Connect with us

Labarai

Jami’an tsaro sun gayyaci matasan da su ka shirya zanga-zanga a Kano

Published

on

Jami’an tsaro sun gayyaci wasu matasan huɗu daga cikin jagororin da suka shirya zanga-zanga a Kano.

Jagoran masu zanga-zanga a jihar Kano Sharu Ashir Nastura ya ce, haɗin gwiwar jami’an tsaro sun gayyace su tun ƙarfe goma na dare kuma ba a sallame su ba har sai bayan ƙarfe uku na dare.

Ya ce, “Mun shirya zanga-zangar ne domin neman lallai gwamnatin tarayya ta kawo ƙarshen matsalar tsaro da ake fama da ita a yankin arewacin ƙasar nan”.

Ya kuma ce, “Muna buƙatar wannan sabon sashen na ƴan sanda (SWAT) a kawo su yankunan mu da ake fama da matsalolin tsaro domin su yaƙi ƴan ta’adda”. Sharu Ashir Nastura

Wata majiya rundunar tsaron farin kaya ta DSS reshen Kano ta ce sun gayyaci masu shirya zanga-zangar ne domin tsara musu yadda zasu gudanar da zanga-zangar bisa tsarin doka.

Koda muka tuntuɓi rundunar ƴan sandan Kano, mai magana da yawunta DSP. Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce bai samu labarin ba, amma zai bincika.

Labarai

Ku tallafawa mazauna gidajen gyaran halin dan rage musu raɗaɗin rayuwa – Mallam Ibrahim Bunkure

Published

on

Limamin masallacin Salafussaleh dake unguwar Ɗorayi ƙarama a jihar Kano, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya shawarci al’umma da su ƙara dagewa wajen tallafawa mazauna gidajen ajiya da gyaran hali, da masu buƙata ta musamman, domin rage musu wani raɗaɗin rayuwa na yau da kullum.

Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya bayyana hakan ne yayin da suka tallafawa mazauna gidan gyaran hali na Goron Dutse, da kayayyakin Abinci, da kuma na gidan yara, a wani ɓangare na taya su bikin ƙaramar Sallah, wajen ganin sun samu farin ciki a bukukuwan ƙaramar sallar da aka gudanar.

Ya ce matuƙar masu hali za su rinƙa tallafawa mazauna gidan gyaran halin da abubuwan da suka sawwaƙa, babu makawa za’a rage musu wata damuwa ta yau da kullum.

Wakilinmu Yakubu Ibrahim Dogarai ya rawaito cewa, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya ce daga cikin kayan abincin da suka kai wa mazauna gidajen akwai Tuwon Sallah, da garin Kwakwaki, da kuma sinadarin Ɗanɗano, da Sukari, domin ragewa mazaunan gidajen wani raɗaɗin rayuwa.

Continue Reading

Labarai

Iyaye ku dai ma marawa ƴaƴan ku baya akan abinda suke yi da ya saɓawa doka – Mai unguwar Ja’en Jigawa

Published

on

Mai unguwar Ja’en Jigawa da ke ƙaramar hukumar Gwale a jihar Kano Sani Muhammad, ya ce bai kamata a rinƙa samun wasu iyaye da ɗabi’ar nan ta marawa ƴaƴan su baya akan abinda yaran suke aikatawa na saɓawa Doka, domin gujewa abinda ka je ya dawo.

Mai unguwar ya bayyana hakan ne yayin zantwarsa da gidan rediyon Dala FM, a lokacin da yake tsokaci kan yadda ake samun wasu daga cikin iyayen yankin sa na marawa ƴaƴan su baya kan abinda suke yi na ba dai dai ba, lamarin da yake ƙara ƙara kangarar da tarbiyyar ƴaƴan tare da tayar da hankalin al’umma.

Mai unguwa Sani Muhammad, ya kuma ce matuƙar yaran ba za su zauna lafiya a cikin unguwa da al’umma ba, to kuwa za su rinƙa ɗaukar matakin miƙa yaran hannun jami’an tsaro mafi kusa, domin ɗaukar matakin da ya dace a kan su, wajen ganin sun sauke nauyin da aka ɗora musu.

Sani Muhammad, ya ƙara da cewa ko a baya bayan nan wasu matasa sai da suka yi yunƙurin yin abinda bai kamata ba, lamarin da yasa aka ɗauki mataki a kansu amma aka samu wasu daga cikin iyaye suka marawa yaran nasu baya, wanda hakan kan haifar da barazanar tsaro.

Continue Reading

Labarai

Matasa ku ƙara dagewa da neman Ilmin addini da na zamani – Dr. Abdallah Gadan Kaya

Published

on

Fitaccen malamin addinin Musluncin nan Dakta Abdallah Usman Umar, ya shawarci matasa da su ƙara mayar da hankali wajen neman ilmin addinin da na zamani, domin zama ababen koyi a tsakanin al’umma.

Dakta Abdallah Gadan Ƙaya, ya bayyana hakan ne ta cikin Tafsirin Al-ƙur’ani mai girma, da yake gabatarwa cikin wannan watan azumin Ramadana a jihar Gombe.

A cewar sa, “Akwai buƙatar matasa ku yi riƙo da ƙananan sana’o’in dogaro da kai, da za ku rinƙa biyawa kan ku kuɗin makaranta wajen neman ilimi domin kaucewa zama a cikin jahilci, “in ji shi”.

Dakta Abdallah, ya kuma yi kira ga shugabanni da su dukkan abinda ya dace wajen inganta makarantu a sassan ƙasar nan, domin ganin ɗalibai sun samu ingantaccen Ilmi.

Continue Reading

Trending