Connect with us

Wasanni

Dan wasan baya: Tottenham ta dauki Joe Rondon Rodon

Published

on

Tottenham Hotspur ta dauki dan wasan bayan Swansea City, Joe Rondon a kan kudi Fam miliyan 11.

Dan wasan mai shekaru 22, ya buga wasanni 54 a gasar Championship tun daga kakar shekarar 2018-19.

Dan wasan ya kuma bugawa kasar sa ta Wales wasanni 3 wanda a yanzu haka wasannin sa baki daya su ka zama 7.

Rodon shi ne dan wasa na bakwai da Tottenham ta dauka a bana. Sannan kuma yam aye gurbin dan wasan bayan Jan Vertonghen wanda ya koma Benfica da kuma Juan Foyth wanda ya tafi Villarreal a matsayin aro.

An dai baiwa kungiyoyin gasar Firimiya damar daukan dan wasa a kungiyoyin gasar Championship a yau juma’a.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Wasanni

Dumama kujera: Na yi takaici da ba ni a cikin jerin ‘yan wasa – Ozil

Published

on

Dan wasan tsakiyar Arsenal Mesut Ozil ya bayyana bakincikin sa karara a fili sakamakon tsige sunan sa da a ka yi a cikin jerin ‘yan wasa 25 a gasar Firimiya.

Ozil mai shekaru 32 ya koma Arsenal a shekarar 2013 daga Real Madrid a kan kudi Fam miliyan 42.4, amma kawo yanzu bai bugawa Arsenal was aba tun ranar 7 ga watan Maris.

Ya ce”Na yi matukar takaici sosai da ba a yi rijista da sunana ba a cikin ‘yan wasan Arsenal da suke fafatawa a Firimiya”. Inji Ozil.

Haka zalika Ozil ba zai buga gasar cin kofin Europa ba, sakamakon ba bu sunan sa a cikin jeirn ‘yan wasan Arsenal, sai dai kawai zai iya bugawa kungiyar Arsenal ‘yan ‘asa da shekaru 23 kafin wa’adin kwantiragin sa ya kare a shekarar 2021.

Continue Reading

Wasanni

Kudin shiga: Manchester United ta yi asarar kudi

Published

on

Manchester United ta yi asarar Fam miliyan 70 na kudin shigar kungiyar na tun daga ranar 30 na watan Yunin shekarar 2020.

Manchetser United ta yi rashin kudin shigar ne sakamakon cutar Corona tun lokacin da a ka dakatar da wasa a watannin baya.

Kudin shigar Manchester United ya yi kasa da kaso 18.8 daga Fam miliyan 627.1 har zuwa Fam miliyan 509, sakamakon rashin fitowa gasar cin kofin zakarun kungiyoyin nahiyar turai da ba ta yi ba a bara.

Continue Reading

Wasanni

Mai taron raga: Tsohon dan wasan Faransa ya mutu

Published

on

Tsohon mai tsaron ragar kasar Faransa Bruno Martini yam utu sakamakon cutar bugun zuciya da ya riske shi.

Bruno Martini mai shekaru 58 wanda shi ne tsohon mai horas da masu tsaron ragar kasar Faransa.

Martini ya bugawa kasar Faransa wasanni 31 wanda ya fara buga wasa a gasar cin kofin Yuro na shekarar 1992 da kasar Faransa ta buga da kasar Ingila.

Ya horas da masu tsaron ragar kasar Faransa a shekarar 1999 har zuwa 2010.

Sannan ya buga wasanni 139 a tsohuwar kungiyar sa ta Auxerre yayin da ya buga wasanni 113 a kungiyar Montpellier.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!