Connect with us

Labarai

Ko ya halasta jami’an KAROTA su rika kwace makullin masu ababen hawa?

Published

on

Abinda ke ciwa masu ababen hawa tuwo a kwarya shine yadda jami’an Hukumar kan kwace makulli, ko kuma shiga abun hawan mutum da sunan za su mika shi ga ofishinsu.

Sai dai shin ko doka ta bai wa jami’an Hukumar shiga ababen hawa na mutanen da suka kama da wani laifin karya dokar zirga-zirga.

Audu Bulama Bukarti, kwararren lauya ne da ke nazarin digiri na uku a wata jami’a da ke birnin Landon, ya ce haramun ne jami’in KAROTA ya shiga abun hawan wanda aka samu da laifin karya dokar tuki.

“Doka ba ta ce jami’in KAROTA ya karbi makulli ko kuma shiga abun hawan mutum ba, abinda doka ta ce, shi ne ko dai ya sanya wanda ake zargin a gaba zuwa hukumar, ko kuma shi mai laifin ya bi bayan su, idan ma mai laifin ya yi musu gardama, to akwai motar da aka ware ta musamman domin daukar ababen hawan mutanen da suka karya doka.” In ji shi

Lauya Bukarti ya kuma ce, dokar Najeriya ta haramatawa wanda bashi da lasisi yin tuki, kuma ko da kujerar da direba yake hawa ne an haramtawa wanda bashi da damar hawa kai.

Ya ce, abin takaici ne abinda ‘yan KAROTA ke yi game da dokar masu ababen hawa, yayin da wasunsu ma ko kwakkwaran tuki ba sa iyawa, a gefe guda kuma ba a tabbatar da ingancin tukinsu a hukumace ba.

“Yan KAROTAn nan da suke kwace makullin direbobi, su fa ba kwararrun masu tuki bane, a wasu lokutan ma da dama daga cikinsu zaka iske su, ba su da lasisin tuki. Kuma a dokar Najeriya haramun ne mutum ya yi tuki ba tare da an bashi dama ba, kuma ko da motar a kashe take babu makulli a jikinta, haramun ne ka hau kujerar da direba ya ke zama.”

Barista Audu Bulama Bukarti ya ce, abun takaicin shine yadda wasu jami’an hukumar basu da lasisin tuki, amma sun karbi makullin masu ababen hawa, har ma suna tukawa, wanda hakan karara ya nuna cewa doka sama da guda daya suka karya a lokaci guda, yayinda suke zargin wasu da karya doka.

“Ko da makullin masu adai-daita sahu da suke karba, ai doka bata basu damar tuka babur din ba, tunda masu wannan sana’a sai sun karbi lasisi daga gwamnati kafin suyi amfani da ababen hawan su, kuma wannan ba sabon abu bane, jami’an hukumar nan sun jima suna yiwa doka karan-tsaye.” A cewar Barista Audu Bulama Bukarti

Labarai

Gwamnatin Kano za ta inganta filaye da bunƙasa duk ɓangarorin wasannin matasa – Kwamishinan Matasa da Wasanni

Published

on

Sabon kwamishinan ma’aikatar wasanni da ci gaban matasa na Jihar Kano Mustapha Rabi’u Musa kwankwaso, ya bada tabbacin cewar Gwamnatin Jihar za ta ɗauki matakin inganta filayen tare da bunƙasa duk wasu ɓangarorin wasanni da matasa ke yi.

Mustapha Rabi’u Musa Kwankwaso, ya bayyana hakan ne yayin da ya kama aiki yau Asabar, tare da kai ziyara a wasu filayen wasannin dake ihar Kano.

Daga cikin filayen wasannin da ya ziyarta akwai filin wasa na Sani Abacha da ke ƙofar Mata, da filin wasa na Kano Pillars da ke sabon Gari, da kuma filin wasa na Ado Bayero Square dake unguwar Sabon Gari, sai kuma filin wasa na Mahaha da ke ƙofar Na’isa.

Da yake jawabi bayan kammala ziyarar kwamishinan wasannin da ci gaban Matasa na jihar Kano, Mustapha Rabi’u Musa kwankwaso, ya ce ya gudanar da ziyarar ce domin sanin halin da filayen wasannin ke ciki.

A lokacin ziyarar kwamishinan na tare da mai bai wa Gwamnan Kano shawara a kan harkokin wasanni Ambasada Yusuf Imam Ogan Ɓoye, da shugaban magoya bayan ƙungiyar ƙwallon Ƙafa ta Kano Pillars Alhaji Rabi’u Abdullahi Kawo, da kuma mai riƙon Shugabancin hukumar wasanni ta jiha Malam Bala Sani Shehu.

Continue Reading

Labarai

Muna sane da ƙarancin Ruwa a wasu sassan Kano – Hukumar rarraba ruwan Sha

Published

on

Hukumar rarraba ruwan sha ta jihar Kano ta ce matsalar rashin samun ruwa da ake fuskanta a wasu sassan jihar Kano, yana da alaƙa ne da lalacewar wani abun kan Famfo a madatsar ruwan da ke Tamburawa.

Shugaban hukumar Injiniya Garba Ahmad Bichi, ne ya bayyana haka yayin zantawar sa da manema labarai, ya ce cikin guraren da za’a yiwa gyaran har da madatsar ruwa ta Challawa da Watari, da amincewar gwamnatin jihar Kano.

Injiniya Garba, ya kuma ce suna sane da ƙarancin ruwan da ake fuskan ta a wasu sassan jihar Kano, amma nan gaba kaɗan za kammala gyaran kan famfon, domin ganin an wadata sassan jihar Kano, da ruwan domin ganin sun samu wani sauƙi.

 “Mu ma a ɓangaren mu Bama jin daɗin yadda al’umma suke rasa ruwa a sassan jihar Kano, kuma nan da ranar Litinin mutane za su fita daga cikin wannan matsala ta rashin Ruwa, a yanku nan su, “in ji shi”

Garba Ahmad, ya kuma ƙara da cewa matsalar fashewar Fayif da aka samu a ci gaba da aikin gadar mahaɗar Ɗan Agundi, yanzu haka suna kan ɗaukar mataki tsakanin su da kamfanin da suka taka har ya fashe, dan ganin an gyara al’ummar da ake baiwa ruwa su ci gaba da damu.

Continue Reading

Labarai

Ƴan kasuwa ku tsaftace magudanan ruwa bisa gabatowar Damuna – Ƙungiyar Amata ta kasuwar Singa

Published

on

An buƙaci ƴan kasuwa da su rinƙa tsaftace tare da gyara magudanan ruwa a cikin kasuwannin su, bisa yadda damuna ke ƙara gabatowa.

Shugaban ƙungiyar Amata reshen kasuwar Singa Alhaji Musa Ibrahim Ɗan gaske, ne ya bukacin hakan a zantawar sa da manema labarai, yayin kaddamar da tsaftace kasuwar da kuma gyara mugudanun ruwan kasuwar.

Alhaji Musa, ya kuma ce ta hanyar tsaftace magudanan ruwan ne za a gujewa kowacce irin ambaliyar ruwa a cikin kasuwanni.

Continue Reading

Trending