Connect with us

Labarai

GWAMNATIN TARAYYA TA KAMMALA SHIRI DOMIN RARRABA MUTANEN DA SUKA SAMI NASARAR CAN-CANTAR SHIGA AIKIN N-POWER ZAGAYE NA BIYU

Published

on

Gwamnatin tarayya ta kammala shiri tsaf domin rarraba mutanen da suka sami nasarar can-cantar shiga aikin N-Power zagaye na biyu har su dubu 300 a wuraren aiki daban-daban a farkon watan Afirilu mai kamawa.
Sanarwar ta fito daga bakin mataimaki na musaman kan harkokin labarai ga mataimakin shugaban kasa Laolu Akande, ya bayyana hakan a daren jiya Alhamis.
Ya ce a cikin mutane dubu dari biyun da suka ci gajiyar shirin na N-Power a kwannan cikin su harda dalibai dubu 500 da suka kammala jami’a.
Laolu Akande ya kuma ce tun da maiatmakin shugaban kasa Osibanjo ya kaddamar da shirin na N-Power ya nuna karara shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna cewa a shirye yake da ya yaki talauci da rashin yi a tsakanin matasa a gwamnatin sa.
Shirin na N-Power shiri ne da gwamnatin tarayya ta fito dashi domin baiwa matasa damar samun aikin yin a tsawon shekaru biyu a cikin gwamnatin tarayya domin suma a dama dasu, wanda a wannan Karin matasan da suka ci gajiyar shirin za su fara aikin 1 ga watan Afirilu na wannan shekarar su kuma kammala ranar 31 ga watan Yulin shekarar 2020 wanda a duk wata akan biya su naira dubu 30.

Labarai

Ba mu san Hamisu Breaker ya saki waƙar Amanata ba – Hukumar tace fina-finai

Published

on

Hukumar tace Fina-finai da Ɗab’i ta jihar Kano ta ce yanzu haka tana kan bincike don gano yadda akai mawakin nan Hamisu Breaker, ya saki sabuwar wakarsa mai suna “Amanata” ba tare da an tantance ta ba.

Mai magana da yawun hukumar Abdullahi Sani Sulaiman, shi ne ya bayyana hakan a wani sakon murya da ya aikowa Dala FM Kano, a ranar Alhamis 24 ga watan Afrilun 2025.

Ya kuma ce aikin dakatar da wakar ba na hukumar Hisbah ba ne na hukumar tace fina-finai ne, amma ba laifi ba ne kasancewar duk hukumomi ne na Gwamnati, a don haka idan hukumar ta Hisbah ta magantu akai babu laifi, domin dama suna aiki kafaɗa da kafaɗa.

A game da wakar ta Hamisu Beraker, mai suna “Amanata”, Abdullahi Sani, ya ce su har yanzu ba su san ta ina wakar ta fita ba tare da an tantance ta ba, amma tuni shugaban hukumar Abba Al-mustapha ya bada umarnin gudanar da bincike akan ta.

Ya ci gaba da cewa, fasahohi na zamani da suka fito yana ɗaya daga cikin ƙalubalen da hukumar take fuskanta, mutum sai ya rera waƙa yana daga Ɗaki ko kuma wata Ƙasa, ya sake ta ba tare da ya zo an duba masa ba, amma hakan ya zo ƙarshe.

Continue Reading

Hangen Dala

Rashin wuta: Muna cikin mawuyacin hali – al’ummar Kano, Katsina da Jigawa

Published

on

Al’ummar jihohin Kano, katsina da Jigawa na fuskantar yanayi mara dadi, Sakamakon karancin samun wutar lantarki daga hukumar KEDCO.

Al’ummar jihohin sun ce iya sa’o’i uku kacal suke samun wutar, wanda hakan ke haifar musu da nakasu a harkokin kasuwancin su.

Wani bincike da jaridar Daily Trust tayi ta ambato yadda masu kananan masana’antu irin su Walda, Cajin Waya, Kankara da masu sana’ar dinki da dai sauran kananan sana’o’i dake amfani da wutar lantarki sun shiga mawuyacin hali.

Kazalika rashin wutar ya shafi hatta bangaren ruwan sha, dama masu sana’ar sayar da Ruwa a irin yankunan Hotoro da sauran irin wuraren dake sayen ruwa, Inda yanzu haka ruwan yayi tashin gwauron zabi a kowace jarka.

Koda dai ana ta bangaren hukumar rarraba hasken wutar lantarkin me kula da shiyyar Kano, Katsina da Jigawa KEDCO sun nemi afuwar al’umma.

Idan za’a tuna dai a makon jiya ne Ministan Wutar lantarki yace ‘yan Nigeria Miliyan 150 na samun wadatacciyar wutar lantarki.

Sai dai kuma a jihohi irin su Kano, Katsina da Jigawa na bayyana damuwa kan karancin Wutar, Inda suka ce bata wuce ta sa’o’i uku suke samu a kowa ce rana.

Continue Reading

Hangen Dala

Rashin wuta:- Muna cikin mawuyacin hali – al’ummar Kano, Katsina da Jigawa

Trending