Connect with us

Wasanni

Premier League: An kafa tarihi a farkon gasar ta bana

Published

on

Mai rike da kambun gasar Firimiyar kasar Ingila Liverpool, ta ci gaba da kafa tarihi a gasar na samun nasarar wasanni 60 ba tare da ta yi rashin nasara a gida ba.

Tun bayan da Chelsea ta yi wasanni 86 ba tare da an zura mata kwallo a gida ban tun a watan Oktobar shekarar 2008, sai kuma ita Liverpool wadda a watan Disambar shekarar 1980 ta taba kafa irin wannan tarihin na samun nasarar wasanni 63 ba tare da an zura mata kwallo a gida ba a gasar Firimiya.

Wannan da is hi ne gasar Firimiya ta biyu kenan da aka fara wasan farko a ka fara zura kwallaye 4 da 3 a wasan Leeds United da Liverpool, tun bayan da Manchester United ta fara zura kwallo 5 da 1 a ragar Fulham a karo na farkon fara wasan a watan Agusta na shekarar 2006, wanda a wasan zagayen farko ta zura kwallaye 4-1 a raga.

Kuma wannan shi ne karo na farko da a ka zurawa Liverpool kwallaye 3 a raga a wasan farko da Leeds United tun cikin shekarar 1982. Yanzu haka Liverpool ta samu nasarar wasanni 35 a gasar Firimiya wanda Mphammad Salah ya zura kwallaye 35 a raga cikin gasar, wanda a yanzu kuma ya yi ywa dan wasa Wayne Rooney fintinkau a gasar wanda ya zura kwallaye 34 a watan Satumba na shekarar 2008 da kuma watan Fabrairu na shekarar 2001.

Shi kuwa dan wasan bayan Liverpool, Virgil van Dijk ya zura kwallaye 10 a gasar da Liverpool, wanda ya fi kowane dan wasan baya zura kwallaye a gasar, tun lokacin da ya fara wasa a kungiyar a watan Janairun shekarar 2018, kuma duka kwallaye 9 da ya zura da kai ya zura su.

Dan wasan bayan Liverpool Van Dijk a cikin wasanni 154 da ya yi a Liverpool kwallaye 2 kawai ya jawo a ka zurawa Liverpool a raga.

Haka zalika Jack Harrison da Patrick Bamford da kuma Mateusz Klich sun kasance sababbin ‘yan wasa da su ka fara zura kwallaye a raga a farkon wasa a gasar Firimiya, tun bayan da dan wasan Leeds United Nick Barmby ya fara zura kwallo a farkon wasan sa a watan Agusta na shekarar 2002 a haduwar da su ka yi da Mancheseter City, wanda kuma ya kasance dan wasan da ya fara zura kwallo a waje tun bayan da Alan Smitth ya yi a watan Nuwamba na shekarar 1998 a Anfield gidan Liverpool.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Wasanni

Serie A: Dan wasa mara lasisi ya janyo an kwacewa Roma maki

Published

on

Hukumar shirya gasar Serie A a kasar Italiya ta kwacewa AS Roma maki Uku a gasar sakamakon saka wani dan wasa mara lasisi a cikin jerin mutane 25 da su ke fafatawa a gasar.

Dan wasan mai suna Amadou Diawara mai shekaru 22, kungiyar ba ta yi masa rijista ba a cikin gasar Serie A, wadda kuma ta saka dan wasan a karawar su da Hellas Verona a wasan farko na gasar da ta yi canjaras da kungiyar.

Yanzu haka Hellas Verona ita a ka baiwa maki da ci 3-0 a wasan bayan an gano dan wasan ba shi da rijista.

Continue Reading

Wasanni

Arturo Vidal: Dan wasan ya koma Inter Milan

Published

on

Dan wasan tsakiyar Barcelona, Arturo Vidal ya koma kungiyar Inter Milan a kan kudi Fam dubu 900 kwatantacin Yuro miliyan 1.

Dan wasan mai shekaru 33 dan kasar Chile yanzu haka ya koma karkashin tsohon abokin sa kuma wanda ya ke a matssyin mai horaswa wanda su ka lashe gasar Serie A uku a kungiyar Juventus.

Vidal ya koma Barcelona daga Bayern Munich a shekarar 2018, yanzu haka zai fafata wasa a karawar su da Fiorentina a ranar Asabar.

Continue Reading

Wasanni

Tottenham: Gareth Bale zai ci gaba da zama a kungiyar – Dilalin sa

Published

on

Dilalin dan wasan gaban kungiyar Tottenham, Jonathan Barnett, ya ce dan wasa Gareth Bale, zai ci gaba da zama a kungiyar a matsayin aro.

Bale mai shekaru 31 dan kasar Wales, a makon da ya gabata ne dai Tottenham ta karbi dan wasan daga Real Madrid a matsayin aro.

A shekarar 2013 ne dan wasan ya bar kungiyar sa ta Tottenham a kan kudi Fam miliyan 85 zuwa Real Madrid.

“Na tabbata babu wata matsala a tsakanin mu, saboda akwai fahimta a tsakanin juna, kuma wannan ita ce kungiyar da da ya zaba ya bugawa wasa, ina ganin babu wata matsala har idan ya bukaci ya kara wata shekarar a Tottenham a matsayin aro”. Inji Jonathan Barnett.

Har yanzu dai dan wasa Bale,ya na da kwantiragi a kungiyar sa ta Real Madrid har zuwa shekarar 2022.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!