Connect with us

Wasanni

Jan kati: Maguire ne na 3 da a ka taba kora a filin wasan Wembley

Published

on

Dan wasan bayan kasar Ingila kuma dan wasan Manchester United, Harry Maguire ya kasance dan wasa na uku da a ka fara kora a filin wasa na Wembley dake kasar Ingila.

Dan wasan ya karbi jan kati a minti 31 a lokacin da kasar sa ta Ingila ta ke wasa da Denmark a ranar Laraba da ci 1-0.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Wasanni

Dumama kujera: Na yi takaici da ba ni a cikin jerin ‘yan wasa – Ozil

Published

on

Dan wasan tsakiyar Arsenal Mesut Ozil ya bayyana bakincikin sa karara a fili sakamakon tsige sunan sa da a ka yi a cikin jerin ‘yan wasa 25 a gasar Firimiya.

Ozil mai shekaru 32 ya koma Arsenal a shekarar 2013 daga Real Madrid a kan kudi Fam miliyan 42.4, amma kawo yanzu bai bugawa Arsenal was aba tun ranar 7 ga watan Maris.

Ya ce”Na yi matukar takaici sosai da ba a yi rijista da sunana ba a cikin ‘yan wasan Arsenal da suke fafatawa a Firimiya”. Inji Ozil.

Haka zalika Ozil ba zai buga gasar cin kofin Europa ba, sakamakon ba bu sunan sa a cikin jeirn ‘yan wasan Arsenal, sai dai kawai zai iya bugawa kungiyar Arsenal ‘yan ‘asa da shekaru 23 kafin wa’adin kwantiragin sa ya kare a shekarar 2021.

Continue Reading

Wasanni

Kudin shiga: Manchester United ta yi asarar kudi

Published

on

Manchester United ta yi asarar Fam miliyan 70 na kudin shigar kungiyar na tun daga ranar 30 na watan Yunin shekarar 2020.

Manchetser United ta yi rashin kudin shigar ne sakamakon cutar Corona tun lokacin da a ka dakatar da wasa a watannin baya.

Kudin shigar Manchester United ya yi kasa da kaso 18.8 daga Fam miliyan 627.1 har zuwa Fam miliyan 509, sakamakon rashin fitowa gasar cin kofin zakarun kungiyoyin nahiyar turai da ba ta yi ba a bara.

Continue Reading

Wasanni

Mai taron raga: Tsohon dan wasan Faransa ya mutu

Published

on

Tsohon mai tsaron ragar kasar Faransa Bruno Martini yam utu sakamakon cutar bugun zuciya da ya riske shi.

Bruno Martini mai shekaru 58 wanda shi ne tsohon mai horas da masu tsaron ragar kasar Faransa.

Martini ya bugawa kasar Faransa wasanni 31 wanda ya fara buga wasa a gasar cin kofin Yuro na shekarar 1992 da kasar Faransa ta buga da kasar Ingila.

Ya horas da masu tsaron ragar kasar Faransa a shekarar 1999 har zuwa 2010.

Sannan ya buga wasanni 139 a tsohuwar kungiyar sa ta Auxerre yayin da ya buga wasanni 113 a kungiyar Montpellier.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!