Connect with us

Labarai

Ganduje zai bude kwalejojin fasaha domin jarrabawar NABTEB

Published

on

Gwamnatin Jihar Kano ta bayar da umarnin hanzarta bude makarantun kwalejojin fasaha guda shida a jihar domin baiwa daliban ajin karshe damar rubuta jarrabawar kammalawa ta NABTEB.

Kwamishinan ilimi na Jihar Kano Malam Muhammad Sanusi Kiru ne ya bayar da umarnin bayan samun amincewar gwamna Abdullahi Umar Ganduje, biyo bayan bukatar hakan da kwamishinan ya nema daga wurin gwamnan.

Ya ce, “Gwamnatin Jihar Kano ta amince da a gaggauta biyan kudin jarrabawar daliban ‘yan ajin karshe wato SSS3 domin ba su damar rubuta jarrabawar”. A cewar Malam Muhammad Sanusi Kiru

Wata sanarwa da jami’in yada labarai na ma’aikatar ilimi ta Jihar Kano Aliyu Yusuf ya fitar da yammacin yau, ta ce, gwamnatin ta ware kudi sama da naira miliyan 16 domin ciyar da daliban da ma sauran bukatu wajen ganin an samu nasarar rubuta jarrabawar.

 

Labarai

Kano da Indiya Danjuma ne da Danjummai – Ganduje

Published

on

Gwamantin Kano ta ce za ta ci gaba da kyautata alakar ta da kasar Indiya.

Gwamnan Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje ne ya bayyana hakan a lokacin da ya ke karbar bakwancin karamin jakadan kasar Indiya a Nijerya.

Ya ce”Dama dai akwai kyakyawar alaka tsakanin kasar ta Indiya da Nijeriya, sannan gwamnati za ta ci gaba da amfani da kayayyakin aikin noma na kasar Indiyar, musamman ma yadda manoma ke jin dadin aiki da su”. Inji Ganduje.

Wakiliyar mu Zahrau Nasir ta rawaito cewa karamin jakadan kasar Indiya a Nijeriya, Abay Takur ya kuma ce ya kawo ziyarar ne da tawagar sa, domin kara inganta alaka da jihar Kano.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Babu zanga-zanga a musulunci domin neman wata bukata – Liman

Published

on

Limamin masallacin juma’a na Shelkwatar rundunar ‘yan sanda da ke Bompai SP Abdulkadir Haruna ya ce, rayuwar al’umma ba za ta inganta ba matukar babu zaman lafiya.

SP Abdulkadir Haruna, ya bayyana hakan a zantawar sa da wakilin mu Abba Isah Muhammad jim kadan bayan idar da sallar juma’a.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Mu guji yada karya a kafafen sada zumunta – Liman

Published

on

Babban limamin masallacin juma’a na Masjidul Kuba da ke unguwar Tukuntawa, Malam Ibrahim Abubakar Tofa ya ce, al’umma su guji yada karya a kafafen sadarwa na Internet wanda hakan kan janyo fitina a cikin al’umma.

Malam Ibrahim Abubakar Tofa, ya bayyana hakan a hudubar sa da ya gudanar a masallacin na Juma’a.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!