Connect with us

Labarai

Duk musulmi na gari ba zai kare mai batanci ga Annabi ba – Mansur Gabari

Published

on

Gidauniyar Empathy mai tausayawa da tallafawa al’umma da ke jihar Kano ta ce, duk mutumin da ya amsa sunan sa musulmi ya kuma sanya hannu domin kare mutumin da ya yi batanci ga Annabi ya yi Ridda.

Shugaban gidauniyar Mansur Musa Gabari ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da Dala FM, game da yadda kungiyar ta ke nuna takaicin ta a kan yadda wasu lauyoyi musulmi da kuma wasu daga kudancin kasar nan ke kokarin bada kariya ga Yahaya Shariff Aminu, wanda kotu ta yankewa hukuncin kisa, sakamakon furta kalaman batanci ga fiyayyan halitta Annabi Muhammad S.A.W.

Ya ce, “Kamata ya yi duk wani lauya da ya kasance musulmi ya bada tasa gudunmowar domin ganin an zartar da hukuncin da kotu ta yanke ga wanda ya yi batanci ga annabi Muhammad S.AW”.  Inji Mansur Musa Gabari

Mansur Musa Gabari, ya kara da cewa, duk wani musulmi kamata ya yi ya fifita ma’aiki Annabi Muhammad S.A W a kan duniyarsa da iyalinsa da ma kansa, don samun dacewa.

 

Labarai

Ƴan kasuwa ku tsaftace magudanan ruwa bisa gabatowar Damuna – Ƙungiyar Amata ta kasuwar Singa

Published

on

An buƙaci ƴan kasuwa da su rinƙa tsaftace tare da gyara magudanan ruwa a cikin kasuwannin su, bisa yadda damuna ke ƙara gabatowa.

Shugaban ƙungiyar Amata reshen kasuwar Singa Alhaji Musa Ibrahim Ɗan gaske, ne ya bukacin hakan a zantawar sa da manema labarai, yayin kaddamar da tsaftace kasuwar da kuma gyara mugudanun ruwan kasuwar.

Alhaji Musa, ya kuma ce ta hanyar tsaftace magudanan ruwan ne za a gujewa kowacce irin ambaliyar ruwa a cikin kasuwanni.

Continue Reading

Hangen Dala

Yau za’a fara Shari’ar Ganduje da gwamnatin Kano

Published

on

A yau ne babbar kotun jaha mai lamba 4 zata fara sauraron wata sharia wadda gwamnatin kano ta ahigar.

 

Gwamnatin jahar kano dai ta shigar da karar tsohon gwamnan jahar kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da mai dakinsa Hafsat Umar Ganduje da kuma dansu Umar Abdullahi Ganduje da kuma wani kamfani mai suna Lamash da kuma Dr Jibrilla Muhammad.

 

Gwamnatin jahar kano dai tana zargin Ganduje da wadanna mutane da laifin hada baki da barnatar da dukiyoyin gwamnati.

 

 

Cikin zarge-zargen da ake yiwa su Ganduje akwai batun sun sayar da wasu filotai ba bisa ka’ida ba.

 

 

Da kuma batun zargin da akewa Ganduje na badakalar karbar dala tun a shekarar 2019.

 

 

Yanzu haka an girke jami,an tsaro a harabar sakateriyar Audu Bako inda kuma daga yanzu zuwa kowane lokaci kotun zata fara sauraron korafin kamar yadda wakilinmu Yusuf Nadabo Ismail ya rawaito

Continue Reading

Labarai

Ku tallafawa mazauna gidajen gyaran halin dan rage musu raɗaɗin rayuwa – Mallam Ibrahim Bunkure

Published

on

Limamin masallacin Salafussaleh dake unguwar Ɗorayi ƙarama a jihar Kano, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya shawarci al’umma da su ƙara dagewa wajen tallafawa mazauna gidajen ajiya da gyaran hali, da masu buƙata ta musamman, domin rage musu wani raɗaɗin rayuwa na yau da kullum.

Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya bayyana hakan ne yayin da suka tallafawa mazauna gidan gyaran hali na Goron Dutse, da kayayyakin Abinci, da kuma na gidan yara, a wani ɓangare na taya su bikin ƙaramar Sallah, wajen ganin sun samu farin ciki a bukukuwan ƙaramar sallar da aka gudanar.

Ya ce matuƙar masu hali za su rinƙa tallafawa mazauna gidan gyaran halin da abubuwan da suka sawwaƙa, babu makawa za’a rage musu wata damuwa ta yau da kullum.

Wakilinmu Yakubu Ibrahim Dogarai ya rawaito cewa, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya ce daga cikin kayan abincin da suka kai wa mazauna gidajen akwai Tuwon Sallah, da garin Kwakwaki, da kuma sinadarin Ɗanɗano, da Sukari, domin ragewa mazaunan gidajen wani raɗaɗin rayuwa.

Continue Reading

Trending