Connect with us

Wasanni

Kocin Munich: Ina taya Klopp murnar daukan Thiago

Published

on

Mai horas da kungiyar Bayern Muncih Hansi Flick ya taya Kocin Liverpool, Jurgen Klopp murnar daukan dan wasa Thiago Alcantara.

Tuni dan wasan, Thiago Alcantara ya yi bankwana da kungiyar sa ta Bayern Munich da kuma abokan karawar sa, sakamakon barin kungiyar da zai yi zuwa Liverpool.

Thiago mai shekaru 29, ya cimma yarjejeniya da Liverpool, inda za ta biya kudin sa a kan kudi Fam miliyan 25 kwatankwacin Yuro miliyan 27.5.

Kocin ya ce“Thiago dan wasa ne wanda ya banbanta da sauran ‘yan wasa, ya shafe tsawon shekaru 7 tare da mu, kwararre ne a harkar kwallon kafa, mu dai duk jikin mu ya yi sanyi yau dinnan, saboda ya yi sallama da mu, kawai dai zan yi masa fatan alheri, kuma ina yabawa Jurgen Klopp sakamakon daukan dan wasan da ya yi, mu kuma mun yi rashin dan wasa mai nagarta”. Inji Flick.

Wasanni

Jinya: Alphonso Davies zai shafe mako 8 – Bayern Munich

Published

on

Dan wasan gefen bayan Bayern Munich, Alphonso Davies, zai shafe tsawon makwanni 8 ya na fama da jinya sakamakon rauni da ya samu a kafar sa a karawar su Eintracht Frankfurt.

Davies mai shekaru 19, ya dai fita daga wasan bayan minti uku a wasan da su ka samu nasarar da ci 5-0.

Kocin Munich, Hansi Flick ya ce“Alphonso ya samu rauni a kafa, kuma mu na sa ran sai farkon watan Dismba zai dawo”.  

Continue Reading

Wasanni

La Liga: Ansu Faty ya kafa tarihi a El Classico

Published

on

Dan wasan gaban Barcelona, Ansu Fati, ya kasance dan wasa matashi na farko a karni na 21 da ya fara zura kwallo a gasar El Classico.

Faty dan wasan kasar Andulusiyya, ya zura kwallo ne a  minti 8 a filin wasa na Camp Nou wanda Barcelona ta sha kashi da ci 3-1 a hannun Real Madrid.

Dan wasan mai shekaru 17 da kwanaki 359 ya shiga cikin kundin tarihin wasan El Classico.

Continue Reading

Wasanni

Bayern Munich: Robert Lewandowski ya kafa tarihi a Bundesliga

Published

on

Dan wasan gaban Bayern Munich Robert Lewandowski ya kafa tarihi a gasar cin Bundesliga ta kasar Jamus bayan da ya zura kwallaye 3 rigis a wasan da su ka lallasa Eintracht Frankfurt da ci 5-0.

Kwallo 3 da Lewandowski ya zura yanzu haka kwallaye 10 kenan a wasanni biyar a kakar ta bana.

Babu wani dan wasa da ya taba zura kwallaye 10 a wasanni biyar a Bundesliga.

Lewandowski mai shekaru 32, ya kasance ya zura kwallo a ragar kowace kungiya 18 a gasar Bundesliga.

Haka zalika, Lewandowski shi ne dan wasan da ya zura kwallaye 55 a dukannin wasannin da a ka fafata a kakar da ta gabata.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!