Connect with us

Wasanni

Rummenigge: Xabi Alonso zai iya zama kocin Bayern Munich

Published

on

Shugaban kungiyar Bayern Muncih, Karl-Heinz Rummenigge, ya ce tsohon dan wasan kungiyar Xavi Alonso zai iya zama mai horas da kungiyar a nan gaba.

Alonso wanda ya taba lashe gasar cin kofin duniya da kasar sa ta Spain, sannan ya lashe gasar Bundesliga guda uku da DFB-Pokal da kuma DFL-Supercup a lokacin da ya shafe tsawon kakar wasanni uku a Bayern Munich tun daga shekarar 2014 har zuwa 2017 kafin ya jingine takalman sa daga harkokin tamaula.

Ya ce“Zai iya zama mai horas da Bayern Munich a nan gaba, domin kungiyar ta na da bukatar hakan a mafarki na, saboda mu har yanzu abokan juna ne da shi, saboda Alonso mu na bukatar sa a nan gaba, musamman ma a irin yanayin masu horaswa na matasa a wannan lokacin, amma a nan gaba mu ke magana, saboda mu na jin dadin Hansi Flick yadda ya ke nasa aikin a yanzu. Amma a yanzu mu na sa ran kocin mu zai ci gaba da zama tare damu sosai, saboda mun amince da shi”. Inji Rummenigge.

A yanzu haka Alonso shi ne mai horas da kungiyar Real Sociedad ajin matasa wadda take a kasar Andulusiya kuma a yanzu haka Rummenigge na tuntubar Alonso, domin ganin ya dawo da shi Bayern Munich a matsayin mai horas da kungiyar a nan gaba.

Wasanni

Bayer Leverkusen ta zama zakarar gasar Bundesliga ta 2023/2024.

Published

on

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Bayer Leverkusen ta zama zakarar gasar Bundesliga ta shekarar 2023/2024, bayan da suka samu nasara a kan Weder Bremen da ci 5-0.

Hakan ne kuma ya kawo ƙarshen shekaru 11 da Bayern Munich, da ta yi tana lashe gasar.

Wannan dai shi ne karo na farko da Bayer Leverkusen suka taɓa lashe gasar a tarihi, ida suka gaza ɗaukar kofin a shekarar 2002 a ranar ƙarshe ta gasar.

Har ila yau, a dai wannan shekarar ne su kayi rashin nasara hannun Shalke 04, a wasan ƙarshe na German Cup Da ci 4-2.

Haka kuma, Real Madrid suka doke su a wasan ƙarshe na zakarun nahiyar turai.

Rahotanni sun bayyana cewa ƙungiyar bata taɓa ɗaukar wata gasa ba a ƙarni na 21, sai bayan da Xavi Alonso ya karɓe su.

Continue Reading

Wasanni

Hukumar NPFL, ta amince da buƙatar Kano Pillars na ɗage wasan ta na mako na 28 da Enyimba

Published

on

Yanzu haka an samu dai-daito da hukumar NPFL, wanda ta amince da bukatar Kano Pillars na dage wasanta na mako na 28, da Enyimba zuwa ranar Alhamis, mai zuwa.

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars, ce ta wallafa hakan a shafin ta na Facebook da yammacin Litinin ɗin nan, ta ce ƴan wasan ta za su tashi a gobe Talata, da safe zuwa Aba domin fafata wasannin su.

Idan dai ba’a manta ba ƙungiyar ta wallafa kaɗan daga irin ƙalubalen da take fuskanta a harkokin gudanarwar ta.

Pillars, ta wallafa ƙalubalen ne kamar haka, “A yanzu haka zancan da muke muku Kano Pillars ta rasa kudin da za taje garin Aba, domin buga wasan hamayya na Nigeria Premier league wato Zobia Classic”.

Wasan dai shine wasa mafi ɗaukar hankali a league din Nigeria baki ɗaya, ku taya mu yadawa dan Allah.

Continue Reading

Wasanni

Glesner ya zama sabon mai horas da Palace.

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Crystal Palace ta sanar da nadin Oliver Glesner a matsayin sabon mai horaswar ta.

Glesner wanda tsohon mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Eintracht Frankfurt ne mai shekaru 49 dan asalin kasar Austrian, ya maye gurbin tsohon mai horaswa Roy Hodson, wanda ake ganin ya gaza kai kungiyar ga tudun mun tsira.

A wasanni 16 da Crystal Palace ta buga a bayan nan ta yi rashin nasara a wasanni 10 duk karkashin jagorancin Roy Hodson wanda hakan yasa take mataki na 16 a teburin gasar firimiyar kasar Ingila.

Glesner dai ya rattaba kwantaragi da Palace har na tsawon shekaru biyu, zai kuma jagoranci kungiyar a wasan sa na farko da kungiyar kwallon kafa ta Burnley a ranar Asabar mai kamawa.

Continue Reading

Trending