Connect with us

Labarai

Saura kiris a kawar da cutar Korona a Kano

Published

on

Hukumar dakile cutuka masu yaduwa ta Najeriya NCDC ta ce adadin mutanen da cutar Covid-19 a fadin kasar sun tasamma 60,834 bayan da aka gano karin adadin mutum 179 da suka kamu da cutar ranar Laraba.

A rahoton da NCDC, ta sanya a shafinta na Twittare ta ce ba a samu ko da mutum guda da ya mutu sakamakon cutar ba a ranar Larabar, kuma adadin mutanen da cutar ta yi ajalinsu tun daga bullarta zuwa yanzu ya tasamma 1,116.

Kazalika an samu karin wadanda suka warke daga cutar, abin da ya sa jumullar wadanda aka sallama daga asibiti ya kai 52,143.

Jihar Legas ce ke kan gaba a yawan wadanda suka kamu da cutar, inda aka samu mutum 116, sai kuma Anambra mai mutum 20.

A jihar Kano kuwa ba a samu ko da mutum guda da ya kamu daga cutar ba, daga cikin mutum tamanin da uku da aka dauki samfurinsu. Sai dai an salami mutum biyar da aka tabbatar sun samu ‘yanci daga cutar.

Labarai

Harin ‘yan bindiga ya yi sanadiyar mutuwar mutane 20 a Zamfara

Published

on

Yan bindiga sun hallaka mutane 20 a wani har da suka kai garin Tungar Kwana da ke karamar hukumar Mafara a jihar ta Zamfara, bayan sun saci wasu dabbobin da jami’an tsaro suka kwato.

Kakakin ‘yan sandan jihar SP Shehu Muhammad ya bayyana hakan a zantawar sa da  wakilin mu Yusuf Ibrahim Jargaba.

Ya ce, “Tuni suka baza jami’an tsaro domin gano wadanda su ka yi kisan su fuskanci hukunci”. A cewar SP Shehu Muhammad

 

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Tarbiyya na taka muhimmiyar rawa wajen samun zaman lafiya – Liman

Published

on

Babban limamin masallacin juma’a na Umar Bin Khaddab da ke Dangi, Dr Yahaya Tanko ya ce, addinin musulunci addini ne na zaman lafiya, saboda haka al’umma su kiyayi tayar da husuma.

Dr Yahaya Tanko ya bayyana hakan ne a zantawar sa da wakilin mu Tijjani Adamu.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Matashin da ake zargi da kashe matar sa ya sake gurfana a kotu

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta ci gurfanar da mutumin nan da ake zargin ya kashe matar sa, a gaban babbar kotun jihar Kano mai lamba 7, karkashin mai shari’a Usman Na Abba.

Tun a ranar 2 ga watan Afirilu na shekarar da ta gaba aka yi zargin Aminu Inuwa ya yi amfani da wuka ya kashe matar sa mai suna Safara’u Muhammadu, kuma binne ta a cikin gidan sa, a unguwar Gwazaye Dorayi Karama da ke karamar hukumar Gwale.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!