Connect with us

Labarai

Mashawarci: Na dakatar da Salihu Tanko Yakasai – Ganduje

Published

on

Gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya dakatar da mai bashi shawara na musamman kan yaɗa labarai Salihu Tanko Yakasai daga muƙaminsa.

Kwamishinan yaɗa labaran Kano Malam Muhammad Garba ne ya sanar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar.

An dakatar da Salihu Yakasai ne saboda bayyana wasu kalaman suka game da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.

Kafin dakatarwar Salihu Yakasai ya shiga sahun wadanda suka soki gwamnatin tarayya musamman kan manufofinta a shafinsa na Twitter.

Salihu Tanko Yakasai ya ce gwamnatin Shugaba Buhari “ba ta tausayin ‘yan Najeriya”, cikin wani martani da ya mayar game da jan kafar da shugaban ya yi game da kiraye-kirayen da ‘yan Najeriya ke yi na rushe rundunar SARS ta ‘yan sanda sakamakon zargin cin zarafi da azabtarwa da ake zarginsu da yi.

Duk da cewa Buhari ya ce ya gana da Sufeto Janar na ‘yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu a daren Juma’a tare da bayar da umarnin daukar mataki, Salihu Tanko Yakasai, yana ganin ya kamata a ce shugaban ya yi wa ‘yan Najeriya jawabi da bakinsa.

Ko da yake bayan wasu sa’o’i, mataimakin na musamman ga Ganduje ya goge wasu daga cikin kalaman nasa.

Ko a ranar 18 ga watan Afrilun da ya gabata, gwamna Ganduje ya sauke kwamishinan ayyuka na jihar Injiniya Mu’azu Magaji Ɗan Sarauniya sakamakon wasu rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Hangen Dala

Rashin wuta: Muna cikin mawuyacin hali – al’ummar Kano, Katsina da Jigawa

Published

on

Al’ummar jihohin Kano, katsina da Jigawa na fuskantar yanayi mara dadi, Sakamakon karancin samun wutar lantarki daga hukumar KEDCO.

Al’ummar jihohin sun ce iya sa’o’i uku kacal suke samun wutar, wanda hakan ke haifar musu da nakasu a harkokin kasuwancin su.

Wani bincike da jaridar Daily Trust tayi ta ambato yadda masu kananan masana’antu irin su Walda, Cajin Waya, Kankara da masu sana’ar dinki da dai sauran kananan sana’o’i dake amfani da wutar lantarki sun shiga mawuyacin hali.

Kazalika rashin wutar ya shafi hatta bangaren ruwan sha, dama masu sana’ar sayar da Ruwa a irin yankunan Hotoro da sauran irin wuraren dake sayen ruwa, Inda yanzu haka ruwan yayi tashin gwauron zabi a kowace jarka.

Koda dai ana ta bangaren hukumar rarraba hasken wutar lantarkin me kula da shiyyar Kano, Katsina da Jigawa KEDCO sun nemi afuwar al’umma.

Idan za’a tuna dai a makon jiya ne Ministan Wutar lantarki yace ‘yan Nigeria Miliyan 150 na samun wadatacciyar wutar lantarki.

Sai dai kuma a jihohi irin su Kano, Katsina da Jigawa na bayyana damuwa kan karancin Wutar, Inda suka ce bata wuce ta sa’o’i uku suke samu a kowa ce rana.

Continue Reading

Hangen Dala

Rashin wuta:- Muna cikin mawuyacin hali – al’ummar Kano, Katsina da Jigawa

Ci gaba ba ya zuwa sai an samu haɗin kan al’umma – Dagacin Ja’en

Published

on

Dagacin garin Ja’en da ke ƙaramar hukumar Gwale a jihar Kano, Alhaji Isma’il Sa’ad Usman, ya ce hadin kai ne kaɗai zai kawo ci gaba ga kowa ce irin al’umma.

Dagacin ya bayyana hakan ne Jim kaɗan bayan wani taron masu Ruwa da tsaki na Garin Ja’en, wanda Hakimin Gundumar Ɗorayi Barde Kerarriya Alhaji Shehu Kabir Bayero ya shirya, aka gudanar a yankin Ja’en a ƙarshen makon da ya gabata.

“Dukkanin wani ci gaba ba ya zuwa har sai an samu haɗin kan kowa ne bangare na al’umma, “in ji Dagacin”.

Wakilin Dala FM Kano, Ahmad Rabi’u Ja’en ya ruwaito cewa, taron ya samu halartar dukkanin bangarori, na unguwannin Ja’en, da suka haɗar da kungiyar mafarauta da maharba dabma kungiyar malaman makaranta.

Continue Reading

Trending