Connect with us

Wasanni

Leeds United: Kocin kungiyar Marcelo Bielsa ya rattaba sabon kwantiragi

Published

on

Mai horas da Leeds United, Marcelo Bielsa, ya sake rattaba sabon kwantiragi a kungiyar har zuwa karshen kakar bana.

Bielsa mai shekaru 65, kwantiragin sa tuni yak are a karshen kakar da a ka kammala, tun bayan da ya dawo da kungiyar gasar Firimiya a cikin tsawon shekaru 16.

A jiya Alhamis mai horaswar dan kasar Argentina, ya cimma yarjejeniya da kungiyar, inda ta tabbatar da cewa Kocin ta ya rattaba sabon kwantiragi.

Leeds United za ta kara da Liverpool a karo na farko a gasar Firimiya ranar Asabar.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Wasanni

Serie A: Dan wasa mara lasisi ya janyo an kwacewa Roma maki

Published

on

Hukumar shirya gasar Serie A a kasar Italiya ta kwacewa AS Roma maki Uku a gasar sakamakon saka wani dan wasa mara lasisi a cikin jerin mutane 25 da su ke fafatawa a gasar.

Dan wasan mai suna Amadou Diawara mai shekaru 22, kungiyar ba ta yi masa rijista ba a cikin gasar Serie A, wadda kuma ta saka dan wasan a karawar su da Hellas Verona a wasan farko na gasar da ta yi canjaras da kungiyar.

Yanzu haka Hellas Verona ita a ka baiwa maki da ci 3-0 a wasan bayan an gano dan wasan ba shi da rijista.

Continue Reading

Wasanni

Arturo Vidal: Dan wasan ya koma Inter Milan

Published

on

Dan wasan tsakiyar Barcelona, Arturo Vidal ya koma kungiyar Inter Milan a kan kudi Fam dubu 900 kwatantacin Yuro miliyan 1.

Dan wasan mai shekaru 33 dan kasar Chile yanzu haka ya koma karkashin tsohon abokin sa kuma wanda ya ke a matssyin mai horaswa wanda su ka lashe gasar Serie A uku a kungiyar Juventus.

Vidal ya koma Barcelona daga Bayern Munich a shekarar 2018, yanzu haka zai fafata wasa a karawar su da Fiorentina a ranar Asabar.

Continue Reading

Wasanni

Tottenham: Gareth Bale zai ci gaba da zama a kungiyar – Dilalin sa

Published

on

Dilalin dan wasan gaban kungiyar Tottenham, Jonathan Barnett, ya ce dan wasa Gareth Bale, zai ci gaba da zama a kungiyar a matsayin aro.

Bale mai shekaru 31 dan kasar Wales, a makon da ya gabata ne dai Tottenham ta karbi dan wasan daga Real Madrid a matsayin aro.

A shekarar 2013 ne dan wasan ya bar kungiyar sa ta Tottenham a kan kudi Fam miliyan 85 zuwa Real Madrid.

“Na tabbata babu wata matsala a tsakanin mu, saboda akwai fahimta a tsakanin juna, kuma wannan ita ce kungiyar da da ya zaba ya bugawa wasa, ina ganin babu wata matsala har idan ya bukaci ya kara wata shekarar a Tottenham a matsayin aro”. Inji Jonathan Barnett.

Har yanzu dai dan wasa Bale,ya na da kwantiragi a kungiyar sa ta Real Madrid har zuwa shekarar 2022.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!