Connect with us

Wasanni

Gwarzon mai horaswa:  Ancelloti ya kafa tarihi a Everton

Published

on

Mai horas da Everton Carlo Ancelotti, ya lashe gwarzon mai horaswa na watan Satumba a gasar Firimiya bayan da ya jagoranci Everton ta hau kan teburin Firimiya.

Haka zalika dan wasan gaban kungiyar, Dominic Calvert-Lewin ya lashe kyautar gwarzon dan wasa na watan Satumba.

Nasarar ta biyo bayan da Everton ta samu nasara da ci 1-0 a hannun Tottenham tare da lallasa West Brom da ci 5-2 da kuma lallasa Crystal Palace da ci 2-1.

Calvert-Lewin yanzu haka shi ne a kan gaba wajen zura kwallaye 6 a gasar Firimiyar kasar Ingila.

Wannan ne karo na farko a tarihi tun shekarar 1894 har zuwa 1995 Everton ba ta samu irin wannan nasarar ba, sai a wannan lokacin karkashin mai horas da kungiyar Ancelotti.

Sai dai Ancelloti ya ce“Burin mu shi ne mu samu gurbi a gasar cin kofin zakarun kungiyoyin nahiyar tuari a shekarar badi”. Inji Ancelloti.

Nasarar da Everton ta samu a hannun Brighton and Hove Albion shi ne wasa na 100 a gasar Firimiya da Ancelotti ya samu. Kyautar kuma ita ce ta hudu da ya samu a gasar tun bayan da ya taba lashe kyautar gwarzon mai horaswa na wata-wata har sau 4 a Chelsea.

Masu horaswa biyar ne kadai a Firimiya su ka taba samun nasarar cin wasanni 60 a cikin wasanni 100 a gasar, tun bayan da Jose Mourinho ya samu nasarar wasanni 73 sai Pep Guardiola 73 da Manuel Pellegrini ya samu nasarar lashe wasanni 65 yayin da Alex Ferguson ya samu nasara sau 62 inda kuma Roberto Mancini ya samu 62.

 

 

Wasanni

Bayer Leverkusen ta zama zakarar gasar Bundesliga ta 2023/2024.

Published

on

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Bayer Leverkusen ta zama zakarar gasar Bundesliga ta shekarar 2023/2024, bayan da suka samu nasara a kan Weder Bremen da ci 5-0.

Hakan ne kuma ya kawo ƙarshen shekaru 11 da Bayern Munich, da ta yi tana lashe gasar.

Wannan dai shi ne karo na farko da Bayer Leverkusen suka taɓa lashe gasar a tarihi, ida suka gaza ɗaukar kofin a shekarar 2002 a ranar ƙarshe ta gasar.

Har ila yau, a dai wannan shekarar ne su kayi rashin nasara hannun Shalke 04, a wasan ƙarshe na German Cup Da ci 4-2.

Haka kuma, Real Madrid suka doke su a wasan ƙarshe na zakarun nahiyar turai.

Rahotanni sun bayyana cewa ƙungiyar bata taɓa ɗaukar wata gasa ba a ƙarni na 21, sai bayan da Xavi Alonso ya karɓe su.

Continue Reading

Wasanni

Hukumar NPFL, ta amince da buƙatar Kano Pillars na ɗage wasan ta na mako na 28 da Enyimba

Published

on

Yanzu haka an samu dai-daito da hukumar NPFL, wanda ta amince da bukatar Kano Pillars na dage wasanta na mako na 28, da Enyimba zuwa ranar Alhamis, mai zuwa.

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars, ce ta wallafa hakan a shafin ta na Facebook da yammacin Litinin ɗin nan, ta ce ƴan wasan ta za su tashi a gobe Talata, da safe zuwa Aba domin fafata wasannin su.

Idan dai ba’a manta ba ƙungiyar ta wallafa kaɗan daga irin ƙalubalen da take fuskanta a harkokin gudanarwar ta.

Pillars, ta wallafa ƙalubalen ne kamar haka, “A yanzu haka zancan da muke muku Kano Pillars ta rasa kudin da za taje garin Aba, domin buga wasan hamayya na Nigeria Premier league wato Zobia Classic”.

Wasan dai shine wasa mafi ɗaukar hankali a league din Nigeria baki ɗaya, ku taya mu yadawa dan Allah.

Continue Reading

Wasanni

Glesner ya zama sabon mai horas da Palace.

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Crystal Palace ta sanar da nadin Oliver Glesner a matsayin sabon mai horaswar ta.

Glesner wanda tsohon mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Eintracht Frankfurt ne mai shekaru 49 dan asalin kasar Austrian, ya maye gurbin tsohon mai horaswa Roy Hodson, wanda ake ganin ya gaza kai kungiyar ga tudun mun tsira.

A wasanni 16 da Crystal Palace ta buga a bayan nan ta yi rashin nasara a wasanni 10 duk karkashin jagorancin Roy Hodson wanda hakan yasa take mataki na 16 a teburin gasar firimiyar kasar Ingila.

Glesner dai ya rattaba kwantaragi da Palace har na tsawon shekaru biyu, zai kuma jagoranci kungiyar a wasan sa na farko da kungiyar kwallon kafa ta Burnley a ranar Asabar mai kamawa.

Continue Reading

Trending