Connect with us

Labarai

Farashin Burodi ya yi tashin gwauron zabi a kasar Sudan

Published

on

Hauhawar farashin kaya a Sudan ya wuce mizani yayin da farashin burodi da sauran kayan masarufi ke ci gaba da hauhawa.

Alkaluma Hukumar kididdiga ta kasar ya nuna cewa hauhawar farashin shekara-shekara da aka fitar ya tashi zuwa kaso 212.29 bisa dari daga kashi 166.83.

Hakan ya kasance mafi girma a tarihin kasar, sakamakon hauhawar farashin burodi da na kayan lambu gami da karin farashin sufuri.

Hauhawar farashi na cigaba a kasar ta Sudan tun kafin hambarar da gwamnatin tsohon shugaba Omar al-Bashir, a watan Afrilun shekara ta 2019 wanda ya dade ya na mulki.

Kasar dai ta fuskanci takunkumin tattalin arziki daga Amurka shekaru da dama karkashin al-Bashir wanda ya mulki kasar tun bayan juyin mulkin soja na 1989.

Gwamnatin rikon kwarya na kokarin farfado da tattalin arziki a cikin gibin kasafin kudi yayinda ake fama da karancin kayayyakin masarufi, da suka hada da man fetur, burodi da magunguna.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Labarai

Harin ‘yan bindiga ya yi sanadiyar mutuwar mutane 20 a Zamfara

Published

on

Yan bindiga sun hallaka mutane 20 a wani har da suka kai garin Tungar Kwana da ke karamar hukumar Mafara a jihar ta Zamfara, bayan sun saci wasu dabbobin da jami’an tsaro suka kwato.

Kakakin ‘yan sandan jihar SP Shehu Muhammad ya bayyana hakan a zantawar sa da  wakilin mu Yusuf Ibrahim Jargaba.

Ya ce, “Tuni suka baza jami’an tsaro domin gano wadanda su ka yi kisan su fuskanci hukunci”. A cewar SP Shehu Muhammad

 

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Tarbiyya na taka muhimmiyar rawa wajen samun zaman lafiya – Liman

Published

on

Babban limamin masallacin juma’a na Umar Bin Khaddab da ke Dangi, Dr Yahaya Tanko ya ce, addinin musulunci addini ne na zaman lafiya, saboda haka al’umma su kiyayi tayar da husuma.

Dr Yahaya Tanko ya bayyana hakan ne a zantawar sa da wakilin mu Tijjani Adamu.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Matashin da ake zargi da kashe matar sa ya sake gurfana a kotu

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta ci gurfanar da mutumin nan da ake zargin ya kashe matar sa, a gaban babbar kotun jihar Kano mai lamba 7, karkashin mai shari’a Usman Na Abba.

Tun a ranar 2 ga watan Afirilu na shekarar da ta gaba aka yi zargin Aminu Inuwa ya yi amfani da wuka ya kashe matar sa mai suna Safara’u Muhammadu, kuma binne ta a cikin gidan sa, a unguwar Gwazaye Dorayi Karama da ke karamar hukumar Gwale.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!