarar bara, Liverpool ta kashe iya Fam miliyan 1.3 kawai, wanda ta dauki matashin dan wasan bayan kasar Holland, Sepp van den Berg daga kungiyar PEC Zwolle, inda ta daukimai tsaron raga Adrian da kuma Andy Lonergan a matsayin kyauta, sai kuma dan wasan gaban kungiyar, Red Bull Salzburg da ta dauka kuma dan kasar Japan, Takumi Minamino a wannan watan Janairu a kan kudi Fam miliyan 7.25.

Wasanni

Jinya: Alphonso Davies zai shafe mako 8 – Bayern Munich

Published

on

Dan wasan gefen bayan Bayern Munich, Alphonso Davies, zai shafe tsawon makwanni 8 ya na fama da jinya sakamakon rauni da ya samu a kafar sa a karawar su Eintracht Frankfurt.

Davies mai shekaru 19, ya dai fita daga wasan bayan minti uku a wasan da su ka samu nasarar da ci 5-0.

Kocin Munich, Hansi Flick ya ce“Alphonso ya samu rauni a kafa, kuma mu na sa ran sai farkon watan Dismba zai dawo”.  

Continue Reading

Wasanni

La Liga: Ansu Faty ya kafa tarihi a El Classico

Published

on

Dan wasan gaban Barcelona, Ansu Fati, ya kasance dan wasa matashi na farko a karni na 21 da ya fara zura kwallo a gasar El Classico.

Faty dan wasan kasar Andulusiyya, ya zura kwallo ne a  minti 8 a filin wasa na Camp Nou wanda Barcelona ta sha kashi da ci 3-1 a hannun Real Madrid.

Dan wasan mai shekaru 17 da kwanaki 359 ya shiga cikin kundin tarihin wasan El Classico.

Continue Reading

Wasanni

Bayern Munich: Robert Lewandowski ya kafa tarihi a Bundesliga

Published

on

Dan wasan gaban Bayern Munich Robert Lewandowski ya kafa tarihi a gasar cin Bundesliga ta kasar Jamus bayan da ya zura kwallaye 3 rigis a wasan da su ka lallasa Eintracht Frankfurt da ci 5-0.

Kwallo 3 da Lewandowski ya zura yanzu haka kwallaye 10 kenan a wasanni biyar a kakar ta bana.

Babu wani dan wasa da ya taba zura kwallaye 10 a wasanni biyar a Bundesliga.

Lewandowski mai shekaru 32, ya kasance ya zura kwallo a ragar kowace kungiya 18 a gasar Bundesliga.

Haka zalika, Lewandowski shi ne dan wasan da ya zura kwallaye 55 a dukannin wasannin da a ka fafata a kakar da ta gabata.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!