Connect with us

Wasanni

EFL: ‘Yan kallo dubu 1 za su fara kallon wasa a cikin fili

Published

on

Gwamnatin kasar Ingila ta tabbatar da cewa a kalla ‘yan kallo dubu daya ne za su fara kallon wasa a cikin fili a wasannin kwallon kafar kasar da a ke fafatawa.

Tun a baya gwamnatin kasar ta sanar da cewa a ranar 1 ga watan Oktoba, za a baiwa ‘yan kallo dama su shiga cikin fili su kalli wasa, tun bayan da a ka hana su shiga sakamakon cutar Covid-19.

Cikin wasanin da a ka yarjewa ‘yan kallon su shiga akwai na gasar Championship da za a fafata a karshen wannan makon ciki sun hadar da:

Championship

  • Luton Town da Derby County
  • Middlesbrough da AFC Bournemouth
  • Norwich City da Preston North End

League One

  • Blackpool da Swindon Town
  • Charlton Athletic da Doncaster Rovers
  • Hull City da Crewe Alexandra
  • Shrewsbury Town da Northampton Town

League Two

  • Carlisle United da Southend United
  • Forest Green Rovers da Bradford City
  • Morecambe da Cambridge United

Ko a makon da ya gabata sai da ‘yan kallo 734, su ka shiga cikin filin wasa domin kallon wasan da West Ham United ta fafata da Arsenal bangaren gasar ta mata a filin wasa na Chigwell.

 

Wasanni

Jinya: Alphonso Davies zai shafe mako 8 – Bayern Munich

Published

on

Dan wasan gefen bayan Bayern Munich, Alphonso Davies, zai shafe tsawon makwanni 8 ya na fama da jinya sakamakon rauni da ya samu a kafar sa a karawar su Eintracht Frankfurt.

Davies mai shekaru 19, ya dai fita daga wasan bayan minti uku a wasan da su ka samu nasarar da ci 5-0.

Kocin Munich, Hansi Flick ya ce“Alphonso ya samu rauni a kafa, kuma mu na sa ran sai farkon watan Dismba zai dawo”.  

Continue Reading

Wasanni

La Liga: Ansu Faty ya kafa tarihi a El Classico

Published

on

Dan wasan gaban Barcelona, Ansu Fati, ya kasance dan wasa matashi na farko a karni na 21 da ya fara zura kwallo a gasar El Classico.

Faty dan wasan kasar Andulusiyya, ya zura kwallo ne a  minti 8 a filin wasa na Camp Nou wanda Barcelona ta sha kashi da ci 3-1 a hannun Real Madrid.

Dan wasan mai shekaru 17 da kwanaki 359 ya shiga cikin kundin tarihin wasan El Classico.

Continue Reading

Wasanni

Bayern Munich: Robert Lewandowski ya kafa tarihi a Bundesliga

Published

on

Dan wasan gaban Bayern Munich Robert Lewandowski ya kafa tarihi a gasar cin Bundesliga ta kasar Jamus bayan da ya zura kwallaye 3 rigis a wasan da su ka lallasa Eintracht Frankfurt da ci 5-0.

Kwallo 3 da Lewandowski ya zura yanzu haka kwallaye 10 kenan a wasanni biyar a kakar ta bana.

Babu wani dan wasa da ya taba zura kwallaye 10 a wasanni biyar a Bundesliga.

Lewandowski mai shekaru 32, ya kasance ya zura kwallo a ragar kowace kungiya 18 a gasar Bundesliga.

Haka zalika, Lewandowski shi ne dan wasan da ya zura kwallaye 55 a dukannin wasannin da a ka fafata a kakar da ta gabata.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!