Connect with us

Labarai

Hada-hadar ‘yan wasa: Jovic na son tafiya Man-U, Dambele, Vinicius na neman sauya sheka

Published

on

Newcastle United za ta fafata da Valencia a yunkurin dauko dan wasan Juventus da Italiya mai shekara 26 Daniele Rugani, wanda ake rade radin zai tafi kulob din Fulham, West Ham ko kuma Sevilla.

Tottenham ta kusa kammala kulla yarjejeniyar karbo aron dan wasan Benfica da Brazil mai shekaru 25 Carlos Vinicius.

Wakilin dan wasan Real Madrid Luka Jovic, mai shekara 22, ya ce dan wasan na Serbia yana son tafiya Manchester United, duk da cewa Inter Milan da Roma suna zawarcinsa.

Liverpool na shirin amincewa da £23m daga wurin Sheffield United kan dan wasan Ingila mai shekara 20 Rhian Brewster.

Arsenal ta samu tagomashi a yunkurin dauko dan wasan Faransa mai shekara 22 Houssem Aouar daga Lyon, a yayin da kocin kungiyar Jean-Michel Aulas ya ce za su iya rasa ‘yan wasa biyu kafin wa’adin musayar ‘yan kwallo ya cika.

Manchester United ta fara tattaunawa da Barcelona kan karbo aron dan wasan Faransa Ousmane Dembele, mai shekaru 23.

Chelsea za ta iya sayar da dan wasan Spain Marcos Alsonso, da dan wasan Jamus Antonio Rudiger, da kuma dan wasan Ingila Ruben Loftus-Cheek, kafin a rufe kasuwar cinikayyar ‘yan wasa.

Arsenal na tattaunawa domin bayar da aron dan wasan Faransa mai shekara 21 Matteo Guendouzi ga Marseille.

Manchester United ta musanta rahotannin da ke cewa tana son dauko dan wasan Ingila Ainsley Maitland-Niles, mai shekaru 23, daga Arsenal.

 

Labarai

Ƴan kasuwa ku tsaftace magudanan ruwa bisa gabatowar Damuna – Ƙungiyar Amata ta kasuwar Singa

Published

on

An buƙaci ƴan kasuwa da su rinƙa tsaftace tare da gyara magudanan ruwa a cikin kasuwannin su, bisa yadda damuna ke ƙara gabatowa.

Shugaban ƙungiyar Amata reshen kasuwar Singa Alhaji Musa Ibrahim Ɗan gaske, ne ya bukacin hakan a zantawar sa da manema labarai, yayin kaddamar da tsaftace kasuwar da kuma gyara mugudanun ruwan kasuwar.

Alhaji Musa, ya kuma ce ta hanyar tsaftace magudanan ruwan ne za a gujewa kowacce irin ambaliyar ruwa a cikin kasuwanni.

Continue Reading

Hangen Dala

Yau za’a fara Shari’ar Ganduje da gwamnatin Kano

Published

on

A yau ne babbar kotun jaha mai lamba 4 zata fara sauraron wata sharia wadda gwamnatin kano ta ahigar.

 

Gwamnatin jahar kano dai ta shigar da karar tsohon gwamnan jahar kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da mai dakinsa Hafsat Umar Ganduje da kuma dansu Umar Abdullahi Ganduje da kuma wani kamfani mai suna Lamash da kuma Dr Jibrilla Muhammad.

 

Gwamnatin jahar kano dai tana zargin Ganduje da wadanna mutane da laifin hada baki da barnatar da dukiyoyin gwamnati.

 

 

Cikin zarge-zargen da ake yiwa su Ganduje akwai batun sun sayar da wasu filotai ba bisa ka’ida ba.

 

 

Da kuma batun zargin da akewa Ganduje na badakalar karbar dala tun a shekarar 2019.

 

 

Yanzu haka an girke jami,an tsaro a harabar sakateriyar Audu Bako inda kuma daga yanzu zuwa kowane lokaci kotun zata fara sauraron korafin kamar yadda wakilinmu Yusuf Nadabo Ismail ya rawaito

Continue Reading

Labarai

Ku tallafawa mazauna gidajen gyaran halin dan rage musu raɗaɗin rayuwa – Mallam Ibrahim Bunkure

Published

on

Limamin masallacin Salafussaleh dake unguwar Ɗorayi ƙarama a jihar Kano, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya shawarci al’umma da su ƙara dagewa wajen tallafawa mazauna gidajen ajiya da gyaran hali, da masu buƙata ta musamman, domin rage musu wani raɗaɗin rayuwa na yau da kullum.

Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya bayyana hakan ne yayin da suka tallafawa mazauna gidan gyaran hali na Goron Dutse, da kayayyakin Abinci, da kuma na gidan yara, a wani ɓangare na taya su bikin ƙaramar Sallah, wajen ganin sun samu farin ciki a bukukuwan ƙaramar sallar da aka gudanar.

Ya ce matuƙar masu hali za su rinƙa tallafawa mazauna gidan gyaran halin da abubuwan da suka sawwaƙa, babu makawa za’a rage musu wata damuwa ta yau da kullum.

Wakilinmu Yakubu Ibrahim Dogarai ya rawaito cewa, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya ce daga cikin kayan abincin da suka kai wa mazauna gidajen akwai Tuwon Sallah, da garin Kwakwaki, da kuma sinadarin Ɗanɗano, da Sukari, domin ragewa mazaunan gidajen wani raɗaɗin rayuwa.

Continue Reading

Trending