Connect with us

Wasanni

La Liga: Marcos Acuna ya koma Sevilla

Published

on

Dan wasan gefen bayan kungiyar kwallon kafa na Sporting CP ta kasar Portugal, Marcos Acuna, ya koma kungiyar kwallon kafa ta Sevilla.

Dan wasan yam aye gurbin Sergio Reguilon bayan da ya bar kungiyar ta Sevilla.

Dan wasan Acuna dan kasar Argentina ya rattaba kwantiragi na tsawon shekaru hudu a Sevilla, bayan da ta dauke shi a kan kudi Yuro miliyan 10.

Acuna ya buga wasanni 134 a Sporting, bayan da ya shafe tsawon shekaru 3 tare da kungiyar a gasar kasar Portugal ta Primera.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Wasanni

Serie A: Dan wasa mara lasisi ya janyo an kwacewa Roma maki

Published

on

Hukumar shirya gasar Serie A a kasar Italiya ta kwacewa AS Roma maki Uku a gasar sakamakon saka wani dan wasa mara lasisi a cikin jerin mutane 25 da su ke fafatawa a gasar.

Dan wasan mai suna Amadou Diawara mai shekaru 22, kungiyar ba ta yi masa rijista ba a cikin gasar Serie A, wadda kuma ta saka dan wasan a karawar su da Hellas Verona a wasan farko na gasar da ta yi canjaras da kungiyar.

Yanzu haka Hellas Verona ita a ka baiwa maki da ci 3-0 a wasan bayan an gano dan wasan ba shi da rijista.

Continue Reading

Wasanni

Arturo Vidal: Dan wasan ya koma Inter Milan

Published

on

Dan wasan tsakiyar Barcelona, Arturo Vidal ya koma kungiyar Inter Milan a kan kudi Fam dubu 900 kwatantacin Yuro miliyan 1.

Dan wasan mai shekaru 33 dan kasar Chile yanzu haka ya koma karkashin tsohon abokin sa kuma wanda ya ke a matssyin mai horaswa wanda su ka lashe gasar Serie A uku a kungiyar Juventus.

Vidal ya koma Barcelona daga Bayern Munich a shekarar 2018, yanzu haka zai fafata wasa a karawar su da Fiorentina a ranar Asabar.

Continue Reading

Wasanni

Tottenham: Gareth Bale zai ci gaba da zama a kungiyar – Dilalin sa

Published

on

Dilalin dan wasan gaban kungiyar Tottenham, Jonathan Barnett, ya ce dan wasa Gareth Bale, zai ci gaba da zama a kungiyar a matsayin aro.

Bale mai shekaru 31 dan kasar Wales, a makon da ya gabata ne dai Tottenham ta karbi dan wasan daga Real Madrid a matsayin aro.

A shekarar 2013 ne dan wasan ya bar kungiyar sa ta Tottenham a kan kudi Fam miliyan 85 zuwa Real Madrid.

“Na tabbata babu wata matsala a tsakanin mu, saboda akwai fahimta a tsakanin juna, kuma wannan ita ce kungiyar da da ya zaba ya bugawa wasa, ina ganin babu wata matsala har idan ya bukaci ya kara wata shekarar a Tottenham a matsayin aro”. Inji Jonathan Barnett.

Har yanzu dai dan wasa Bale,ya na da kwantiragi a kungiyar sa ta Real Madrid har zuwa shekarar 2022.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!