Connect with us

Wasanni

Bayern Munich: Ko kasan cewa a sansanin ‘yan gudun Hijira a ka haifi Davies?

Published

on

Dan wasan bayan gefen kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich, Alphonso Davies wanda ya tallafawa Bayern Munich ta lashe kofi uku a kakar da ta gabata ciki harda Champoins League da Bundesliga tare da kuma Pokal Cup na kasar Jamus.

Dan wasan mai shekaru 19, wanda ya lashe kyautar Bundesliga Rookie award na kakar 2019-20, sakamakon rawar da ya taka.

Lokacin da ya daga Farantin gasar Bundesliga.

An dai haifi Davies ne a sansanin ‘yan gudun Hijira dake kasar Ghana, bayan da iyayen sa su ka gudu daga ainihin kasar su ta Liberia.

Davies da iyayen sa lokacin ya na da shekara biyar a duniya kuma shi ne daga farko daga kasa a kungiyar sa ta yara a kasar Canada.

Tun a wannan can lokaci iyayen dan wasan Davies su ka yi kaura zuwa kasar Canada a lokacin ya na dan shekara biyar da haihuwa, kuma a shekarar 2017 ne ya samu shaidar katin izini na zama a kasar Canada.

Davies ya na karami a daya gefen kuma ya daga kocin Champions League.

Davies ya kuma kasance dan wasa na farko a kasar Canada da ya taba zuwa wasan karshe a kasar a gasar cin kofin zakarun kungiyoyin nahiyar Turai, har ma ya samu damar lashe gasar a karo na farko a tarihin kasar da shi kan sa.

Yanzu haka dai tauraruwar dan wasan na haskakawa a Bayern Munich, tun bayan da ta dauke shi daga kungiyar Vancouver Whitecaps ta gasar MLS ta kasar Amurka a shekarar 2019.

Wasanni

Jinya: Alphonso Davies zai shafe mako 8 – Bayern Munich

Published

on

Dan wasan gefen bayan Bayern Munich, Alphonso Davies, zai shafe tsawon makwanni 8 ya na fama da jinya sakamakon rauni da ya samu a kafar sa a karawar su Eintracht Frankfurt.

Davies mai shekaru 19, ya dai fita daga wasan bayan minti uku a wasan da su ka samu nasarar da ci 5-0.

Kocin Munich, Hansi Flick ya ce“Alphonso ya samu rauni a kafa, kuma mu na sa ran sai farkon watan Dismba zai dawo”.  

Continue Reading

Wasanni

La Liga: Ansu Faty ya kafa tarihi a El Classico

Published

on

Dan wasan gaban Barcelona, Ansu Fati, ya kasance dan wasa matashi na farko a karni na 21 da ya fara zura kwallo a gasar El Classico.

Faty dan wasan kasar Andulusiyya, ya zura kwallo ne a  minti 8 a filin wasa na Camp Nou wanda Barcelona ta sha kashi da ci 3-1 a hannun Real Madrid.

Dan wasan mai shekaru 17 da kwanaki 359 ya shiga cikin kundin tarihin wasan El Classico.

Continue Reading

Wasanni

Bayern Munich: Robert Lewandowski ya kafa tarihi a Bundesliga

Published

on

Dan wasan gaban Bayern Munich Robert Lewandowski ya kafa tarihi a gasar cin Bundesliga ta kasar Jamus bayan da ya zura kwallaye 3 rigis a wasan da su ka lallasa Eintracht Frankfurt da ci 5-0.

Kwallo 3 da Lewandowski ya zura yanzu haka kwallaye 10 kenan a wasanni biyar a kakar ta bana.

Babu wani dan wasa da ya taba zura kwallaye 10 a wasanni biyar a Bundesliga.

Lewandowski mai shekaru 32, ya kasance ya zura kwallo a ragar kowace kungiya 18 a gasar Bundesliga.

Haka zalika, Lewandowski shi ne dan wasan da ya zura kwallaye 55 a dukannin wasannin da a ka fafata a kakar da ta gabata.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!