Connect with us

Labarai

SWAT: Mu na goyan bayan zan-zangar da matasa su ka yi – Ganduje

Published

on

Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya yabawa matasan Kano akan gudunmawar da suke bayar wa ga jamian tsaro da gwamnati domin tabbatar da zaman lafiya a jihar.

Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana hakan ne a yau Laraba lokacin da tawagar matasa a nan Kano ke gudanar da zanga-zanga a kan goyon bayan sabon tsarin SWAT a kofar gidan gwamnatin Kano.

Ya ce, “Duba da yadda ake gudanar da zanga-zanga a wurare da dama bisa ga rashin amincewar aikin na SARS, matasan Kano basu bi wannan tsari ba sai su ka zo da kuduri na sun yadda da SWAT”.

Ya kara da cewa, “Jihar Kano na goyon bayan matasan tare da godewa shugaba Buhari bisa ga gyara tsarin domin tsare dukiyar al’umma da lafiyar su”. A cewar Dr. Abdullahi Umar Ganduje.

Wakiliyar mu Zahra’u Nasir ta rawaito cewa, jim kadan bayan kammalawa gwamna Ganduje ya karbi bakuncin hukumar NIPOST a fadar gwamnatin ta Kano.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Labarai

Harin ‘yan bindiga ya yi sanadiyar mutuwar mutane 20 a Zamfara

Published

on

Yan bindiga sun hallaka mutane 20 a wani har da suka kai garin Tungar Kwana da ke karamar hukumar Mafara a jihar ta Zamfara, bayan sun saci wasu dabbobin da jami’an tsaro suka kwato.

Kakakin ‘yan sandan jihar SP Shehu Muhammad ya bayyana hakan a zantawar sa da  wakilin mu Yusuf Ibrahim Jargaba.

Ya ce, “Tuni suka baza jami’an tsaro domin gano wadanda su ka yi kisan su fuskanci hukunci”. A cewar SP Shehu Muhammad

 

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Tarbiyya na taka muhimmiyar rawa wajen samun zaman lafiya – Liman

Published

on

Babban limamin masallacin juma’a na Umar Bin Khaddab da ke Dangi, Dr Yahaya Tanko ya ce, addinin musulunci addini ne na zaman lafiya, saboda haka al’umma su kiyayi tayar da husuma.

Dr Yahaya Tanko ya bayyana hakan ne a zantawar sa da wakilin mu Tijjani Adamu.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Matashin da ake zargi da kashe matar sa ya sake gurfana a kotu

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta ci gurfanar da mutumin nan da ake zargin ya kashe matar sa, a gaban babbar kotun jihar Kano mai lamba 7, karkashin mai shari’a Usman Na Abba.

Tun a ranar 2 ga watan Afirilu na shekarar da ta gaba aka yi zargin Aminu Inuwa ya yi amfani da wuka ya kashe matar sa mai suna Safara’u Muhammadu, kuma binne ta a cikin gidan sa, a unguwar Gwazaye Dorayi Karama da ke karamar hukumar Gwale.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!