Connect with us

Labarai

Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda

Published

on

Shahararren mawakin masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood Hamisu Breaker ya mika kan sa ga jami’an ‘yan sanda da yammacin ranar Alhamis biyo bayan karawa wani mutum mai suna Sani Kamal Muhammed, mota a mahadar titi dake Dan Agundi a yammacin jiya Laraba.

Sai dai tun a jiyan aka yi zargin Hamisu Breaker, ya arce wanda kuma a yanzu haka ya kawo kan sa sashin na MTD domin bayar da bayanin yadda lamarin ya faru.

Domin jin cikakken rahotan saurari wannan.

Labarai

Ma’aurata su guji daukar dabi’u a kafofin sada zumunta – Malam Kabiru

Published

on

Shugaban makarantar Markazul Tabligul Risalatul Islam Malam Kabiru Ghali Ibrahim ya ce, Yanayin rayuwar wasu ma’auratan ke janyo matsaloli a zaman takewar aure.

Malam kabiru Gali Ibrahim ya bayyana hakan ne a ganawar sa da gidan rediyon Dala a ranar Alhamis

Yana mai cewa, “Lokuta da dama wasu ma’auratan su na daukar wasu dabi’u ne a kafofin sada zumunta ba tare da tantance sahihancin abin ba kuma suce za su gwada a gidajen su”.

Ya kuma ce, “Rashin sanya tsoron Allah a wajen neman aure na taka muhimmiyar rawa wajen samar da matsaloli bayan aure”. Inji Malam Kabiru.

Wakilin mu Nasir Khalid Abubakar ya rawaito cewar, Malam Kabiru Ghali Ibrahim ya kuma ja hankalin ma’aurata dama waɗanda ke da niyyar auren kan su sa tsoron Allah a dukkan al’amuran su dan samun da cewa a duniya da kuma lahira

 

Continue Reading

Labarai

Gwamnati ta rinka sayawa matasa Baburan Adaidaita – Human Right

Published

on

Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Human Rights Community Service Iniative ya shawarci gwamnatin Kano da ta rinka siyan baburan Adaidaita sahu tana bada su ga matukan su a kudi mai sauki domin samun sauki ga al’ummar jihar.

Shugaban kungiyar, Kwamared Balarabe Shehu Leko ne ya bayyana hakan ta cikin shirin Jamhuriyya na nan gidan radiyon Dala dake zuwa a kullum da karfe 8 na dare.

Ya kuma ce, “Akwai bukatar gwamanatin ta yi kokari wajan samar da tsayayyen farashi ga masu sayar da baburan sahun da kuma masu siye su bayar haya a matsayin Hire Purchase”. A cewar Kwamared Leko.

Continue Reading

Labarai

‘Yan Jarida ku rinka watsi da labaran bogi – Kabiru Alhasan Rirum

Published

on

Dan majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Rano, Kibiya da Bunkure Kabiru Alhasan Rirum ya shawarci ‘yan jaridu a jihar Kano da na kasa baki daya da su kara jajircewa wajen watsi da labaran bogi.

Dan majalisar ya bayyana hakan ne yayin wata ziyayar taya murna da ya kaiwa sabbin shugabanni kungiyar ‘yan jaridu ta kasa reshen jihar Kano a ranar Laraba.

Tsohon shugaban majalisar dokoki ta jihar Kano Kabiru Alhasan wanda ya sami wakilcin mataimakinsa na musamman a kan kafafen yada labarai Fatihu Yusuf Bichi ya jaddada muhimmancin ‘yan jaridun wajan sanar da al’umma labarai na gaskiya.

Ya ce ‘yan jaridu suna da rawar da zasu taka wajan raba al’umma da labarai na karya da suke futowa daga shafukan sada zumunta da sauran hanyoyi na bogi.

 

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!