Connect with us

Labarai

Dokar hana shigo da abinci daga waje ta taimakawa manoma – Ganduje

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta kaddamar da babban kwamitin da zai rika kula da harkar burtali a Nan Kano.

Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje ya kaddamar da kwamitin ne yau Asabar a ofishin hukumar bunkasa aikin noma da raya karkara na jihar Kano wanda manajan daraktan hukumar Ibrahim Sulaiman Dan’isle zai shugaban ta.

Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje ya Kuma kaddamar da rabon motoci da babura Wanda ya ce gwamnati da masu taimaka mata sun samar da su ne ga  manoma domin rika amfani da su wajen saukaka zirga-zirga.

A yayin taron gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje ya kuma ce, dokar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi ta hana shigo da abinci daga waje ta taimakawa manoma wajen yin noma a kasar nan tare cin riba.

A nasa bangaren manajan daraktan hukumar bunkasa noma da Raya karkara na Kano Ibrahim Sulaiman Dan’isle ya godewa gwamnatin Kano bisa ga samar da motoci da baburan zirga zirga ga manoma.

Wakiliyar mu Zahrau Nasir ta rawaito cewa, kwamitin harkar Burtalin Yana da wakilici daga wasu maaikatu a nan Kano tare da kuma Masaurautun Kano biyar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Labarai

Harin ‘yan bindiga ya yi sanadiyar mutuwar mutane 20 a Zamfara

Published

on

Yan bindiga sun hallaka mutane 20 a wani har da suka kai garin Tungar Kwana da ke karamar hukumar Mafara a jihar ta Zamfara, bayan sun saci wasu dabbobin da jami’an tsaro suka kwato.

Kakakin ‘yan sandan jihar SP Shehu Muhammad ya bayyana hakan a zantawar sa da  wakilin mu Yusuf Ibrahim Jargaba.

Ya ce, “Tuni suka baza jami’an tsaro domin gano wadanda su ka yi kisan su fuskanci hukunci”. A cewar SP Shehu Muhammad

 

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Tarbiyya na taka muhimmiyar rawa wajen samun zaman lafiya – Liman

Published

on

Babban limamin masallacin juma’a na Umar Bin Khaddab da ke Dangi, Dr Yahaya Tanko ya ce, addinin musulunci addini ne na zaman lafiya, saboda haka al’umma su kiyayi tayar da husuma.

Dr Yahaya Tanko ya bayyana hakan ne a zantawar sa da wakilin mu Tijjani Adamu.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Matashin da ake zargi da kashe matar sa ya sake gurfana a kotu

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta ci gurfanar da mutumin nan da ake zargin ya kashe matar sa, a gaban babbar kotun jihar Kano mai lamba 7, karkashin mai shari’a Usman Na Abba.

Tun a ranar 2 ga watan Afirilu na shekarar da ta gaba aka yi zargin Aminu Inuwa ya yi amfani da wuka ya kashe matar sa mai suna Safara’u Muhammadu, kuma binne ta a cikin gidan sa, a unguwar Gwazaye Dorayi Karama da ke karamar hukumar Gwale.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!