Connect with us

Wasanni

Thiago Alcantara: Zai saka riga mai lamba 6 a Liverpool

Published

on

Zakarar gasar Firimiyar kasar Ingila, Liverpool ta amince za ta dauki dan wasaona, Thiago Alcantara daga Bayern Munich wacce ta ke rike da zakarar gasar kungiyoyin nahiyar Turai da Bundesligar kasar Jamus.

Thiago mai shekaru 29, wanda Liverpool ta cimma yarjejeniyar daukar dan wasan a kan kudi Fam miliyan 20 da kuma karin Fam miliyan 5 a kai.

Dan wasan zai rattaba kwantiragin shekaru hudu a Liverpool, bayan da a ka cimma yarjejeniya a tsakanin juna.

A shekarar 2013 ne dan wasan ya koma Bayern Munich daga Barcelona, kuma ya tallafawa kungiyar sa ta lashe Champions League a hannun PSG.

Thiago Alcantara zai saka riga mai lamba 6 a kungiyar kwallon kafa ta Liverpool, kuma ya kasance shi ne dan wasa na biyu da Liverpool ta dauka, tun bayan da ta dauki dan wasan bayan kasar Girka, Kostas Tsimikas.

Haka zalika, an cimma yarjejeniyar cewa idan dan wasan ya tallafawa Liverpool ta samu nasara a gasar Firimiya da Champions League za a kara masa Fam miliyan 5 a kai

Wasanni

Jinya: Alphonso Davies zai shafe mako 8 – Bayern Munich

Published

on

Dan wasan gefen bayan Bayern Munich, Alphonso Davies, zai shafe tsawon makwanni 8 ya na fama da jinya sakamakon rauni da ya samu a kafar sa a karawar su Eintracht Frankfurt.

Davies mai shekaru 19, ya dai fita daga wasan bayan minti uku a wasan da su ka samu nasarar da ci 5-0.

Kocin Munich, Hansi Flick ya ce“Alphonso ya samu rauni a kafa, kuma mu na sa ran sai farkon watan Dismba zai dawo”.  

Continue Reading

Wasanni

La Liga: Ansu Faty ya kafa tarihi a El Classico

Published

on

Dan wasan gaban Barcelona, Ansu Fati, ya kasance dan wasa matashi na farko a karni na 21 da ya fara zura kwallo a gasar El Classico.

Faty dan wasan kasar Andulusiyya, ya zura kwallo ne a  minti 8 a filin wasa na Camp Nou wanda Barcelona ta sha kashi da ci 3-1 a hannun Real Madrid.

Dan wasan mai shekaru 17 da kwanaki 359 ya shiga cikin kundin tarihin wasan El Classico.

Continue Reading

Wasanni

Bayern Munich: Robert Lewandowski ya kafa tarihi a Bundesliga

Published

on

Dan wasan gaban Bayern Munich Robert Lewandowski ya kafa tarihi a gasar cin Bundesliga ta kasar Jamus bayan da ya zura kwallaye 3 rigis a wasan da su ka lallasa Eintracht Frankfurt da ci 5-0.

Kwallo 3 da Lewandowski ya zura yanzu haka kwallaye 10 kenan a wasanni biyar a kakar ta bana.

Babu wani dan wasa da ya taba zura kwallaye 10 a wasanni biyar a Bundesliga.

Lewandowski mai shekaru 32, ya kasance ya zura kwallo a ragar kowace kungiya 18 a gasar Bundesliga.

Haka zalika, Lewandowski shi ne dan wasan da ya zura kwallaye 55 a dukannin wasannin da a ka fafata a kakar da ta gabata.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!