Connect with us

Labarai

Kudade sun yi tasiri a zaben jihar Edo – CDD

Published

on

Cibiyar bunƙasa dimukuraɗiyya ta CDD ta ce, duk wanda ya ci zaɓen gwamnan jihar Edo da a ka gabatar a jiya Asabar, ƙarfin kuɗinsa ne yasa ya samu nasara.

Jami’i mai lura da wakilan cibiyar dake sanya idanu a zaɓen jihar Farfesa Jibril Ibrahim ne ya bayyana hakan a zantawarsa da Dala FM

Ya ce, “Wakilai 250 tare da ƴan jarida 18 ne ke aikin sanya ido kan zaɓen a ƙarƙashin cibiyar, kuma rahotannin da muka samu daga wakilan mu ya nuna cewa amfani da kuɗi wajen sayen ƙuri’u ya yi tasiri matuƙa a rufunan zaɓe”.

Ya kuma ce, “Labaran ƙarya game da zaɓen sun ta’azzara, kasancewar wasu na amfani da kafafan sada zumunta wajen yaɗa labaran da basu da tushe game da zaɓen”.

Ya kara da cewa, “An fuskanci matsalar rashin fara zaɓe da wuri a wasu mazaɓun, duk da cewar shekara da shekaru an saba fuskantar wannan matsalar a zaɓe amma ya kamata a ce an kauce mata” A cewar Farfesa Jibril Ibrahim

Farfesa Farfesa Jibril Ibrahim ya kuma ce, an yi zaɓen ba tare da samun rigingimun zaɓe ba wanda tun a baya a ka yi zato, sai dai wanda ba a rasa ba.

Inda kuma a yanzu haka rahotanni suka fita cewar, Gamna Godwin Obase na jam’iyyar PDP, ya lashe zaben jihar ta Edo da kuri’u 307, 955, inda abokin takararsa daga jam’iyyar APC Ize-Iyamu ya samu kuri’u 223, 619.

 

 

Labarai

NAHCON ta sanya ranar fara jigilar maniyyata aikin hajjin bana zuwa Saudiyya

Published

on

Yanzu haka hukumar Aikin Hajji ta ƙasa NAHCON, ta 15 ga watan nan na Mayun 2024, a matsayin ranar da za’a fara jigilar maniyyata aikin hajjin bana, zuwa ƙasa mai tsarki.

Bayanin hakan ya fito ne ta bakin shugaban hukumar ta NAHCON, Jalal Ahmad Arabi, a wajen taron masu ruwa da tsaki kan aikin Hajji da Umrah, da ya gudana yau Alhamis birnin tarayya Abuja.

“Maniyyata kimanin 65,500 ne za su sauke Farali daga ƙasar nan a ƙasa mai tsarki; za su shafe aƙalla kwanaki huɗu domin yin ziyara a Madina kafin fara aikin Hajji, “in ji Arabi”.

Daga bisani shugaban hukumar aikin hajjin Jalal Ahmad Arabi, ya kuma bayyana cewa za ayi jigilar maniyyata aikin hajjin ne daga cibiyoyi 10 a faɗi ƙasar nan.

Continue Reading

Labarai

Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Laraba a matsayin ranar hutu

Published

on

Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Laraba, 1 ga watan Mayun 2024, a matsayin ranar hutu, domin bikin ranar ma’aikata na wannan shekara.

Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayyana hakan, a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Talata.

Olubunmi, ya kuma sake nanata buƙatar ganin ma’aikata sun jajirce da yin aiki yadda ya kamata a dukkanib matakai daban-daban.

Continue Reading

Labarai

Wahalar Fetur ta haifar mana da koma baya a sana’ar mu – Mai Motar Haya

Published

on

Wani mai sana’ar tuƙin motar Haya, da kuma lodin fasinjoji mai suna Kabiru Muhammad, mazaunin ƙaramar hukumar Munjibir, ya ce ƙarancin motocin Haya da ake samu a yanzu, yana da alaƙa da wahalar man Fetur da ake fuskanta a sassan Najeriya.

A zantawar mutumin da wakilinmu Yusuf Nadabo Isma’il, ta cikin shirin rahotanni daga ƴan Zazu na yau Talata, ya ce a baya har motoci hamsin suke yiwa lodin fasinjoji su tashi, amma a yanzu Mota ɗaya suke iya cikawa sakamakon ƙarancin Fetur da ake fama da shi.

Ya kuma ce ƙaranci tare da tsadar man fetur ɗin da ake fama da shi, sun haddasa musu koma baya a sana’ar su, baya ga batun kuma matsalar da suke fuskanta da fasinjoji wajen biyan kuɗin Mota.

Wakiliyarmu da ta bibiyi shirin na ƴan Zazu Ummi Bala Ahmad ta rawaito cewa, matuƙin motar Kabiru Muhammad, ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jahohi, da su yi abinda ya kamata dan ganin farashin man Fetur ɗin ya sauka, domin al’umma su samun sauƙi.

Continue Reading

Trending